page 03

224 8 0
                                    

https://chat.whatsapp.com/HeRo2w8C8gdG0Et1lqafjk

*_KURMAN BAƘI_*

*H U G U M A*

Page 03

            Yara biyu ne a gaba suka fara shigowa,mace da namiji wanda dukkansu ba zasu wuce shekara goma da hudu ba. Macen itace babba sai namijin. Farare ne sosai kamar yadda yanayin fatar mahaifiyarsu zainab take. Daga bayansu sauran yaran maza biyu suka shigo. 'Yan biyu ne identical masu kama da juna sosai. Rirriqe labulen sukeyi suna shigowa a hankali da alama babu sakewa sam a tattare dasu. Tunda sukaga qofar maman nasu a kulle hankalinsu ya gaza kwanciya,duk da qarancin shekarunsu amma dai dai da rana daya basa qaunar su shigo gidan su samu mahaifiyarsu bata nan.

                Zainab daketa fadin tashin kintsa falon ta watsa musu harara

"Shegu masu shegen baqin hali,duka duka shekarunsu basu wuce a qirga da yatsu ba amma sun iya nunqufurci da shegen gulma da sanabe irin na uwarsu" ta fadi idanunta a kansu kamar zasu fado,har yanzu tana jin dacin haifar yaran a dai dai lokacin da take ganin cewa itace da gida,a sanda dukka lissafinta ya gama bata ta gama mallakar saleem mahaifiyarsa da kuma danginsa,ta haifa masa abinda ya jima yana mararin samu wato 'YA'YA,sai gashi a dare daya ruqayyan ta gigitata da wata irin ba zata da bata shirya mata ba.

"Don uwarku ku koma idan ba zaku shigo ba" ta fada cikin daka tsawa tana jan tsaki. Tsam al_hussain ya riqe hannun al_hassan yana mele baki alamun zagin data masa ya taba ransa. Yafi al_hassan zuciya sosai,sai kawai ya figi hannun dan uwansa suka fice zuwa babban parlor din da ya hade qofofin falukan da suka samarwa da kowaccensu sassanta.

"Kinga shegen yaro?" Zainab ta fada cikin mamaki tana binsu da kallo. Tun yanzun yaran suke da wani irin hankali da saurin fahimtar abu,tana tunanin gaba zaiyi wuya basu zame mata tarnaqi ko alaqaqai ba.

"Zakaci ubanka zanga ka dawominne" ta fada tana daga murya don ta tabbatar suna falon a zaune.

"Mama yunwa nakeji fa gaskiya" babbar diyarta haneefa ta fada tana yamutsa fuska

"Iyalan ci da baku da aiki sai cin abinci,yo nima banci ba tun safe,ki bude lunch box dinki ki cinye sauran abinda ke ciki kafin na gama kintsa gidan na dora" ta fada tana ci gaba da hidimar gabanta. Ita a yanzu ma bata abinci take ba,maganinta kawai take kasa kunne taji me delivery yace gashi ta afa ta tabbatar ya isa cikinta. Yunwa ba yau ta saba zama da ita ba.

"Mama dumamen abincin jiya ne fa dama kika zuba mana,kuma wallahi tun kafin azahar shinkafar ta jiqe,sai abincinsu alhassan muka ci"

"Kut" zainab din ta fadi tana dakatawa da abinda takeyi bayan ta waiwayo

"Uban waye yace kuci musu abinci?,ban hanaku ba?" Ta fada cikin fushi tana kaiwa yarinyar mari. Tun ranar da yaran suka taba yabon girkin ruqayya a gabanta saleem ya tayasu taji ta tsani duk wani abinci da zai fito daga gurinta,duk kuwa da cewa girkin dare hadawa sukeyi,hasalima tare sukeci a babban falon gidan.

             Zagi ta shiga dura mata abinda ya sanya yarinyar sakin kuka ta miqe tana zubda jakar makarantar da flask din a wajen tayi dakinsu da gudu. Hakan bai hana Zainab ci gaba da masifa ba kamar zata ari baki,da da hali dukan tsiya zata yiwa haneefa din a yau,saidai ta tabbatar muddin ta taba lafiyarta kamar a kunnen mahaifinta,abinda kuma tasan bazai haifar mata da d'a me ido ba,tana son yau ta gyara wasanta ba zata bar wani abu na rashin jin dadi ya wargaza mata shirinta ba,dole yau tayi kaffa kaffa da komai.

              Dan qara speed na motar tayi hankalinta yana kan lokaci. Tasan tabbas zuwa yanzu yaran sun dawo,bataso hakan ba amma uzurin da ya riqeta dole ta gama kafin ta taho.

             Shigowar motar tata yaja hankalin yaran, suka watsar da abinda sukeyi suka rufo da gudu gurinta. Tana qoqarin bude murfin motar amma sun hanata saboda yadda sukayi tsaye a bakin qofar suna murnar ganinta. Murmushi ta saki tana dubansu zuciyarta na karyewa. 'yan awanni kadan tayi bata gidan,amma dukka hankalinsu ya tashi,ina ace yau mutuwa tayi ta barsu?. Cikin taqaitattun mintunan da ta qara bata nan yaran har sun fara fita a kamanninsu,sunyi wasa a farfajiyar gidan sun vodeyAllah,suit din uniform din tasu sun cikata da qasa da ruwa abinsu,kada ma kayan alhussain yaji labari.

KURMAN BAK'IWhere stories live. Discover now