12

116 27 13
                                    

WA'ADI
✍🏾Safiyyah Ummu-Abdoul

12.

Gaisuwa na musamman ga hajiya Naima, Ubangiji Allah ya sadar da ke ga farinciki a duniya, kabari, da ƙiyama, ya nesanta ki da dukkan ƙunci, cuta, da ɓacin rai.

Ina son ki Fisabilillah...

WA JA'ALNA BAINAKUM MAWADDATAW WA RAHMAH
(Kuma sai muka sanya soyayya da kyautayi a tsakaninku)
                        _Ayar Ƙur'ani

Sharhabilu na shiga ɗaki kwanciya ya yi, gaba ɗaya so yake ya yi bacci, ya san zai samu bacci irin wadda ya manta yaushe rabon da ya yi irinsa. Ko ba komai ba zai kwanta da zulumi da ƙishirwar son Zinatu ba, wanda tunaninta ya zame masa kamar wata ibada duk ƙarshen dare. Yanzu Allah ya ƙaddara ta zama mallakinsa, min haisu la yahtasibu. Irin rungumar da ya yi wa matashinsa kaɗai ya isa ya bayyana tsantsar farin cikin da yake ciki. Baccin ya fara ɗaukar sa ke nan sautin rurin wayarsa ya farkar da shi. Ya kai hannu inda ya ajiye wayar gefenshi yana mai jan wani dogon tsaki, ya duba sunan wanda yake kiran shi yana mincincine idanunshi saboda hasken wayar.

Ganin My Love a kan gilashin wayar ne ya sanya shi murmushi haɗe da amsa kiran.

"Fisabilillahi ba ki kalli lokaci ba kike kiran magidanci mai sabuwar amarya, kin san me kika katse kuwa!" ya  ce yana gimtse fuska kamar tana ganin sa.

"Me kuwa zan katse in ban da minsharin gardi, kai ban da lokacin nan yanzu. Ban da ni wa ka tura ma hotuna?" Jin nutsuwar da ya yi a muryarta ya sanya shi tashi zaune gaba ɗaya.

"E to, ƙila an tura ma 'yan nan gidan, amma ni de banda ke ba wanda na tura mawa, sis me ya faru ne?" Haka kawai ya ji gabansa na faɗuwa.

"Ga ku can kuna yawo Instagram, abin tashin hankalin ma labarin da aka dangana da hoton, ga kuma bayyanar dangin 'yarku." Firdaus ta ce murya a sanyaye.

"What! Bari na kira Aliyu, shi ke da hotunan."  Ya ce yana mai katse kiran, Addu'a yake a ranshi kar zinatu ta samu labari, dan bai san ya za ta ɗauki lamarin ba. Cikin ikon Allah bugu ɗaya ya same shi.

"Me nake gani ne Aliyu? Meke faruwa ne?" ya ce muryarsa na rawa.

"Daga cikin gidan nan ne. Jira, bari na ƙaraso ɗakin naka.”

Ko da Aliyu ya shigo ɗakinsa, nuna masa lokacin da ya tura hoton family group dinsu ya yi na WhatsApp, lokacin ya yi daidai da lokacin da hoton ya shiga sakon wacce ta fara buga labarin.

"Wane ze yi  haka to fisabilillahi!" Sharhabilu ya faɗa muryarsa da ɓacin rai ciki.

"Wa ma ya sani, na nemi ta sauke sakon ko mu yi ƙararta a kan ɓata suna da ta yi. Ta sauke, amma da na nemi ta bayyana min wacce ta sa ta buga sai ta ce hakan ya saɓa ma ƙa'idojinsu, tunda ta sauke ai shi ke nan."

"Ai ba saukewa ba ne  mafita, an riga da an yi ɓarna. Bari mu ga zuwa gobe mu ga ya abin zai kasance. Ban san meke gare ni da wasu ke ganin na fi ƙarfin Zinatu ba. Kai mutum na da wuyan sha'ani, Inna da Gwaggo sun matuƙar ba ni mamaki musamman ma Inna, ita Gwaggo ai na daɗe da sanin hawainiya ce."

Mamakin kalaman da Sharhabilu yake ya cika Aliyu, ya san Tahir ya taɓa zuwa masa da zance shigen na Sharhabilu, wannan ɓaraka da ke Kunno kai zuriyar Alaramma. Nan take ya danne saboda ba ya son abin da zai ƙara zargin da zuciyarshi take. Maimakon haka sai ya numfasa ya ce da shi.

"Manta da su fa, kar ka bari hakan ya dame ka, shirme ne irin na mata, yanzu dai ka lalubo mutuniyar ka ba ta baki, dan na tabbata ta san abin da ke faruwa." Aliyu ya ce yana mai miƙewa da ficewa daga ɗakin.

Sharhabilu ya yi shiru yana tunani, dan dai gaba ɗaya kansa ya kasa yarda da abin da aka yi. Wai wa zai yi haka?, Gani ya yi dai 'ya'yan Alaramma na da haɗin kai, to zuciyar waye guba ta gurɓata har da yake ƙoƙarin kawo ɓaraka cikin zuriyar? Da a ce Inna da Gwaggo na da wayewar sarrafa kafofin sada zumunta da zai rantse aikin ɗaya daga cikinsu ne. Lokacin da yake zaman gidan, ba zai manta yadda Gwaggo ta so ɓata Yaya a idonsa ba, da ta ga ba ya ɗauka sai ta koma yi masa wa'azi akan muhimmancin mahaifiya, tana mai nuna masa kamar ba ya daraja tashi mahaifiyar ya fi darajanta Yaya m. Da fari abin na damun sa matuƙa, sai ya kwana ya wuni yana neman ta inda ya tauye mahaifiyarshi, amma haka zai gaji ya bari.

WA'ADI Where stories live. Discover now