11

1.6K 109 0
                                    

11. Alhaji muhammed galadima haifafen dan billiri sannan dan billiri wanda ya ajiye iyalansa acikin garin. Yanada mata fatyma wanda akafi sani da hajiya babba. Ita yar garin dukku ce. Wanda sukahadu tun kuruciya sukayi aure . Mata mai cikar kamala wato wacce afrah tazauna agunta. Haihuwanta bakwai anma basu rayuwa.  Biyune suka rayu. Wato usman. Yaya babba kenan. Saidan autanta Ahmed. Hakan yasa dakyar galadiman yakara aure da aisha inda ta zube yaya uku  duka mata itakuma. .anacemata anty amarya. Farkor yarta salamatu wacce akamata aure da dan sarkin  dukku tahaihu anma Allah yayi wa yar rasuwa.don ko ganin yar batayiba. Saikuma hafsat itama tayi aure da yayanta biyu acikin garin gombe. Yar autarta hussiena itace batayi aureba tana zama agun salamatu tana karatunta.  Gydane na mutunci da kamala. Kowa yasan mutuncin juna. Ga su da farin jini duk inda suka shiga. Abun hannunsu bai tsole musu idoba. . Zurian galadima kenan!.<br />
Afrah bayan karyawa tafito inda tagayshe da  babban yaya da anty amina. Inda babban yayan yace afrah tunda kin iya girki zakinayi . Akwai masu hidima afrahn tace to. Tamike tanufi kitchen inda tahadu da abu mai aiki yanata wanke wanke suka gaysa tafara hada abun girki shima yaci gaba da hidimansa.<br />
Fitan yaya babba yasa amina ta kwala mata kira tana zuwa takalleta sama da kasa. Tace ke kin tabbata ke kanwar sa ce?. Afrah tayi xuru xuru da ido kafin ta amsa sai aminan tace bar kallona da manyan idonki irina galadima. Ku zurianku kowa da manyan ido. Afrah dai tana shiru can tace kitashi kije kigyra min kan gado kigyramin wardrobe. Sannan kije dakin yaya babban shima ki gyra ki wanke bayan gydan ki kimtsa. Sannan ahmed bayanan inyadawo shima zakina mishi inya amince don miskilin gaskene. Tamike tafice. Afrah taja dogon numfashi. Angudu baa tsiraba

KECE GUDALLIYA (2013)Where stories live. Discover now