https://chat.whatsapp.com/EKyzZCUEGyRAEGGAnTHmGF
*_KURMAN BAƘI_*⚫⚫⚫
*HUGUMA*
PAGE 10
Hankali kwance cikin nutsuwar ta ta macen da tasan kanta ta tura kanta cikin gidan bakinta dauke da sallama. Sai da tayi sallama sau biyu kafin a amsa. Daga can cikin daya daga cikin dakunan dake hannun hagunka.
"Da alama umma bata nan" ta fadi qasa qasa ta wucewa dakin da take jiyo ana amsa mata sallamar.
Labulen ta dage tana sake jaddada sallamarta. Ido hudu sukayi da matashiyar dake zaune saman abun salla. Sanye take da hijab har qasa,baka ganin komai sai fuskarta da tayi wani haske dauuuu,irin hasken da kana masa kallon farko zaka san cewa ba natural haske bane. Hannunta da yanayin hasken fatarsa yasha banban da hasken fatar fuskarta na riqe da carbi tana ja daya bayan daya,bakinta yana motsawa mis mis da alamun wani abun take karantawa
"Iskancin banza,ashe kina ciki kina jina naketa kwada sallama" ta fadi tana dan jifanta da harara hadi da zare takalminta ta shigo dakin gaba daya tana cewa
"Yo wannan basai a shigo ayi muku sata bama?" Tayi maganar tana zama gefan kujerar guda daya dake dakin idonta akan matar.
Hannunta ta dora saman bakinta alamar tayi shuru,sannan taci gaba da jan carbinta. Sasakai ruqayya tayi tana binta da kallo,sai kuma taja tsaki ta maida dubanta ga dakin.
Kayan ado ne jere sama madubin,mayuka kala kala da turaruka,harda kwalabe da gwangwanayen supplement kala daban daban.
Kan supplement din hankalinta yakai,ta miqa hannu daga inda take ta dauki wata zungureriyar kwalba dake dauke da syrup a ciki.
Tun a rubutun farko ta fahimci maganin qara qiba ne,saita daga kai tana kallo fuskar matar dake zaune akan sallah. Tabbas,ta qara qiba qiba data jima tana mamakin ya akayi wasila siririya da ake tsokanarta da sunayen tsokana kala kala saboda rashin qiba lokaci guda tayi irin wanna qibar?. Mamaki ya hanata magana,saita mayar da kwalbar ta ajjiye dai dai sanda idonta ya gano mata wani tablet din dake nuna whitening yakeyi. Kai ta sake jinjinawa tana maido dubanta ga wasilar,dai dai nan ta shafa hannunta akan fuskarta da alama ta gama.
"Ke kuwa me kika zauna yi har rana tana shirin faduwa bakiyi sallar la'asar ba?"
"Haba ni da nake da tarin buqatu?,ta yaya zan bari sallar ta kufecemin? la'asar dinta liman yana sallamewa ina sallame tawa,wannan wani wuridi aka bani nakeyi"
"Wuridi ko addu'a"
"Duk daya ne ai" ta amsa mata tana ninke sallayarta
"Addu'ar ce idan anayi ba'a amsa sallama?,nidai a iya sanina salla ce kawai ya haramta idan anayinta ayi magana" Ruqayya ta sake jifanta da tambayar
"Ke wannan ba irin addu'ar da kika sani bace,wannan ta neman miji ce,yazo ayi aure nima na ganni a dakina na huta kamar kowacce mace" ta fadi tana zare hijabin jikinta t wurgar gefe,hakan ya sake bayyanawa ruqayya qibar da ta tsammata daga wasilar,saidai ashe hijabi ma ya rufe wani abun.
Kasa shuru ruqayya tayi tana duban wasilan tace
"Yanzu wasila wannan wacce irin qiba ce haka da uban fari da fuskarki tayi?,ga kunnenki duk kin bula kin cikashi da barima?" Gefen ruqayyan ta zauna tana daukar wayarta
"Ba zaki gane bane,ke don kina dakinki asirinki a rufe,yanzun rayuwar sai da updating sai kina gyara,idon mazan a bude yake,saisu rainaka ko kiga wanda baikai ajinka ba yazo yace kai yakeso saboda rainin hankali"

YOU ARE READING
KURMAN BAK'I
Non-FictionKURMAN BAQI ne me wuyar fassaruwa,ga duk me nisan zangon hankali da tunani zai tsinkayi hakan,DAN JAGORA NE ga mata,musamman masu KISHIYA,kuma hannunka me sanda ne ga masu sana'a data shafi labarin dake cikin littafin