9

118 27 6
                                    

FIKRA WRITERS ASSOCIATION...

WA'ADI...
✍🏾Safiyyah Ummu-Abdoul

Dedicated to Zeenatu Muhammad Lawal of blessed memories, Ubangiji Allah ya yalwata makwanci ya sadar da ita da dukkan Rahma...

9.

INNA RABBAKA FA'ALUL LIMA YURID
(haƙiƙa Ubangijinka ya kasance mai aikata abin da ya so)
                           _Ayar Ƙur'ani

Da ƙyar Hajiya Zulai ta isa ɗaki, zama ta yi gefen gadonta da tagumi hannu biyu. Tun tana tsumayen Alhaji Mamuda mamuda har ta gaji, mutumin da ya ce zai je salla shi ne bai shigo ba kusan ƙarfe uku, ko da ta gwada kiran shi sai jiyo ƙarar wayar ta yi daga falonsa, tana shiga ta iske ta a kan teburin tsakiyar falon. Nan ma wani jerin tsaki ta ja, kafin ta koma ɗakinta tana mai ƙunƙuni.

Sai a lokacin Firdausi ta faɗo mata a rai, cikin rawar jiki ta latsa lambobinta.

“Sweet mother!" Firdausi ta faɗa cikin sigar waƙa, hakan ɗabi'arta ce a duk lokacin suke waya da mahaifiyarsu, ko dai ta furta hakan a farkon wayar ko a tsaka ko daga ƙarshe.

"Sharhabilu ya kira ki?"

"Muradinsa zai cika ba! Gani nake kamar a mafarki fa Momma. Alhamdu lillah!"

Shiru Hajiya Zulai ta yi ba ta cewa Firdausi komai ba, dan ta yi imani da a kusa da ita take da sai ta wanke ta da mari.

"Momma!" ta ce jin shirun ya yi tsayi.

"Me zan ce da shashasha irin ki, fisabilillahi farin ciki kike Sharhabilu ya auri yayarsa."

"Oh Momma, what's wrong with hakan! Nan fa aunty Maryam ta auri saurayi da ta ba shekaru bayan mutuwar mijinta, and you gave all your support then." Firdausi ta tuna mata auren yayarta wadda tana cikin waɗanda suka yi uwa suka yi makarɓiya da faɗin ya dace.

"Rashin kunya za ki min Firdausi, ko kin manta da wa kike  magana ne?!" Hajiya Zulai ta faɗi hakan tana mai katse wayar.

Janyo matashi ta yi ta taro hannayen da ta yi tagumi da su. Komai ya dinga mata gizo a ido, tun daga haɗuwar Hajiya Maryam da Kamal, da yanda ta zagaye ɗakin Allah tana roƙon Allah ya tabbatar wa masoyan burinsu, kuma har a lokacin ba ta ga laifin aurensu ba. Amma ai Sharhabilu ɗanta ne, kuma tana da burika a kanshi wanda gaba ɗaya babu Zinatu a ciki, ta ina ma hakan zai yiwu!

Tana tsaka da karanta wasiƙar jaki ne ta jiyo sallamar Alhaji Mamuda. Kamar wacce aka tsikara ta tashi ta iske shi, daidai lokacin da ya durƙusa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarshi daga inda ya ajiye ta.

"Ai wai kira na kika yi?” Ya ce bayan ganin kiranta.

"To ai kai ne fa ka daɗe." Ta faɗa tana zumɓuro baki. Dariya ya yi ya ce,
"Shek Ibrahim ɗin ma ya kira sau huɗu, bari na kira shi.”

Samun wuri ta yi ta zauna cike da zaƙuwa, gabanta na bin ƙarar kiran bayan da ya sanya sautin wayar a amsa kuwwa.

"Akaramakallahu ka kira ba na kusa, mun je sauke farali ne.”

"Ma sha Allah, ma sha Allah! Ni ma na yi tunanin hakan a raina.” Alaramma ya furta, bayan 'yan sakwanni kuma ya ɗaura da faɗin, “Da ma na kira ne a kan auren ɗanmu, ka yi haƙuri ban isar ma da saƙon lokacin da ya kamata ba, ni kaina a jiya ya bijiro min da zancen, ya kuma nemi arziƙin a ɗaura, tun da ya kira Hajiya Zulai na ji amincewarta se ban jinkirta ba, amma ka yi haƙuri do Allah.”

"Haba dai, ai duk duniya Sharhabilu bai da uban da ya wuce ka Shehi, haƙƙinka ne ma zaɓa masa mata, yanzu yaushe ne ɗaurin auren?" Alhaji Mamuda ya amsawa Alaramma cikin girmamawa.

Hajiya Zulai ko in ban da harara kawai ba abin da take banka masa, ranta na suya, musamman yadda ta ji mijinta ke magana cikin ladabi, duk da ta san akwai girmamawa sosai tsakanin mijinta da Alaramma.

WA'ADI Where stories live. Discover now