Sha tara

518 12 0
                                    


Cikin mintuna kaɗan Muhammad ya iso gidanshi, a waje yayi parking ya samu Salima a tsakar gida tana hawaye ga Hafiz J shima yana kuka duk sun birkice.

"Me ya sameki ke kuma kike kuka?" Ya tambayeta yana karɓan yaron daga hannunta ya ɗaurashi a kafaɗa yana lallashinshi.

"Babu komai." Ta bashi amsan tana share hawayen fuskar tata.

"Haka kawai zaki fara kuka babu abun da ya sameki?" Ya tsareta da ido yana ɓata rai don baya son yawo da hankali.

"Dama kar ka zo kace ni na sakasu ne ka mini faɗa, wallahi bani na sakasu ba. Kuma da Maman Hanan ɗin ma tace zata yi magana sai da na roƙeta tace ta fasa amma kuma sai da tayi. Kayi haƙuri." Ta ƙarisa maganan tana kecewa da wani kukan.

"Ni nace zan miki faɗa Salima? Kuma na san halinki ba zaki nuna musu su aikata hakan ba. Yanzu dai ki share hawayenki, hingo karɓi yaron ki je ki kwantar dashi zai yi bacci." Da haka ya miƙa mata HJ wanda har ya fara gyangyaɗi domin ya gaji da kukan da bashi da dalili.

Da haka Muhammad ya shiga falon Juwairiyya ya isa bakin ƙofar ɗakin nata ya fara bugawa yana kiran sunanta.

"Juwairiyya ki buɗe ƙofar." Ya cigaba da murɗa handle ɗin yana jijjigawa.

Caraf ya ji ta cire lock ɗin ya buɗe ya shiga yana binta da kallo har ta je ta kwanta a kan gado tana mai kare fuskarta da hannayenta duka.

"Wa ya dafa indomie a gidan nan?" Shine abun da ya fara tambaya yana tsaye a kanta.

Wani irin zabura tayi ta miƙe zaune tana kallonshi fuskarta ɗauke da tsantsan mamaki ta ce,

"An faɗa maka an shigo har cikin gidana an mini rashin mutunci shine ba zaka tambayi wani hali nake ciki ba sai waye ya dafa indomie? Ni ce na dafa da kwai don ba zan iya cin ɗumame ba."

"Akan bakya cin ɗumamen ne a gidanku?"

"Zagina zaka yi kenan? Kana so kace mu talakawa ne?"

"Tambaya na miki ki bani amsa."

"Don Allah ka barni, idan abun da ya kawoka kenan ka tafi ka barni in ji da abun da yake damuna."

"Wato da na hanaki fitan kin fita?"

Galala take kallonshi cike da mamaki, ta ɗauka zai zo ne ya ji ba'asin me ya faru sannan ya samu mazajen shegun matan nan a musu faɗa ko a musu iyaka da gidan amma shine zai zo yana maganar wani indomie?

"Na fita kuma na sayo carton ɗin indomie da crate ɗin kwai da kayan haɗa tea saboda ina so kai kuma baka saya mini ba." Ta faɗa a harzuƙe don haushinshi take ji sosai kamar ta je ta wanka mishi mari.

"Saboda kina da gajen haƙuri ne, da kinyi haƙuri da kin jira kin ga gudun ruwana. Na farko na hana cin indomie a gidan nan saboda illolin da ke cikinta. Na biyu fitan da kika yi ba da yawun bakina ba na barki da wanda ya bani amanarki har sai kin nemi gafara a gurina. Na uku kuma na haramtawa kowacce matata zuwa shago, in kina da aika ki bawa almajiri in babu ki jira in dawo in sayo miki amma na hana zuwa shago. In kuma kika ga ba zaki iya ba ki tafi gidanku don zan iya jure duk rashin hankalinki amma banda fita ba tare da izinina ba, ba zan lamunci hakan ba ko kaɗan."

Kallon-kallon suka tsaya yi zuciyoyinsu na tafasa domin kuwa wannan karon ran Muhammad ya ɓaci sosai domin ya tsani ya ga matarshi ta je shago tana sayan abu sai kace a bariki suke, wannan dalili yasa ya hana Salima wacce dama ko a gidansu ita bata fita sai dai su aika masu aiki ko almajiran da suke musu aika. Ya dawo ne don Juwairiyya amana take a gurinshi amma ba wai don yayi tsammanin zata lahanta kanta ba, wannan ba halinta bane sannan a da ta shiga damuwar da ta fi haka amma bai taɓa jin cewa ta yiwa kanta illah ba. Ya dawo kuma ya samu hakan ne wato tana nan lafiyarta kalau, sai dai ya tarar da guntun indomie da aka ci a plate aka bari akan carpet. Kenan Juwairiyya fita tayi ba tare da izininshi ba?

TAFIYAR MU (Completed)Where stories live. Discover now