Cast

3.7K 239 49
                                    
AYSHATUUU (Emily)

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

AYSHATUUU (Emily)

AYSHATUUU (Emily)

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Hamza Ali

Aliyu Mudallab

KAMILA Tukur.

Vito (King)

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Vito (King)

Turhan Mohamed Abdo

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

Turhan Mohamed Abdo. (The Prince Of Sudan )

DOCTOR, ADAM BELLO  (Dr A-B)

TSAKURE.

'Akwai matukar zafi, da bacin rai a auren mutumen da baka so, akwai da ci a auren mutumen da aka cilasta masa aurenka, akwai tsananin bakinciki da nadama a auren mutumen da yana so ba ka son shi...!
Yawancin irin waɗannan aurarraki sakamakonsu nadama ne, da dana sani, wanda kan iya haddasa ciwon zuciya da kan iya silar ajali mai shi.
Amman ina makomar auren da aka gina akan soyayya? Miye tukuicin kyakkyawar alaka da kaunar da aka gina aure da ita? Shin minene ribarta?'
Soyayyah ruwan zuma! Haka na ke jin sunanta a bakinsu, haka na ke kallonta a finafina da littafai. Hakan yasa ni shiga dakinta. Da fari tai min marhabun tare da yi min shimfida mai laushi, sai da na mika duka karfina na kwanta a ciki sai ta shammace ni, ban sani ba ashe a saman kaya da kusoshi tawa soyayar tai min shifidar, tai min matashin kai a saman narkaken garwashin wuta, daga lokacin sai na soma kiranta da dayan sunanta, wato soyayya ruwan guba! Ruwan daya fi ko wane ruwa haɗari a duniya, ruwan ta kan aika mai yinta a lahira nan take ta, ruwan da wanda ya dandana ta zai gwammace mutuwa da rayuwa...'

Hannuna na hagu na kai na share hawayen idona, ba tare da na samu amsar tambayoyin da kullum na ke yi ma kaina ba.

"Akwai matukar zafi, akwai ciwo..."

Na fada ina shafa sarkar cross din dake hannuna na dama, cikin sautin da ke nuna alamar kuka nake rerawa da sautin da babu wanda zai ji ni sai ni kaina.

'Tabbas akwai ciwo a rayuwar da baka san karshenta ba, akwai ciwo a rabuwa da mace da ta zame maka uwa, akwai ciwo a barin addinin da shi yake maka gata, akwai ciwo a shiga addinin da masu shi basa maraba da kai, akwai ciwo a karbar soyayyar mutumen da be san me ake kira da so ba, akwai ciwo a auren mutumen da ba san darajarka ba, akwai ciwo a zaman auren da babu natsuwa da kwanciyar hankali a ciki.
Na zabe shi cikin dari, ya wulakanta ni cikin dubu, na kunyata Momy saboda shi, ya kunyata ni saboda rashin dalili, na bar adinina na shiga nashi ya nuna min rashin gata a addininsa, da ruwan jini da alkalamin zinari na rubuta sunansa a tsakiyar hatimin zuciyata, shi kuma ya rubuta sunana a jikin dutse da bakin gawayin da ruwa zai iya gogewa'

"Shin wane irin miji na ke aure ne?"

Wannan karon a fili nai tambayar cikin kuka, muryarta na amsa amon a duka fadin dakin, sai kuma na fashe da wani matsanaicin kuka...💔

Coming soon...😍❤
Are you guys ready...?

ABOKIN RAYUWA Where stories live. Discover now