Babi Na Arba'in

1.8K 156 143
                                    

A ranar jumma’a ce Hindu ta wayi gari da bakon ciwon da ya tsakure ta a marar ta. Ba ta fada wa kowa ba a gidan, don ba ta san yadda za ta fara ba. Ba mamaki ma ba komai ba ne, don da cikin ta ya kosa sosai tana yawan jin ire-iren wannan ciwon, kawai daga baya ya bari.

Sai da ya ki tafiya, ya na dawowa kowanne bayan dakika daya sannan ya na karuwa tukunna ta tabbatar ba mai barin ba ne. Mai gaba dayan ne ya zo, Malik ba ya kasar balle ta fada.

Don haka ta yi shiru ta na ta fama ita kadai. Gaban ta ne ya rika faduwa, ta na zumudin son ganin abin da ke cikin ta, sannan ta na fargabar abubuwan da ke gaban ta kafin Allah Ya nufi hakan.

Ta sha jin ma ta su na mutuwa, ta sha jin yara na mutuwa. Bugu da kari kuma, ta sha karantawa sannan matan da ta kan hadu da su wajen awon ciki sun sha bayanin yadda ciwoon nakuda ke da tsanani, wanda a ke hada shi da mutuwa kai tsaye. Ta rika jin taraddadi, don an ce kafar ta daya a duniya take, daya kuma a lahira.

Bilkisu ce ta fara gane cewar Hindu na cikin wani yanayi. Duk da kin amincewar ta, sai da ta sanar wa Hajiya Lauratu. Hajiya ta dan yi fadan rashin sanarwa da wuri da ba su yi ba don komai ya na iya faruwa.

Ba tare da bata lokaci ba, suka nufi asibiti, wurin da a ka gwada ta sannan aka tabbatar musu cewar haihuwar ce, amma da saura. An ba su zabin ko su zauna, ko kuma su koma gida. Hajiya ta zabi zaman, a ka ba su daki ita kadai a ciki don ta sake. 

A gida an bar Zuwaira ce da Mashida, wadan da suka shirya abinci da ruwan zafi a filas hade da sauran kayayyakin da a ke bukata a asibitin. Bayan Bature ya kai su, sai ya koma da Hajiya don ita ma ta yi wanka sannan ta kara shiri. Ta sanar wa kowa cewar it ace za ta rika kwana a jikin Hindu.

Duk da dai Hindun ta na jin dadin kasancewar su tare da ita, ta samu kan ta cikin tsanar hirar da suke yi suna dariya. Ta ji ta fi kaunar a bar ta kawai ita kadai saboda bata son hayaniyar ko kadan.

Wani ciwon marar da ya damke ta ta rike jikin gado ba ta san lokacin da Zuwaira ta umurci kowa ya fice ba. Sai da ya sake ta tukunna ta lura cewar su biyun su ne ciki. Zuwaira sai gaishe ta kawai ta ke yi, ta na zuba ruwan bunun da ta zabga wa sukari ta na ba ta ta na sha.

“Ki rika yawaita yin addu’a, a halin da ki ke ciki yanzu, addu’ar ki karbabbiya ce.”

Hindu dai ta gyada kanta ne kawai. A ce irin wannan ciwo ya damki mutum yaushe zai wani tuna yin addu’a kwakwwara? Kamar Zuwairan ta fahimci hakan, ta dan yi dariya, idanun ta cike da kulawa.

“Na san za ki dauka ba abu ne mai yiwuwa ba ko? Daurewa za ki yi, ki rika karanta duk abin da ya sawwaka gare ki.”

Wani ciwon ya sake rike ta, ta jira ya ware sannan ta rika kurbar numfashi, “Anty, dama da haka kike ta haihuwa ashe?”

Zuwaira ta tintsire da dariya. A yanzu dangantakar su ta yi kyau. Hindu ta rike babbar Yaya fiye da yadda ta dauka tun farko. A kwanaki ashirin da biyar din da su ka gabata kusan ita ke kulawa da Hindun sosai.

Ta kan matsa mata da zuwa motsa jiki, sannan ta hana ta shan bombita saboda kar yaro ya gagara fita idan nakuda ya tashi.

Ta ji wani sabon fargaba. Anya, za ta iya haihuwa da kan ta kuwa? Idan yaron ya gagara fitowa fa, sai an fede ta? Idan ita ce ta mutu, yaron ya tike rabin hanyar fitowa fa?

“Haka kowacce mace ta haifo ‘ya’yan ta duka. Sai dai kawai kowacce da yanayin yadda nakudar ta ke.”

Hindu ta ji tausayin Zuwaira ya kara kama ta. A ce ta na cikin wannan hali ne mijin ta mta cin amanar daa yayi? A ce mace ta na cikin wannan hali amma ta rasa tallafi da taimako daga wanda ta dora masa yarda da kauna, wanda tun farko shi ne dalilin shigar ta wannan halin? Anya, za ta iya juriyar da Zuwaira ta yi, na rasa ganin ‘ya’yan da ta sha wahala kafin zuwan su duniya?

..... Tun Ran Zane Where stories live. Discover now