Chapter 5

27 0 2
                                    

9️⃣----🔟

Sa'eeda mutuwar tsaye tayi tun daga shigowa gidan da kuma farajin masifar Gwaggo Ladi ta tafi nisan zango a ranta tana cewa 'Wai yaushe zamuyi masoya a duniya, kowa bai son mu,Toh meyasa ta ce Ummina batada asali, daman ba ita bace kakata, toh wacece kakata, kenan Gwaggo Ladi ba ita bace ta haifi Ummina ba'.
Haka taita karatun zuci daga ƙarshe ta dauki kayansu zuwa inda Baba ya umurcesu, ɗaki ne ɗan ƙarami da ƴar katifa itama ƙarama wacca batafi ta kwanciyar mutane biyu ba, sai labulen ƙofa da na window, ɗakin ba laifi a gyare yake kamar ansan da zuwansu.
Ciki ta iske Ummanta a zaune akan katifar tayi tagumi, da sauri Sa'eeda ta ajiye kayan hannunta ta nufi gun Ummanta don arayuwarta bata ƙaunar ganin damuwa a fuskar Umman nata, haka da sassarfa ta isa gunta tare da cewa " Ummina don ALLAH kidena tagumi, Banaso please kidaina "
Sai kuma ta fashe da kuka,har da shashsheka, don ita ta rasa wannan baƙin jinin da suke dashi, kowa baya sonsu, ko a makaranta haka ta ke fuskantar tsana da tsangwama daga ƴan ajinsu, wurin Maryam kaɗai ne ta ke samun sassauci.
Ummanta ne riƙo haɓarta tare da girgiza maka kai alamun tayi shiru duk da itama kanta hawayan ne suke kwaranya a bisa kuncinta tare da cewa " Duk wani ƙunci da tsanani maganinsa yana ga UBANGIJI ne, haƙuri da juriya suna kai mutum mataki babba arayuwa, kasancewarmu a wannan yanayi baya nuni akan dawwamarmu cikinsa, don haka mu cigaba da haƙuri tare da juriya wataran sai labarin kinji sanyin idanuwa na"
Sa'eeda da tunda Ummanta ta fara magana ta ke shashshekar kuka ɗan ɗaga mata kai tayi tare da tambayarta alokaci guda " Ummina meyasa Gwaggo Ladi ta kiraki da mara asali?
Tirƙashi lokaci guda yanayin Umman Sa'eeda ya sauya ita a tunaninta Sa'eeda bataji surutan Gwaggo Ladi ba, saida ta ɗan sauke nauyayyan ajiyar zuciya kafin ta fara magana "Banso kika ji zantuttukan Gwaggo Ladi ba, hasalima shiyasa tun kina ƙarama rabona da zuwa garin nan saboda banason hankalinki ya tashi,nabar hakan ya zamo sirri agareni ba tare dana sanar miki ba, amma tunda allura ta tono garma, kibari anjuma da daddare bayan munyi sallar Isha'i sai na baki tarihina kamar yanda nima mamata ta sanar min, kinji"
Sa'eeda da ke kallon Ummanta ta amsa da "Toh, ashe nima inada kaka"
Murmushi Umman Sa'eeda tayi ganin wauta da shirme irin na Sa'eeda tare da cewa "Daman ance miki babu wanda baida kakane, kema taki ALLAH Yayi mata rasuwa ne"
Ɗan lunshe sexy eyes ɗinta Sa'eeda tayi sannan ta ce " Allah ya kai haske a ƙabarinki kakata da na al'ummar musulmai baki ɗaya"
da "Ameeeeeen", Umman Sa'eeda ta bita dashi, kana suka cigaba har hirarsu.

@@@@@@@@@@@@@@

Kamar yanda Baba ya faɗa za'a girko musu abinci hakan ta kasance, don ɗan saƙon da aka aika gidan Mairi yana sanar ma ta fara murna saboda duk acikin ƴaƴan Gwaggo Ladi tafi kowa sonta tare da mahaifiyarta kafin ta rasu.
Habawa ai da ɗan aiken ya sanar mata, daman tana kiyon zabbi , kaji da awakai, sai tasa a yanka mata zabbi guda biyu, bayan an yanka mata su, tayi zaman gyaransu ita da ƴarta mai kimanin shekara 14 dayake bata haihu da wuri ba,sannan ta ɗora sanwan girki, tayi musu tuwon dawa da miyar kuka wacca tasha manshanu haɗe da naman zabbi duk da ba duka tayi miyar dasu ba, ta soya sauran tasa alanga haɗe da na tuwon da miyar, nan fa ta aiki ƴarta ta dashi a babban kwando.

@@@@@@@@@@@@@

Da sallama ɗiyar Mairi ta shiga gidan, sai tayi sa'a Gwaggo Ladi na ɗaki kasancewar lokacin azahar ne, sai ta wuce ɗakin baƙi dayake mamanta ta faɗa mata inda baƙin suke.
Sallama tayi a lokacin Sa'eeda ta zagaya bayi ita kuma Umman Sa'eeda ta kammala sallah tana zaune,jin anyi sallama yasata amsawa tare da cewa"A shigo"
yarinyar ce ta shigo tare da russunawa ta gaisheta, Umman Sa'eeda cike da fara'a ta ke amsa mata ganin kamannin ƴar uwarta ta kuma masoyiyarta wacca bata da kamarta, cike da ladabi yarinyar ta ce"Mamata ta ce gashi in kawo muku kuma tana muku sannu da zuwa, gobe bayan sallar Idi tana nan zuwa "
faɗaɗa murmushinta tayi da faɗin" ALLAH ya kaimu, kice mata ina godiya sosai, sannan tsarabarta na nan saita zo"
yarinyar tace "Toh".

Yarinyar na tafiya Sa'eeda ta shigo ɗakin,tare da zama suka fara cin abinci, duk da yau ake hawan Arfa, Sa'eeda na period ita kuma Umman Sa'eeda na fama da chronic ulcer kuma yanxu an ɗorata akan magani shi ya hanata ɗaukar azumin Arfa. Haka suka kammala cin abincinsu tare da hamdala sannan kowa ya sami wuri don warware gajiyar tafiya.

NACINA YA JAWO MINWhere stories live. Discover now