Babi Na Sha Hudu

1.7K 160 35
                                    

Assalamu alaikum and a very good afternoon to you all.

Daga yau zuwa updates biyu  masu zuwa za mu saurari labari ne.

Shiyasa za mu dan dakata da wurin da ta zauna ba da labarin

Ina son na sanar cewar tarihi ya kunshi labarin abubuwa da yawa, farin ciki, bakin ciki da kuma rashi.

Amma fa zan fada tun wuri, akwai ban tausayi da tarin kunci. Rayuwa ke nan, dole sai da wadan nan.


Suna na Hindatu , wacce kowa ya fi sani da Hindu. Labarina ba zai cika ba, har sai na fara da mutumin da ya fi muhimmanci a cikin sa, wato Baba Alhaji.

Cikakken sunan sa Muhammadu Umar. Mutum ne mai dimbin dukiya da arziki da kuma yawan jama’a. Ya na daya daga cikin ma su juyawa da damawa cikin al’amuran al’ummar da yake zaune a cikin ta.

A garin Pankshin ya zauna, wanda ya kasance garin kabilar Angasawa ne, kuma yawancin su ba musulmai bane. Hakan bai taba hana shi hulda da su ba, tun da tun ya na tasowar kuriciyar sa ya yi hulda da maguzawa a nan arewa da kuma wasu kabilu da ke kudancin kasar nan.

Baba Alhaji, mutum ne mai son taimakon mutane, ba tare da la’akari da addini ko yare ba. Hasali ma ya fi duba cancanta da kwazo, tun da tun fil azal a kan hakan ya gina rayuwar sa.

Mutumin Dutsin Ma ne da ke Katsina, wurin da ya yi rayuwar shekarun sa na kuruciya. A can Mamman kowa ya san shi. Mahaifin sa Alhaji Umaru Sanda manomi ne tukuru, wanda ya yi nomar auduga a zamanin turawan mulkin mallaka. Da kasuwar auduga ta fadi, ya koma yin na gyada da wake. Ya kan noma fiye da buhunhuna dari uku a damina daya.

A lokacin da yayi tashen arzikin sa, ya auri mata uku, biyu daga Dutsin Ma, amaryar sa kuma daga Funtua mai suna Delu. Biyun farkon, Audi da Asabe suka hade kan su wa Delu, saboda bayan ba daga garin su ta fito ba, yarinya ce shaar gau a leda.

Wasu daga cikin manyan ‘ya’yan sa ma za su haifi mai yawan shekarun ta, wato sha uku. Lokacin da ta shiga gidan su Asabe sun bar haihuwa. Saboda haka ita ce kadai ke yi. Maimakon su rike ta cikin amana, babu kunya suka zake suna kishi da sa’ar jikokin su.

Ita ma Delun ba auren soyayya a ka mata da Umaru Sanda ba. Auren hadin iyaye ne, kamar yadda a kan yi a wancan zamanin.

Alhaji Sanda abokin kanin mahaifin ta ne, wanda a wani lokacin da ya kai wa ziyara ne, ya gan ta. Kan ta da tallen fura, ta na tafiyar ta cikin natsuwa.

Ya saye furar duka, har ma ya sa ta karo ma sa sauran na gidan na su da ta bari a na dakawa, duka ya saye. A wannan rana farin ciki ta yi saboda ba ta sha wahalar zagaye ba. Shi kuma Alhaji Sanda ya san abin da ya hango.

Ko da ya tambayi abokin sa Ghali ko diyar wace ce wannan? Ghali ya shaida ma sa diyar Yayan sa Lawwali ce. daga nan su ka ci gaba da hirar su kamar yadda suka saba. Amma sha’anin zancen manya, Ghali ya fahimci akwai manufar abokin sa ga Delu.

Ba tare da wani dogon bayani ba, ya tarar da Yayan sa Lawwali ya shaida ma sa, shi kuwa cikin dattaku da kamala, ya kira Sanda, ya shaida ya je da goron sa da sadakin sa don ya ba shi Delu a matsayin matar auren sa.

A wancan zamanin da yake ba abin hawan ne sosai ba, tawagar Alhaji ta makara. Shi kuwa Yaya Lawwali ya ga lokaci zai kure, ya sa Ghali ya karba ma sa auren, sannan a ka daura a kan sadaki ajalan, ba lakadan ba.

Sai bayan isar su ne su ka kai sadakin, sannan a ka ce ya tafi da matar sa. Duk wata bidi’a an sawwake ma sa, a ka hada su da mata biyun da a ka yarje su raka ta da ‘yan komatsan ta.

A gaskiya Delu ba son Sanda take yi ba, amma a lokacin ba a san kin bin umarnin iyaye ba. Sannan kuma cikin daula ta shiga, ba a san yunwa ba balle wahala. Ba a aikatau balle abin sana’a. Komai akwai a gidan Alhaji.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now