Babi Na Ashirin Da Bakwai

2.1K 176 122
                                    

Assalamu alaikum.

Na dawo yau ma da sabon ci gaba.  A ci gaba da min uzuri.

Mun sha soyayya a baya.😍😍😘

A yanzu kuma bari mu dan girgiza 🙊🏃😂.

A sha karatu lafiya.




A wannan ranar juma’a hasken ranar bai fito sosai ba saboa gajimaren da ke baibaye da sama, sun rufe ta kamar bargo liif. Duk da haka, babu iska sosai, don haka a ke cikin wani irin yanayin zafi mai ratsa jiki.

Tun kafin fitar Hindu daga gida zuwa gidan su Auwal don nuna was u Baba sabuwar motar ta, Hajiya Lauratu ke hasashen watakila a yi ruwan sama a ranar.

A na bukatar ruwan kam, Hindu ta amince cikin zuciyar ta, ganin yadda ciyayi suke a bushe rabi da rabi, yabanyar irin wadan da ke shuke ta kusa da gari ke nuna alamar mutuwa muddin ba a samu ba. Daya daga cikin yanayin Bauchi da ta gagara sabawa da shi ke nan, wato zafin sa. Ba ita ba, duk wanda ya yi rayuwa a Jos da Pankshin zai samu zafin Bauchi da tsanani.

“Wannan ma ba komai ba ne. Ba ki je Gombe ba ma ke nan.” In ji Bilkisu a safiyar wannan rana, lokacin da ta ke shirin ta na zuwa makaranta, ta je wajen ta don neman aron takalmin da za ta saka da sabbin kayanta na Baby kofiyon, ruwan hoda.

“Ko ma Yola.” Mashida ta jefa nata ciki, lokacin da ta ke zaune a kan kujerar madubi, ta na shafe shafe.

Akwai abin da Hindu ta lura da shi, cewa duk zaman dadewar da za su yi da ita a dakin, ba sa taba zama a bakin gado, ko taba duk wani abin da suka san na Yayan su ne. Natan ma sai sun nemi izinin ta tukunna.

“Ai Yola kam iyaka ne.” Bilkisu ta amince. “Ko da na je bara bikin aure kamar na cire kaya na yi yawo haka.”

Hindu ta dan yi dariya, “Tooo?! Ai da ba kan ta ke nan.”

“Ina kuwa kan ta Anti? Ga shi kuwa a lokacin na yi wani sabon kamu mai zafi.”

Mashida ta kyalkyale da dariya, “Alhajin Yola ba! Mai ruwan nera.” Ta kalli Hindu sosai, sannan ta dora da, “Anty Bilki ta ce dama Allah ne Ya tsaga rabon samun kudin ta ta hannun sa.”

Kan Hindu a daure, ta tambaya, “Ban gane ba?”

“Eh man.” Bilkisu ta tabbatar mata. “Mutum daga haduwar wajen cocktail partyn bikin ya nemi na masa kwatancen gidan da nake. Ko da na yi masa, washegari sai ga shi nan har gidan, ya je cikin mota sabuwa kirar Passat, bayan ya sha jamfar tazarce na shaddar galila mai ruwan algashi (Maroon), ya sha Zanna Bukar ya na wani kamshin turaren Khaleedji. ‘Yar hirar da muka yi bai fi na mintuna talatin ba, ya min sallama, sannan ya fidda wasu makudan kudi ya ba ni, wai shi bai san kalar kayan da nake so ko abin da nake sha’awar ci ba don haka na yi amfani da kudin na saya.”

“Ai fa wannan rana da ina wajen Anty Bilki sai kin saya min kayan zaki.” Mashida ta furta cikin nuna rashin jin dadin ba ta wajen a lokacin.

“Yarinya, wadannan kudade sun zo ne a daidai lokacin da a ke bukatar su kin ji. Da ma bani da isasshen kudi a hannu, Hajiya ba ta son na je na yi taurin kai na nace sai da ta bari. Kudin da na rike a ka sace gidan amarya cikin jakata, na rasa in azan saka kaina. Kawai sai ga wannan bawan Allah ya zo ya kawo kudi ya ban. Allah ne kadai zai saka masa da alheri.”

Mashida ta yi dariya, ta na girgiza kai, “Ko sunan sa fa ba ta rike ba.”

Bilkisu ta juya idanun ta, “Sau dayan nan da ya je wajena fa ba mu sake haduwa da shi ba. Shi yasa na ce kudin ne kawai Allah Ya aiko min ta hannun sa, dolen sa ne kuma ya ba ni.”

Hindu ta tsaya sauraren su cikin ban sha’awa. Ba ta taba samun kanta cikin irin wannan yanayi ba; a ce an yi kwalliya don saurayi, an fita hira har an karbi toshi.

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now