NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani) Babi Na Bakwai

178 8 0
                                    

🤔 *NEESMA'A WAH NUSHUUF*
(Maji Ma Gani)🤔

          *NA*
*HUMAIRAH BASHIR MELODY*👄

*January 2017*
7⃣

    Don komai yana iya faruwa, Salman ne tsaye yake knocking kofar motar Sadi, inka tanka mai karatu toh sadi ya tanka koh glass din yaki ya bude, bare ya saurari Salman don yana ganin zai iya shake Salman ya kashe shi don haushi.
"Sadi ka bude kafito ubanme ya kawoka gidanmu? Banyima iyaka da gidannan ba? Toh koh yau saina koya maka hankali".

Koda wasa Sadi baiyi niyyan tanka wa Salman ba amma yaxama dole yafito ya koyawa Salman hankali, Fitowa yayi ya Tsaya jikin Motarsa yana huci yana k'allon Salman, itak'o Nasreen tuni tafito tsaye take takasa motsawa ikon Allah takeso ta gani shin mezai faru tsakanin Sadi da Salman.?
Nimadai Humairah tsayawa nayi inga ruwan gudun Salman.

"Banace karka sake shigowa cikin gidan nan ba? Me akeda Dan iska irinka? Mara amfani a doron kasa?
Sadi ya bude baki yace
"Marasa amfani dai zakace, abunda yayika ada Salman shiya yini in tonon asiri kakeso inyima toh wallahi a shirye nake da inyima shi, kuma gida da kake cewa indaina zuwa matuk'ar NASREEN tana gidannan toh wallahi saidai ka hadiyi rai ka mutu, don bazan fasa zuwa ba.

Sannan ina umurtanka daka dauke akwalar motarka kafin insa a matsarmun da ita in wuce, inje ingama da waccan yar iskar Beti wacce kabata lambar Nasreen tak'irata donta batani a wajenta, toh sainayi maganinku daduk wani munafik'i dak'e bayan ayimun zagon kasa"
Wani kukan kura Salman yayi ya shake Sadi
"Nida kanwata harka isa ince Abu kace ba hakaba? Karya kake Dan matsiyata Mara Sanin kimar mutane banza mayaudari".

Sadi daya kasa jurewa, kalaman Salman ya fara dukansa, yana kai mishi naushi da dukkan karfinsa Nasreen dai takasa ce dasu komai mai gadine yafito yake musu magana amma ina dambe sukeyi na kece raini,
Bayan anyi nasaran rabasune Sadi yafita yasamo matasa majiya k'arfi yace Ku d'auk'emum motarnan kachok'an daganan in wuce haka koh akayi, dazai shiga mota yace "Aure danida Nasreen ba fashi, kuma inka fasa hanawa Allah yafika" ya tofawa Salman daskararren miyan bakinsa.

Salman yana tashi yabi Nasreen da gudu yadinga dukanta har saida yaga bata motsi sannan yabarta, Laure koh mezatayi banda ihu da salati, waya ta dauka tak'ira Ammi ta sanarda ita wainar da ak'e toyawa, cikin sauri saiga Ammi tadawo tareda direba, basu Tsaya wata wataba Sai international hospital, Gado ak'a bata sai wani nishi tak'e dai dai alaman taki jiki.

Ammi tace akan wani hujja ne Salman zai Daki Nasreen haka harta fita hayyacinta,? Laure takema wannan tambayar, Laure tace
"Ammi inajin sabani suka samu da abokinsa akan Nasreen don sunyi dambe sosai har saida mai gadi ya rabasu".

Ammi tace
"Dambe? Lallai abun ya girma, kardai ace saboda Sadi yace yanason NASREEN?"
Laure tayi saurin cewa
"Kwarai uwar dakina kamar kina wajen wai salman yace sadi karya sake zuwa gida shikuma yazo shine fada ta kaure",
Likitane ya fito yace "tafarfado kuma tace gida tak'eso taje, Ammi jiki na rawa tace
"likita babu abunda yake mata ciwo? Ya amsa da eh saidai ga wasu magunguna Wanda zasusa ciwon dataji su warke kumburin ya sace",
Ammi tace
"mun gode likita"
Cikin mota akasa Nasreen sai kuka takeyi,
"Ammi Dan Allah kice da yaya yayi hakuri ya barni da abunda nakeso Ammi wallahi inasonsa, sona hakika Ammi idan aka rabani da Sadi Ammi Zan iya rasa raina".

Tuni hankalin Ammi ya tashi tace  "Daman saboda sadi ne Salman ya dakeki? Toh koyanaso kobayaso aure da sadi ba fashi yaro mai mutunci Dan kirki, nikam meye aibun sadi? Ai Alhaji zai dawo za'ayi komai a gama share hawayenki yar Ammi kukanki ya kare kuma duk ranarda ya sake dukanki saina cimasa mutunci.

*DORAYI*
Cikin gida suka shiga, saiga salman zaifita Ammi tace
"Baba Karami har kanada damar dazaka ganni ka wuce baka gaidani ba,? Tabbas da'ace Sadi ne da tuni ya tsugunna ya kwashi gaisuwa amma har kakeda bakin cewa wai mama karama bata dace dashi ba? Toh k'aryarka Mara kunya kawai ka kama mun ya' ka daka ga jaka na haifama toh wallahi ka kula dakyau, waye besan abunda kakeyi ba? Haba Baba karami mexaka boyemun kana nufin in haifeka ka fini wayo? Toh ina maka kashedi tun wuri kasakarwa mama karama Mara tayi fitsari in gidanka ne ka hana sadi zuwa gidannan".

Salman yakasa motsi bare yace wani Abu, Ammi kuwa Jan Nasreen tayi suka shiga ciki, tuni aka hada ruwan zafi akayi mata kashin fuska da jiki, baccine mai nauyi ya kwashe ta bata farkaba sai gabanin magriba, tashi tayi cikin gaggawa ta gabatar da sallolinta, data makara batayiba, tana zaune aka kira magriba ta tashi tayi indai ibadane batada wasa saboda irin tarbiyan data samu daga wajen Ammi.

Karar wayarta taji, amma dayake Adu'a take saibata koh kalli wayarba,
( *Yanmata Mu kula wata koh raka'an karshe take saita, katse sallan ta dauki waya kamar yafi Ibadan datake*).
Bayan ta kammala ne, ta dauki wayan taduba Sadi ne cikin zumudi takirashi, "hello inayini hasken idanuna? Dafatan ka wuni lafya Dan Allah kayi hakuri da abunda yaya yayimaka dazu kaga nima yanzu muka dawo daga asibiti,
Dukana yayi har naji ciwo"
Nasreen kenan babu abunda yamun, abokinane fah duk abunda yamun Nasan dukda rashin fahimta ne amma ina fatan ya gane abunda nake nufi, nan gaba



*©ZAZZAU*😍😘

NEESMA'A WAH NUSHUUF (Maji Ma Gani)Where stories live. Discover now