page 02

298 13 2
                                    

*_KURMAN BAƘI_*

*H U G U M A*

PAGE 02

           Muhallin da ta tashi dazun a dakin shi ta koma ta zauna,har yanzu babu wani sassauci data samu ko qanqani,duk da cewa daga ruqayya har saleem ta barwa kowa a cikinsu saqo. Sam bata damu da tarin qazantar dake a sashen nata ba bare hankalinta ya dauku wajen ganin ta tsaftace shi,duk kuwa da cewa rana ta fara yi,kuma lokaci ne da ya kamata ace gurin ya kasance cikin kintsi da gyara. Ba abinda yafi damunta irin uban kudadenta data kashe,ta siya magunguna masu tarin yawa na mata,magungunan da aka bata tabbacin sunansu KAFI MALLAKA. Kuma muddin tayi amfani dasu ba saleem ba,duk wani wanda yake rayuwa da saleem ma zaya zama qarqashinta ikonta da zabinta ne. Sai gashi gaba daya daga kudin har maganin babu abinda ta amfana dashi,maganin da yake na kwana biyu ne,tayi asarar dare daya,saura dare daya ya rage mata,wanda bata da wani hope a kanshi,saboda bahaushe ma ya fadi juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta. Irin rabuwar da sukayi da saleem a yau bata tunanin zai nema wani abu daga wajenta a daren yau din,ita kuma batajin koda zatayi asarar kudin data zuba zata iya saukar da kanta ta nemeshi,muddin ba shine akayi katari ya saukar da kanshi ba.  Koda bai bata haquri ba tana iya sallamawa,saboda kaf kudaden da ya basu ne saboda siyayyar sallah tasu data yara ta narka a ciki cike da yaqini da imanin zata maida mafiyinsu muddin tayi amfani da maganin.

           Kamar wadda aka tsunkula ta miqe da sauri,ta sanya hannu tana jawo locker din madubinta. Tarin ledoji ne da tarkacen da zakayi tsammanin qaramar bolar mahaukata ce dake cunkushe da karikice,wasu a leda,wasu a kwalaye,wasu a takarda,wasu ma saboda rashin gyara da kintsin gurin sun fashe sun barbade a cikin locker din.

            Da kallo tabi locker wani takaici yana sake ninkuwa a zuciyarta

"Wai dame na gaza da har yau na kasa ture wannan baqar matar tasa?,dame ruqayya ta fini ne?" Ta tambayi kanta tana qarewa locker din kallo,tako ina bata wasa da gyaran HQ dinta,duk wami magani da zata gani ana tallatawa,ko taji labarin kyan ingancinsa da aikinsa a gurin qawaye saita tabbatar ta mallakeshi hankalinta yake kwanciya,amma har yanzu ta gaza samun nasarar da take hangowa kanta.

            Hannu ta saka ta dauko baqar ledar dake ajjiye daga gefe tana jan tsaki,kunceta tayi saman madubi,wasu qullukan garurruka ne da dunqulallun wasu abubuwa guda hudu. Daya brown daya baqi daya fari tas dayan kuma kore. Tsaki ta sake ja

"Fiye da rabin ma da akace nayi inserting nasu ashe nayi,banajin wadan nan ragowar zasu samar min da abinda nakeso" ta qarashe maganar tana maida ledar ta qulle. Gwara ta samo wani abun da zai cikashe mata gibin da zata samu.

              Saman hautsinannen gadonta ta miqa hannunta,ta cusa shi qasan pillow dinta ta ciro wayarta. Kai tsaye data dinta ta kunna,sannan ta hau watsapp dinta.

             Tarin saqwanni ne suka shiga shigowa,duk da jiyan raba dare tayi tana chart kafin ta rufe tabi saleem din bedroom dinsa.

             Fitsarin da ya cika mata mara ya sanyata ajjiye wayar a gefan gadonta,sannan ta miqe da sauri ta tura qofar toilet dinta ta shige.

               Saman tiles din toilet din ta tsugunna ta kwata fitsarin. Sai ta dinga bin fitsarin da kallo saboda wasu launika da ya fito dasu da wani birtsi birtsi. Tsaki ta saki tana jin wani sabon bacin ran

"Kalli yadda damshina da aikin maganin ke bi ta rariya a banza,haba,dole a yiwa saleem uzuri,akwai abinda ke shan kansa" ta fada a zuciyarta.

               Ko digewa fitsarin bata jirayi ya gama yi ta miqa hannu ta tari ruwan famfon dake kwarara ta yafawa wajen,ta sake miqa hannu ta tara ta yafawa gurin ba tare da ta sanya hannu ta wanke ba,ta miqe tana qoqarin maida pant dinta da uban danshin dake maqale a sumar dake mararta damqam,wadda a qalla kusan watanni biyu kenan cikin ta uku ba tare da ta samu aski ba.

KURMAN BAK'IWhere stories live. Discover now