2/7

91 4 1
                                    

💕 *AUREN WUCIN GADI* 💕

✨ *GORGEOUS WRITER'S FORUM* ✨

    ✨ *G.W.F* ✨

WRITTEN:ZAHRA ALI ABDULLAHI

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM.

BOOK 2

Chapter 7

Yanda Hajia bilki take a rikice hakama Alhaji Sunusi yake harma gwara ita Hajiar akan shi dayake namiji,tunda yaga halin da ƴar tasa take ciki yayi baya ze faɗi sai tarosa mai gadi yayi yashiga bashi baki,zuface yaji yakaryo masa tun daga tsakar kansa har dunduniyar ƙafar sa.

wani irin tsorone ya shige shi lokaci guda bade Alhaji Shehu bane yamasa haka dan yace masa matukar wani abu mara daɗi yasamu ƴarsa to kowa sai ya amshi rabon sa,karde shine yamasa haka,jiki na rawa ya ƙarasa inda take a kwance cikin rawan jikin yakai hannu ze taɓata"ranka ya daɗe nace ko zamu kaita asibiti ne?inji driver cikin ɗari ɗari yayi maganan"Eh Asibitiiiiii hajiya balki tafaɗa dakarfi tana mai wage baki sai mai gadi da driver ne yanzun ma suke cicciɓeta sukai waje da ita suko Iyayen binsu kawai suke a baya dan ba mai ƙuzari ko ɗaya acikin su.

Duk yanda Ahmad yake daukan abunda sauki abun ba haka yake ba,dan ƙaramar yarinya daya rena tana neman sauya masa tunani,hatta aiki nawani lokacin sai yayi da gaske sannan yake samunyi.

Gefe guda kuma sun haɗa kan Alhazawa dan tuni shakkan junan su yafara ɗarsuwa a zukatan su sun fara samun tsaɓani a tsakanin su.

Dama sana'ace akeyin ta ba gaskiya cikin ta zalumci da zamba yafi yawa a cikinsa hakan sai yabasu daman wajen karkata zarginsu wa junan sa rashin jutuwa yafara yashiga tsakanin su,gakuma asara da suke ta tabkawa a ƴan watannin nan ga yawan kame musu mutane da akeyi kuma ba wanda yasan inda ake kaisu yawanci akwai mutanen su daga ko wace ƙasa cikin jami'i da duke basu bayanan kamai amma ko sunyi kira anyi musu bincike to saide su samu labarin tunma kafin su shiga airport ake kamesi ko kuma da sunfita daga airport ɗin abun kaman almara yake faruwa dasu.

*****
Daddy Ishaq yau ko yaran sa sun sheda yana cikin farin ciki mara misaltuwa da ganin matar sa sanyin idaniyar sa wacce ya fidda tsammanin sake haɗuwa da ita,su Goga kuwa Albarka sun shashi yafi cikin carbi daya ƙalli Anna Nafisat ɗinsa zaune kusa dashi sai yace"Allah de yama yaran nan Albarka ya faranta musu kaman yanda suka faranta mun rai ya karesu daga dukkannin abun ƙi ya sadasu da alkharan sa.

Itade Anna saide tace Amin cike da kunya daga karshe de Daddy Ishaq yakira su Goga yace yau da gobe duka ranan hutuce a sauke duk wani abunda zamuyi cikin kwana biyun nan,dariya kawai sukai masa dan su shedane irin ɓakar wahala dayasha a hannun su Alh Sunusi,har yakamu da ciwon damuwa duk randa ciwon nasa ya motsa baya masa da daɗi tsakanin sa da wanda yake da ciwon taɓin hankali abune ƙalilan,kullum addu'arsu shine Allah ya bayyana masa da iyalansa ko ze dawo daidai Alhamdullahi yau gashi Allah ya amsa addu'an su sun samo masa matar sa batare dako ɗaya daga cikin su yasan itace ba.

Aisha dake zaune a ƙasan carpet kanta a ƙasa tace"Abba gobe nakeson komawa can wajen su Auta.

Shiru kaman Daddy Ishaq baze amsa ba,sai kuma ya ɗago yana kallon Anna yace kinji abunda ƴarki ke cewa ko?murmushi tayi tace"toh ni me zance mata Abban Aisha ɗazu Faisal ma yaxo naji yace jirgin karfe  takwas na dare zasu bi Mamin sa ta matsa Aisha ta koma can,bande san dalilin ta ba.

Murmushi yayi irin tasu ta manya dan kafin shigowansa sunyi waya da ita Ikilaman take ce masa"ɗan jarida nasanka nasan halin ka karkace zaka hanani abunda nake niyan yi Aisha zatazo zama dani harsai Ahmad ya hankalta"nikan Ikilima meyasa ku mata wani lokacin baku da hankaline kibar Yara su zauna Gidan su,ta tari numfashin sa tana cewa"karkace haka so nake sai Ahmad yabar ganin kaman alfarma yayi mana da muka aura masa ita,har yake wani ikirarin auren na wucin gadine to inason tabbatar masa cewa ɗiyata tafi karfin auren wucin gadi tafi karfi tabishi saide shine ze bita wallahi,shide dariya ma maganar tata tabashi yace da Anna"kindeji dalilin ƴar uwartaki itama son  daurema karya  gindi harwani cewa fa take ya daukar mata ƴa ya gudu bawani biki ba kayan lefe neko ce mata nayi ba yabada sadaki ba"Allah ya kyauta cewar Anna ita ko Aisha dama ta jima da barin wajen hakama su Goga dasukai waje suna ƙumshe dariyar su yanda Ogan nasu yake wani shagwaɓema Mama sunan da suka samata tun ranan da suka sameta.

Karfe bakwai da rabi daidai Yah Faisal yazo daukan Aisha dan kaita airport dan shi aiki yamasa yawa baze samu kaita Kano ba,saide koda yazo gidan nan yakejin labari mai daɗi daga bakin su Goga na anga Mahaifiyar Aisha din wannan labarin yamasa dadin dan tuni ya kira Anty Hajia yafesa mata itama tayi ta murna da ganin Nafi da'akai kasa zama tayi harde saida takwala kiran Anty Malika ta gaya nata itama ta taya su Aisha murna lokacin da khadija da Mubaraq sukaji kaman suyi tsuntsu suje gareta haka sukeji barin ma da Anty hajia tace musu harma da Abban ku yanzu haka suna tare kusan rudewa khadijan tayi jin an ambaci Abban su,Mubaraq da dama betashi yaji ko yaga wani Abban ba sai cewa yayi"Anty hajia dama idan an mutu ana zuwa ne?tambayar tasa taso basu dariya dukkansu amma de basuyin ba sai Anty hajia ce ta jawoshi jikin ta tana cewa"wayace maka idan mutum ya mutu yana zuwa?

Yaro sai cewa yayi"toh ai Anna kullum cemun take Abbamu ya rasu duk sanda akacemana mu shegune"Mubaraq Malik yakira sunan sa sauri juyowa yayi ya rungumesa yana masa oyoyo Uncle M Anna tasamo mana Abbanmu zaka kaini wajen sa,kuma sai nunawa duk ƴan Nguwanmu shi.

Tausayi maganan yaron yabasu wato tsawon shekarun nan sunyita ne cike da tsangoma mutane,wai meyasa mutane basa da tunanine kaddara takan iya faɗawa kan kowa sam wasu basu da hankali dama tunani baki ɗaya,ba wanda yake gujema kaddararsa idan kaga dan uwanka a wani hali idan kana da halin taimakonsa ka taimaka masa idan ko baka dashi yimasa fatan alhari wannan kawai ya wadatar amma yanzu dubi yaro ƙarami kaman Mubaraq ya taso da baƙin cikin tsangwama da ake musu yariƙe abun aransa dukda ba wai yasan me shege ke nufi ba.

***da dare Anty hajia tasami Aisha a ɗaki ita kaɗai zaune dama ta zaɓe wannan lokacin ne dan yaran suna can waje malamin su mai daura musu karatu al-qur'ani dama sauran litattafai na addini yaxo.

Da sallama ta shigo tana cewa"a'a Aishatul nabiyi zaune kike?murmushi Aisha tayi mata tana amsa mata sallaman da cewa"wallahi Anty hajia yanzu nake tunanin fitowa falo"a'a na hutashsheki kede ta fada mata cike da zolaya tana kaiwa zaune bakin gado saida ta riƙo hannun Aisha sannan ta kira sunan nata da Aisha"na'am Anty Aisha ta amsa mata jikinta yanayin sanyi da yanayin da Antyn takira sunan ta.

"Kibani aron hankalin ki taji tace da ita tana ƙatse mata tunani da yake neman daukan hankalin ta"kiyi hakuri Anty idan na ara miki hankalina dame zan sauraroki,ta kare maganan kanta a ƙasa.

"Hmmm Anty hajia ta sauke ajiyar zuciya to shikenan riƙe abunki nama fasa aron tace mata tana sakar mata murmushi ta daura da fadin wannan karon ba wani uzuri da zaki kawu na yarda na dauka dan haka ki shirya gobe zakije tare da Malika amiki komai na shiga makaranta.

"Makaranta kuma Anty ta tambaya cike da mamaki?

"Eh makaranta ta amsa mata kaitsaye wannan karon ba wani uzuri da zaki kawo a yanzu na karɓeta yana daga cikin dalilin dayasaka na matsa sai kindawo inaso kiyi karatu ta yanda zaki tsayu da kanki maza irin Ahmad ƴan boko sunason matarsu ta kasance ƴar boko yar uwansu koda wani abu ze taso wacce zata iya tashi ta tsaya tayi jawabi a cikin mutane.

Aisha ba wai na raina karantunki bane a'a sannan ban raina wayewarki ba,saide ance ko kanada kyau ka kara da wanka,na yaba da hankalin ki da nutsuwarki wannan dalili yasa nawa Ahmad sha'awar aurenki saide kashh,daukan da yama auren matsayin na wucin gadi yasa nakeso kiyi karatu ki goge yanda kina nan zaune da kansa ze bibiyeki da neman sulhu inaso yanuna miki soyayya mai suna soyayya ya janye kalmar wucin gadin nan da bakin sa.

Banason jin komai daga bakin ki wannan umurni nake baki ba shawara nazo nema gunki ba....

ALLAH YASA MUDACE

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 23 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

AUREN WUCIN GADI 2Where stories live. Discover now