2/3

36 1 0
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITER'S FORUM* ✨

*HOME OF GORGEOUS INTELLIGENT,AND EXPERT WRITER'S WE ARE THE BEST AMONG THE REST.*

   ✨ *G.W.F* ✨

BOOK 2 CHAPTER 3

  Cikin rarrabuwar murya mai haɗe da sonyin kuka nasake furta"ANNA rawa hannu matar dake tsaye bakin ƙofa riƙe da tire mai dauke da wormer na abinci masu kyau da plat  yafarayi batasan sanda tasake tiren hannun nata ƙasa ba,itama cikin wani irin murya mai haɗe da tashin hankali ta shiga faɗi"anƴa Aishata tawa ce kode zigo yauma kikemun kaman yanda kika saba yimun a sauran lokuta?

Hawaye masu ɗumi suka shiga shatata saman ƙuncinta,jin abunda matar nan ke cewa yasaka Aisha tashi daga inda take zaune tashiga takowa har tana haɗawa da sassarfa tafaɗa jikinta tasaki wani irin kuka"Anna dama zamu haɗu ashe da rabon haduwan mu ina kika shiga kika barmu nayi rashin ki Anna ta munyi kewanki banfidda rai daga rahman Allah na cewa watarana zamu hadu zakizo garemu ba, haka Aisha taringa  sumbatu tanayi tana kuka ita kanta Annan kuka takeyi amma na farin cikin haɗuwarta da gudan jinin ta data ɗebe tsammanin haduwar tasu nan kusa.

Alhaji Sunusi ya shiga firgici iya firgici ya kaɗu sanda labarin ƙubutar da Aisha wasu jami'an farin kaya sukazo sukai tare da tafiya masa da Yaron sa wanda yakeji dashi wato Samude da sauraran Yaran mata dasuke ƙoƙarin fitar dasu waje jibi,dafe kansa yayi yasan idan Alhaji Surajo yaji wannan labarin sai ransa yasake ɓace duk rashin imanin sa da tausayin sa Alhaji Surajo da Na Allah Ubannin sane sundame shi sun shanye,shi sai yanzuma nadaman biyewa zuciya dayayi wajen shiga har gidan Na Allah ɗauko Yarinyar da yayi yake duk da Alhajin yana kwancene a gadon Asibiti amma muddin yaji wannan labarin to fa shi nashi yakusa karewa.

Wayansa ya dauka yasake kiran wata lamba akaro na ba adadi saide har yanzu amsan ɗayace,switch off cilli yayi da wayan yana dafe kansa yakai gwauro yakai mari yarasa ma abunyi kawai sai yashiga haɗa kayan sa ya yankewa kansa shawaran barin ƙasar yasan kafin susame shi koda a wayane sai komai ya lafa  daukan wayansa dayayi cilli da ita ɗazu yayi yashiga kiran wani Yaron sa yayi a waya kan yayi masa booking flight yau koman daren yakeson barin ƙasar baki ɗaya.

Bayan gama wayan sa duk yakasa nutsuwa yazauna waje ɗaya,wayan sa daya ajiye a gefen sa tayi ringin kaman baze dauka ba saboda yanayin da yake ciki amma ganin wanda yake kiran nasa yasashi dauka yana ƙarata a kunne"idan kana a tsayene kanemi waje ka zauna idan ko kana zaune ne toh inaso kanutsu ka saurareni.

Abunda aka cemasa kenan batare da an bashi koda daman yin sallama ba,kunna wayan ka kaga abunda yake faruwa a gari idan ma kana tsammanin barin garin ne to gwara kayi zaman ka dan shine rufin asirin ka daga haka sai kitt aka kashe wayan.

saida aka kashe wayan sannan yasamu zarafin yin tunani"anƴa Alhaji Shehu ne mai maganan nan kuwa?amma muryar kaman batashi ba,wata zuciya tace masa kaide kawai kunna wayan ka kaga abunda aka turo maka.

Datan wayan sa yakunna,Alhaji shehu ya gani tsaye ƴan jarida sun zagaye shi yana musu bayani da cewa"gaskiya kaman yanda kuka sani nan din wajen ajiya na ne nakan ajiye masara duk shekara amma shekara biyu banyi ajiya ba.

Wani ɗan jariya ya jeho masa da tambaya yana cewa"saboda kabawa masu garkuwa da mutune hayan wajen yasa kadena ajiyan ko kuwa?a fusace Alhaji Shehu ya daga yakalli dan jaridan da yayi masa wannan tambaya yace"ko ɗaya bansan ana wannan ɗanyen aikin anan ba,da ace da sanina ake aikata haka dakaina zankai ƙaransu ga hukuma ai basufi karfin hukuma ba,inada wajen ajiyan daban a Samu naka ina ajiyan ne acan saboda yafi mun sauki nan sainayi kuɗin mota can kuma koda zanyi bekai yawan wanda zan biya akawo nan din ba.

Banida alaqa da wanda aka kama tare da Yaran nan bansan suba,asalima bansan sun fake dani suna aikata ɓarna ba da inda masaniyar haka ni da kaina zan shigar dasu ƙara saboda ɓatan suna dasukai kuma kowaye ya ɗaure musu gindi sainayi shari'a dasu.

AUREN WUCIN GADI 2Where stories live. Discover now