EPISODE 10

5 0 0
                                    

♦️AL'AJABI♦️
DAGANI BABU TAMBAYA
   BY
HAJARA YUSUF
_REAL HAJARA YUSUF_

Episode 10

Jibrin saida yadau kusan dakika talatin sannan yace kwarai zaki samu.

    A bangaren zainab kuwa jitake tamkar tahaka rami ta binne kanta idan ta tuno da Abunda Mal Zakiru yataba fada mata abaya, tayi kusan awa uku zaune awaje daya tana tunanin mafita, wata zuciyar kuma tafada mata kodai takoma wajen Mal Zakiru ne haka dai ta yanke shawarar fara zuwa gidansu fati. A take tadau mayafi zata fita kenan tajiyo muryan umma tana kiranta, furzar da iskan bakinta tayi ta nufi dakin umman
    Da sallama tashiga sannan tasamu waje tazauna gabanta sai faduwa yake tarasa dalili.

    Umma tace Zainab lafiya kalau kike kuwa naga kwana biyunnan duk kin birkice kinfita hayyacinki. Zainab tadanyi murmushi sannan tace bakomai umma lafiyata kalau kawai dai yanayin garinne da Babu kudi kuma ba wajen zuwa tana maganar ne kanta akasa hakan ya Kuma tabbatarwa umma cewa akwai matsala

    Umma tace dago kanki ki kalleni. Zainab daga kai tanayin ido hudu da umma tasake sauke kanta kasa, Gaban ummane ya yanke yafadi ganin zainab acikin wannan yanayin. Amma tayi karfin hali tace! Yaushe rabonki da ganin Al'adarki?
       Zainab tayi saurin daga kai tana kallon umma, sannan ta kyalkyale da dariya, sabida maganar umma yabata dariya sosai dukda damuwar datake ciki hakan bai hanata dariya ba.

    Ganin zainab na dariya yasa hankalin umma yadan kwanta itama cikin dariya tace tofa!! Yanzu maganar nawane abun dariya? Zainab tace aa wallahi ko daya, kawai dai gani nayi kamar na tsallake wannan stage din, dawayona da ilimina da dabarata da karfina amma a.....  Bata karasa maganar ba umma tace Dallah yimin shuru da zancennan.
        Zainab tamike tace to umma zanje duba umman fati, umma tace to kice ina gaisheta. Zainab tace to tasa kai tafice. Bayan ta shiga gidansu fati dakin kaka tafara shiga tasameta zaune akan darduma tana lazimi, kaka na ganin zainab tafara faraa tayi Addua ta shafe sannan tace maraba zainabu sannu da zuwa.
    Zainab tace yauwa kaka ina yini, kaka tace lafiya kalau Abu ya mamar taki, zainab tace lafiya lau tace a gaidake, kaka tace Ina Amsawa kindawo lafiya? Da mamaki zainab ta kalli kaka sannan tace dawowa daga ina kenan kaka?
    Kaka tace au nadauka tafiya kikayi ai shiyasa kikafi sati baki shigo gidannan ba, Zainab tace kai kaka zaki farako? Kaka tace dadina da lalacewar Zamani har gaskiya sai anhana mutum fada. Zainab tace aa yi hakuri kaka kwana biyunnan banajin dadine Shiyasa kikaji shuru.
    Kaka tace to yanzu ya jikin, zainab tace da sauki! To Allah yakara sauki zainabubu! Ameen kaka bari naje nagaida umma idan nadawo zan fada miki wata magana sai kibani shawara.
    Kaka tace ai nasan baa nemana saida dalili amma dukda haka ba zanyi fushi ba jeki kidawo zan baki shawara kuwa amma zaki biya kudi.
      Zainab tayi dariya sannan tace lalle kaka to wannan ba sabon abu bane, tsohon magana ne wanda ba wanda yasan dashi sai ni dake da fati sai kuma Allah. To shine yanzufa zamu dawo da hannun agogo baya.
     Kaka tace ikon Allah! To yimaza ki gaidata kidawo mu tattauna. Zainab tace tare da ita zaayi wannan tattaunawar sabida girman Al'amarin.
     Zainab tana fadin haka tamike ta nufi dakin umma bayan sun gama gaisawane zainab tace mama akwai maganar da akeso ayishi a dakin kaka dan Allah kibiyoni muje can wallahi babban Al'amarine.
     Umma batayi wani musu ba ta tashi tayi gaba zainab nabiye da ita abaya har suka isa zuwaga dakin kaka. Bayan an zazzauna waje yayi shuru sannan zainab tayi gyaran murya tafara magana

      Idan Baku manta ba akwai sanda muggan magarkai da firgici suke damun fati, kaka da mama sukace kwarai anyi haka
    Zainab taci gaba da cewa to awancan lokacin da ai anyi magani kala kala baa daceba, kuma ko tayi sauki na kwana biyu abun zai sake dawowa. Shine Babar wata kawarmu a makaranta tafada mana muje gidan Mal Zakiru zamu samu biyan bukata kaka tace ay anyi haka wannan wanda yace zai muku magani amma sai anmai bakin bunsuru da bakin agwagwa dinko? Zainab tace mutuminnan ya fada mana maganganu da dama amma jin yace mukawo bunsuru da agwagwa yasa mukayi masa rashin kunya muka tashi muka tafi.
    Muna tafiya ya aika mana Almajirinsa agaya mana zamuyi dana sani kuma Babu inda zamuje musamu magani idan ba wajensa ba, sannan nan gaba idan mundwo korar kare zai mana bazai taba yarda ya bamu magani ba. *Innalillahi wa inna ilaihirajiuun* shine abunda mama ke cewa kaka tace to fada mana menene shi Mallam Zakirun yace.

Saida zainab tagyara zama tayi gyaran murya tafara magana kamar haka....

♦️AL'AJABI♦️ (DAGANI BABU TAMBAYA) Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu