TURHAN POV.
“Shikenan zan jiraka a waje”
Ya aje wayar ya nufi gurin da suitcase dinsa yake ya bude ya ciro wani karamin roll on ya murza a wuyan hannunsa sannan ya aje a mirror dake dakin ya sake nufar wayarsa ya dauka ya saka aljihu ya dauki key din dakin ya fice ya rufe dakin.
Stairs ya bi har ya sauko daga hawa na uku zuwa na daya, kamin ya karaso kasa ransa ya gama baci domin Turhan ba mutum ne mai son motsa jiki ba sai dole, ko kadan baya son aikin wahala balle kuma wahalar ita kanta da baya hada hanya da ita.Harabar hotel din ya fito yana kallon yadda tsari da kawar babbar hotel din take daga kasa, domin sun sauka sa dare ne a jiya, gajiya bata bashi dama kamar yadda hutu ya bashi a yau da safe ya kalli ko'ina ba. Kusa da wata flower ya tsaya yana kallon ko'ina da kyau, kyam idonsa suka sauka akan wata hallita mai ban tsoro, mutum ne irinsa namiji mai kirar mazaje da jarumtaka, Turhan ya dauke idonsa daga kallon mutumen da shi ma kallonsa yake babu kyabta ido. Ganin sarkar Cross a wuyan mutumen da murdaddiya fuska irin na wanda baya sha'awar dariya, ya saka shi fahimtar addininshi da nasa akwai banbanci, tattoo jikinsa ma ya sanar da hakan.
Feeling awkward ya saka shi ciro wayar dake aljihunsa ya fara dannawa, ya dauki lokaci a haka kamin ya sake dagowa ya kalli harabar, a karo na biyu ya sake kallon gurin da mutumen dazun yake tsaye yana kallonsa and wannan karon ma yana tsaye and still kallonsa yake har yanzu, irin kallon nan mai daure kai ga wanda ake yi ma shi, da mace ce take kallonsa sai yace ko tana sonsa ne, amman namiji kamar wannan da zai yi wahala su hada hanya da imani abun tambaya ne a kallon da yake masa, zuciyarsa ta raya masa wata kila yayi masa kama da wani ne da ya sani ne, idan ba haka ba kallon da yake masa yayi yawa, and babu wani dalili da zai saka yayi ta kallonsa haka.
Kallo ne mai rikitarwa da mamaki ga wanda ake yi ma shi, hakan ya saka Turhan jin babu dadi kuma ya dan tsorata, ganin ba garinsu ba ne, haka kuma ba gurin da ya saba mutanen ba ne, ko be taba zuwa ba, ya kan ji ana fadar bad side na Lagos, dan haka dole ne yayi taka tsantsan. Takawa ya fara yi cike da izza da takamar da suke zame masa jini ya isa gate din hotel din hannayensa rumgume a bayansa sai kamshi yake zubawa tafiyarma ita kanta ta karbe shi kana ganinsa kasan babban mutum ne kuma dan babban gida.
Sai da ya fice daga katon gate din dake bude sannan ya juyo kadan ya kalli mutumen dazun domin jikinsa ya ba shi har lokacin yana kallonsa, ga mamakinsa sai ya ga mutunen yana kallonsa har yanxu, kusan kallon yanxu yafi muni fiye da na dazun, domin a yanzu yana iya hango tsana da harzuka a idanuwan mutumen da be san waye ba, be kuma san dalilin haka ba.
Wannan karon Turhan be tsaya shawarta zuciyarsa ya daga wayarsa ya kira Faruk.“Wai baka karaso ba har yanzu? I'm not safe here fa, ina jin tsoron irin mutanen da suke a nan gaskiya”
“Gani isowa ranka ya dade, na kusa karasowa, ka kwanta da hankalinka babu komai In Shaa Allahu, Hotel din da ka sauka hotel ce mai tsaro sosai, ba wani matsala In Shaa Allahu, da akwai matsala ai oga Aliyu ba zai bari na sauke ka a wannan hotel din ba”
“Ina fatan haka”
Ya fada sannan ya sauke wayar tare da jan dogon numfashi, wannan karon be yarda ya sake juyawa ya kalli bayansa ba, balle ya san da wanzuwar mutunen dazun ko akasin haka, sai ya cigaba da tafiyarsa. Kamin ya sake daga wayar ya kira farar uwar data kawo shi duniya. Ringing daya biyu ta daga, daman bata ignoring call dinsa idan tana kusa da waya, tun a lokacin da suke shiri da juna da kuma yanzu da ta sauya mu'amala da shi, banbancin wacan kiran da kuma yanzu, idan ya kira bata kusa bata mayar masa da kiran, kamar yadda ba zata amsa kira da saukin kiransa ba, ba kamar can farko ba da take daukin kiransa da far'a da na jindadi kuma yake kiransa idan ta samu miss calls dinsa, a yanzu sai dai ta amsa masa duk abun da zai fada ne ba a cikin dadin rai ba.

YOU ARE READING
ABOKIN RAYUWA
Mystery / ThrillerA iyakar sani, kasuwanci ake wa siye da siyarwa. To ita wannan kaddara ta yi safararta tun daga Nijeriya har kasar Sudan, a can ta cike gurbin wata rayuwar da aka rasa ne, a wata masarautar mai ban tsoro, da ba a daga ido a kalli Sarki da mukarraban...