2/1

38 0 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI💕*

Ina yima ɗaukacin al'umman musulumai barka da sallah fata anyi sallah lafiya Ubangiji Allah ya maimaita mana Allah ya amshi ibadun mu yasa muna cikin salihan bayin sa wanda ya ƴata cikin wata mai albarka Allah yakare mu da imanin mu yasa mu gama da duniya lafiya Allah yajikan wayanda suka rigamu gidan gaskiya mu kuma idan tamu mutuwar tazo Allah yasa mucika da imani Amin.

✨ *GORGEOUS WRITTER'S FORUM* ✨

     ✨ *G.W.F* ✨

BOOK2

CHAPTER 1

Rai a ɓace yake kallon ta ji yaje kaman  yayi da naushin ta haka yakeji saboda yanda taurin kanta yake bashi haushi saide yafiso yabita ta lallami ko zata fadi inda ta ajiye abunda suke nema kafin sannan zafin rai banashi bane harsai yasamu abunda yake nema kafin yafito mata da ainihin colour dinsa zata san koshi wanene.

Tari take kaman zata shiɗi dafe take da cikin ta,duk halin da take ciki itade burin ta be wuce wanda aka kira da Ogan su ya saurare ta ba,ka adanamun ita sannan ka kulamun da ita sosai fiyema da yanda zaka kula da kanka ta tsinkayi muryan sa yana ma wannan sakandamin magana kafin tace me tuni ya ɓace ma maganin ta yana baza babban rigar sa wasu manya majiya karfi na biye dashi a baya,batasan sanda wani irin kuka yataso mata ba,aiko take tasaki abunta mai sauti da karfin ta take yinsa.

"Wallahi iya abunda nasani kenan kuyi hakuri kuman rai nayi kuskure wallahi sharrin sheɗan ne,bige masa baki Ahmad yayi ya kafesa da idon sa daya rine yayi jajir yace"dalla malam rufewa mutane shegen bakin ka mai ɗuyin nan,mutane sai kunyi son zuciyar ku kuma kuzo kuna wani cewa sharrin sheɗan akwai shedan dayafi kane?nace akwai wani sheɗanin da bayan kai da kake zaune nan gaban mu?ya daka masa tsawa.

Jikin sane ya dauki rawa karkarkar yana girgiza kansa badan Faisal daya shiga tsakanin su ba da Ahmad yasake rufeshi da duka,Oh yace yana cizon dan yatsan sa yajuyo wa Faisal din yayi yana cewa why broo meyasa kake hanani dukan wannan sheɗanin ba bazaka bari na shaƙe shege har lahira ba kake hanani kasan munin abunda ya aikata kuwa?

Dafa kafadansa Faisal yayi yashiga cewa cooldown mana broo"dont cool me down akawan ɗan banzan karen farauta.

Baba maigadi de baki yakumbura sumtum fuskan sa duk ancanza masa kamanni ba baki sai ido wirƙil wirƙil wirkil,iya tsoro ya tsorata da betaɓa tsammanin abun ze zo masa a haka ba,ganin Ahmad din dayayi shiru shiru betaɓa tunanin yana da zafi har haka ba,ya dauka komai ze tafi yanda suka tsara sai gashi tun ma ba'age ko ina ba asirin sa ya tonu sai gashi da tuƙwicin duka.

Alhaji surajo yakasa zama sai kai kawo yake yama rasa wani irin tunani ze soma yine,wai wake bibiyar su dole akwai wanda yake bibiyar rayuwar su,idan ko ba haka ba taya zace mutum goma da suka tura saudiya da kaya ace duka ankame su ba ko mutum ɗaya daya tsallake kuma dukkan su tun a airport ake kamasu da kumshin cocaine a ciki,wai meke shirin faruwa ne damu ne haka?haka wancan satin aka kama masu kaya na kimanin 500m a kudin mu na nan Nigeria a Delhi India,sunyi asarar muƙudan kuɗaɗe,idan ko hakan be dena faruwa ba lalle wata talaucin su yana gab da kamawa.

Wayan sa yaciro yakira lambar Alhaji Bala bugu biyu aka ɗaga tun kafin ma yayi magana wanda yakira din ya rigashi yana kiran sunan sa"Surajo karka sake kirana bani da wata alaqa daku idan wancan jakin kake nema yanzu haka yana Abuja yaje ya dauke ƴar mutane saide idan ya saba taɓa ƴaƴan wasu yakwana hankalin shi kwance bana tunanin wannan karon hankalin sa dama duka wanda yake tare dashi ze samu kwanci,cire wayan Alhaji Surajo yayi daga kunnensa yana kallon screem din dan son sake tabbar wa ba tsaɓa lamba yayi ba.

Saide tsaɓanin abunda yake tunani ne Alhaji bala ya gani rubuce baro baro da manyan harufa katse shi yayi yana cewa"Bala shin kayi haukane?kake irin wannan maganganun harmafa kirana kayi Surajo gatsai ba ɗan tsaƙayawa yau"ba sunan ka kenan ba Surajo ko kana da wani sunan bayan shi?kaga kaina ya dauki zafi saboda zafin da kaina yake har turiri yake fita daga saman kaina,bana iya fahintan komai yanzu saide abu ɗaya zan iya faɗa maka shine muddin sunan ƴata ya lalace ko nasamu matsala da iyalina to kuyi kuka da kanku dan ba hakura zanyi inyi shiru ba,yana fadin haka ya kashe wayan yabar Alhaji Surajo riƙe da waya saima bin wayan yayi da kallo kaman wanda ze hango Alhaji bala ta ciki.

AUREN WUCIN GADI 2Where stories live. Discover now