EPISODE 9

5 0 0
                                    

♦️AL'AJABI♦️
DAGANI BABU TAMBAYA
   BY
REAL HAJARA YUSUF

Episode 9

Saida fati tayi kusan awa uku asume sannan ta farfado tana bude ido taganta akan gado sannan ga jibrin a gefenta yana kallonta, tayi saurin tashi da niyyar guduwa sai taji ya rikota, Rike hanunta da yayi saida taji kamar an zare ranta Dan tsoro da fargaba.

Jibrin yace fati menene? Meya sameki kike irin wannan tsoron? Kodai mafarkanda kikeyi cikin dare suke miki gizau. Meyasa zaki gudu kuma bayan gani awajenki.

Fati kam tashiga rudani dan zuwa yanzu tafara tunanin watakila gaskiya yake fada, amma sai wata zuciyar taki Aminta da hakan.

Fatee! Firgigit tayi danjin yadda yakira sunanta. Sannan tayi karfin halin cewa, Ni yaukam Bazan kwana a gidannan ba, jibrin yace Meya faru da zakice bazaki kwana a gidan ba.

Fati tayi saurin kallonsa cikin ido sannan tafara magana a fusace, Wato tambayata kake meya faru ko bayan duk abubuwanda naga sun faru, rikidewa kayifa kadawo wata iriyar halitta sannan kuwwa da gurnani yakarade ko ina a gidan ana wannan yanayin kayo kaina da gudu daganan bansan meka aikatamin ba, nadaisan na farfado naganka a gefena, Dan haka inma gizau ne inma gaskiya ne nidai nagaji da Rayuwa irin wannan yau a gidanmu zan kwana kawai sai tasa kuka mai ban tausayi tana fadin Wllh nayi dana sanin aurenka kuma nacuci kaina nacuci rahuwata.

Jibrin ne ya darkusa a gabanta ya ware tafukansa da niyyar ta daura nata akai amma taki, hakan yasa yamike ya tsaya sannan yajuya mata baya yafara magana kamar haka.

Fati kinsan ina sonki kema kina sona auren soyayya mukayi dajuna sannan yau kece da kanki kike jifana da munanan kalamai akan abunda Sam ba laifina bane.

Abunda yafaru shine, muna zaune muna hira kawai sai naga kin kurawa daki ido, daganan naga kinruga da gudu kika shige dakin kina ihu nikuma nabiki abaya ina tambayar ko kina lfy, amma ko saurarona bakyayi kawai sai naga kin fadi kasa sumammiya, ganin haka yasa nayi miki addu'a nayita shafa miki ruwa a fuska ina hura miki iska har kika dawo Hayyacinki. Ki yadda dani fati Bazan taba cutar dakeba kuma bazan miki karya ba wannan ne gaskiyar abunda yafaru ba kamar yadda kika fada dinba.

Fati Hawaye kawai take zubarwa cikeda tsananin dana sani kuma a ranta tasan wannan maganar ba gaskiya bane amma afili kuwa cewa tayi Nikam nashiga uku wannan wani kalan abune kaman Almara.

Jibrin yajuya yana kallonta sannan yace kiyi hkr fati watakila wata larurar ke damunki amma karki damu zamu shawo kan abun sannan idan na fita gobe zan dawo miki da magani.

Fati tace shikenan ba komai Allah yayi mana maganin matsaloli amma inada bukata guda daya wanda samunsa shine lasisin cigaba da zamana a gidanka.

Jibrin yace wacce bukata ce wannan?

Fati tace inaso a satinnan ka kaini garinku wajen iyayenka idan basa raye ko yan uwanka idan babu ko makotanku ka kaini wajensu, barema babu wani mahaluki dazaice shi shi kadaine a danginsa. Wannan itace bukatar tawa.

Jibrin mutuwar tsaye yayi yarasa me zaice, tuni ya lula duniyar tunani.

Bai ankare ba yaji fati tamatso kusa dashi tace wannan itace bukatar tawa Shin zan samu???

Jibrin saida yadau kusan dakika talatin sannan yace.....

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Onde histórias criam vida. Descubra agora