NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani) Babi na Shida

189 8 0
                                    

🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔

          *NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄

*January 2017*
6⃣

Kallonta kawai Sadi yakeyi yarasa ta inda zaifara warware mata bakin, zaren kansa ya sinna kasa yafara magana
"NASREEN tabbas Dan uwanki baiyi karya ba duk abunda yasanar dake haka yake".
lokaci guda ta zaro ido kamar na gurjiya tace "Inhar mafarki nake yaci ace na farfado, amma Sadi maiyasa ka boyemun baka sanar Dani tuntuni ba kuka takeyi mai sauti.

"Nasreen kece baki bukaci ki sani ba amma tunda gashi yau dakika bukaci ki sani ai gashi na sanar dake, kuka takeyi lokaci guda yaji wani ciwo cikin zuciyanshi,
"Nasreen kidaina irin wannan kukan yana tadamun da hankali, ai kamar yace Nasreen kara sautin kukanki, amma Nasreen inhar abunda yayanki ya fadi gaskiya ne toh yau kisani, tun ranar da kika bukaci soyayyata Nasreen na daina duk wani Abu dakika sani, sanadiyyan ki na tuba daga duk wani miyagun halayena".

Nasreen ta kalleshi, tace Amma...........sai kuma tayi shuru  Sadi ya kara da cewa
"kinji iya Gaskiyan Dana gaya miki amma inaso kamar yadda kikace nayi miki Alfarma lokacin dakika rubuto mun wasika, toh nima Alfarmar nakeso kiyimun ki aureni".

Kallonsa kawai takeyi don Sadi har yanzu baikai ayaba
"Nasreen sonki yashiga cikin zuciyana ya Daskare tabbas in za'a cireshi sai an fasa kwalban, sonki kuma kamar jini ne daya shiga cikin sassan jikina ya gaurare, rabuwa dake babban illah ne a gareni, Nasreen ki amince na zama ke yadda kema Nasan burinki kenan inzama ke".

A hankali Nasreen ta waiwayo, ta kai dubanta gareshi "tabbas Sadi ya iya kalaman so sannan yanada tattausan lafazi wacce kowacce mace take burin samu"
Kukan take har yanzu amma taci alwashin bazata rabuda Sadi ba don shine annurin zuciyanta mai yaye mata damuwa.

"Nasreen kice kina sona Wallahi tallahi kinji Allah daya namiki Alkawarin daina duk wani Abu kuma insha Allah saikin saneni namiji mai alkawari, Nasreen karki bari Salman ya ruguza mana soyayya don yin hakan komai na iya faruwa kina iya rasani, a yadda sonki yayi rassa cikin birnin zuciyana".

Nasreen ta dago kanta data binna a kasa, tace "Ina sonka masoyina banida kamarka a fadin duniyar masoya fatana shine ka rike Alkawari kaxama mutumin Kwarai, Amma kasani duk randa na kamaka da wani laifi kasani koda aure mukayi toh abakin aurenka",
Sadi ya zare ido yace "Nasreen kina nufin zaki iya rabuwa dani kenan?
Nasreen tace
"Kwarai inhar nakama ka da wani laifi ba".

Tashi tayi "Ni zan tafi amma inaso dakai karka daina zuwa gidanmu, abunda kakeyi karka fasa aure dani dakai ba fashi koda hakan zaiyi sanadiyyan rasa rainane."

Sadi yaji dadi har bakin mota ya rakata ya mika mata handkerchief
"Gimbiya sarautar mata gashi ki goge fuskanki, insha Allah inanan zuwa anjima inna tashi daga aiki"
Nasreen tace
"Danaji Dadi kam kagayamun, mekakeso in dafama Wanda ranka yakeso? "Kema kinsan abunda nafiso Dan'wake".

Dariya Suka kwashe dashi, daga bisani ta tada motar tafe take harta fita sadi yana daga mata hannu.
Bakin aikinsa ya koma amma gaba daya Mamakin Salman yakeyi, Ashe abota takan zama kiyayya? Ji yadda sadi ya nuna cewa baitaba sanina ba amma babu komai Allah yafishi.

DORAYI
        Nasreen ce tayi horn lokaci guda, mai gadi ya wangale mata Gate cikin gida tashiga,tayi packing mota a wajen aje motoci, fitowa tayi ta gaida mai gadi tace zanyi bako anjima inyazo ka bude mai gate yashigo kaji,
"Toh hajiya"
Juyowan dazatayi taci karo da Salman yar kallon kallo kawai sukeyi,
Wucewa Nasreen tazo yi Salman yace "ke dawonan"
Bamusu ta dawo  "Gani" Nasreen tace.

"Daga ina kike"? Cikin rashin fahimta tace, " Yaya ban gane daga ina nakeba, dacan inzan fita kai nake gayawa koh Ammi? Inso kake kaji daga inda nake toh naje Wajen SADI ne don in tabbatar da abunda kake gayamun akanshi shin Gaskiya ne koh akasin haka? Shikenan nina gaji inaso inshiga ciki in huta koh dakwai sauran magana ne?".

Salman yabita da kallo, daga bisani hartakai kofa zata shiga yace "Wane bako kike cewa abudemai gate idan yazo?"
Nasreen tace "A gaskiya yaya yawan tambayane banaso saikace wani Dan jarida, inkanaso kaga kowaye inka fita ka dawo da wuri."

Ciki tashiga tabarshi tsaye, koh dai Sadi ya fadawa Nasreen cewa halinmu daya dashine? Inyayimun haka bai kyautamun ba ga yarinya tana Neman ta rainani!!!!
Motarsa ya dauka yafita.
Ammi! Ammi
Laure ce tafito tace batanan tafita taje gidan hajiya murja amma tace bazata Dade ba,
Har zata wuce tace "Laure inaso kiyimun Dan wake nagani na fade, zanyi bako zuwa anjima dafatan ban takura miki ba?"
"Ah ah hajiya".

Ciki tashiga ta huta tayi wanka, dinning room tashiga tafara da breakfast din dabatayi ba, sannan ta shiga ta tsantsara kwalliya, wayarta taji tana ringing cikin kosawa ta dauka Sadi ne, ta daga wayan jitayi mace tana magana shuru tayi kafin tace lafiya kika kirani?
"Eh lafiyarace ta kawo haka inaso ki sani Sadi nawane ba nakiba don haka kifita daga harkansa inba hakaba ranki inyayi dubu saiya baci banza karya".

"Guda Nasreen tayi tace, kece karya yar bariki kawai, wallahi indai akan sadi ne bazaki taba bani tsoroba, bakisan cewa afagen son Sadi ni jaruma bace toh bari kiji ki Adana kalamanki kila suyi miki amfani wata rana kuma kece karya wacce ke fada akan namiji inkin isa ki nuna kanki mana" mtwww tsaki taja ta kashe wayar tasa lambarta a bakin feji.

Bata Dade da gama wayarba saiga, Sadi kanshi tsaye ya shigo sallama yayi yaga Nasreen zaune ta zabga uban tagumi!!! Cikin sauri ya isa gabanta ya tsugunna, yace
"Lafya Gimbiya kika yi tagumi mekikeso me kika nema kika rasa?
Dagowa tayi tace, "Babu komai amma inaji ajikina cewa zan rasaka wayarta ta mikamai, duba yanzu wata lamba ta kirani wai in rabu dakai wai, kai natane".

Yana dabawa yace beti????? Nasreen ta matso kusa dashi tace kasan tane? Ina Sadi yatafi cikin kogin dukiyar fulanin Nasreen, ga wani kamshi daya doki ilahirin duniyar hancinsa,
Nasreen tace
"kayi shuru"
Sai a lokacin yasan cewa magana take tashi yayi yace
"Kwarai farin sani budurwatace ada ba'a yanzuba, da tare muke agida daya sanadiyyanki na koreta, inajin shine zasu hada bakida ita don su ruguza alakata dake Toh karyane yafadi da karfi".
Nasreen tace
"suwaye"?
Sadi yace
"salman mana kuma saina Shayar dasu ruwan mamaki dagashi har Beti," fuuuuuu bai jira tace komaiba ya fita, Motarsa yadauka yayi horn kenan Salman yana horn mai gadi ya bude Gate, Sadi ya kutsa hancin Motarsa shima Salman ya kutso tashi saura kiris su buga juna,
Fitowa Salman yayi ya cire tabaran dake makale a idonsa, shiko Sadi koh motsi baiyiba bare ya fito daga cikin motarsa zuciyanshi kawai tafarfasa takeyi.

*©ZAZZAU*😍😘

NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)Where stories live. Discover now