2/4

23 0 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITER'S FORUM* ✨

  ✨ *G.W.F* ✨

BOOK 2 CHAPTER 4

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

  Wani irin taƙaicin Anty Hajia ne ya kamashi kwafa yayi yana cewa ina nan zaune zaki nemi nazo na dauki Matata dan ba zuwa zanyi ba,idan ma kina tsammani zan biyo tane zan nuna miki ni ɗan zamani ne.

Itama  Anty hajia ta ɓagaren ta tana sauke wayan a kunnen ta ta kalli Yayar ta tace"Yaya ni Yaron nan yake neman mai dawa ƴar iska ina masa magana yayi shiru yana jina karshe ma kashe wayan sa yayi to wallahi zan nuna masa dani yake zance sai nasaka shi sintiri tsakanan Abuja da Kano idan ba haka sunana ba Ikilima ba.

Murmushi mai faɗi Ammi tayi tace"nide a masa da sassauci Anty yara karki zautarmun da ɗa kinsan be iya saka abu arai ba,kuma ke tunda kikaga ya tafi da ita ai ko be furta ba ai yaci ace kingane ɗiyarki itace wacce ta ciri tuta ta zama zara cikin wata.

Ƴar dariya Anty hajia tayi har Alhaji badamasi yana tayata yace"nimade nayi mamaki Allah de ya tabbatar da alheri ya haɗa zuciyoyin su amma duk da haka ina bayanki Ikilima koda zaki bashi ita kibari saiya garu da kyau ya gane darajarta da ƙimarta yadena ganin kaman alfarma akai mata aka aura masa ita,yadena bubbuɗama ƴar mutane hanci yana aure wucin gadi nayi da ita.

Dariya Alhaji Badamasi yayi yace"ina bayanki Ikilima da gaskiyar wallahi"au bade harka ka fara shiri da ita ba yanxu kun haɗewa Yaro kuna neman rabashi da matar sa.

"Ayyah Yayah ai banyi komai bama nida ya sace mun ƴa ya tsallake garin da ita,nayi magana Aure ba lefe ba biki ai ba zeyu ba,ko zan bashi ita sai yayi zarya yabimu sauda ƙafa kafin mu du ba lamarinsa,ta ƙare maganan tana sakin murmushi.

*****Sun sha hirar su sosai cikin dare hiran da ta dauke su har karfe biyun dare,sai Anna ce tac"Aisha kwanta ki huta kina ɗauke da gajiyan hanya gashi ko abinci baki ci ba,wancan yaɓare bara na nemo miki wani abun kici karki kwana da yunwa,ta yunƙura zata tashi riƙo hannun ta Aisha tayi cike da kewar Mahaifiyarta tace"Anna yi zaman ki yanzu fa karfe biyun dare kumama ni banajin yunwa ganin ki a kusa dani kawai ya ƙusar dani,haƙiƙa yau ranace mai mahimmanci gareni ranan da bazan mance da ita a rayuwa ba.

Gani gaki Anna ina kwance a jikin ki ina jin ɗuminki ina baki labarin rabuwar mu,wannan kaɗai yaƙusar dani yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa inama khadija da mubaraq suna tare damu yau.

Anna mace mai kawaici da kara sai cewa tayi"me kikeci na baka na zuba Aisha ai suma zasu ganni ne nasan Auta saiya fiku jin daɗin ganina da zeyi.

Tashi zaune Aisha tayi tana kallon Anna tace"lallema wato son kai Allah ni nafisu jin daɗin ganin ki bakiji yanda nakeji ba.

Shafamata kai Anna tayi fuskarta ƙunshe da farin ciki tace"da wasa nake miki amma kema kinsan dole Auta yafi kowa farin cikin gani na"harda Abba?ta faɗa cikin tsuɓutar baki.

Shiru Anna tayi tana ƙureta da Ido mukut ta haɗiye wani ƴawu mai kauri tafara inda inda tama rasa ta ina zata soma,tsab Anna tamiƙe batare da tasake cewa komai ba tace"ki kwanta ki huta sai da safe taduƙa tana tattare kwanukan da yaɓare ɗazu.

Jiki a sanyaye Aisha ta miƙe tazo batayi wata wata ba tafaɗa jikinta ta rungume ta tabaya ta fashe da kuka tana cewa"dan Allah Anna kiyi hakuri banyi danna ɓata miki rai ba"naji jeki ki kwanta mayi maganan da safe yanzu dare yayi.

"Nide dan Allah Anna kiyi hakuri ina zan samu kwanciyar hankali kina fushi dani,tasake fadi tana ƙarawa kukan ta himma,cike da fushi Anna ta saka dayan hannun ta ta ɓanɓareta daga jikin ta cikin daure fuska tace"oya jeki ki kwanta banson gardama.

AUREN WUCIN GADI 2Where stories live. Discover now