10

407 28 0
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

       by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*

Assalamu alaikum masoyana,ina farin ciki sosai da irin soyayya da kuke nunamin Allah yabar zumunci ameen,wannan page d'in nakun nagode❤❤❤


Page 10
  Mubinat ce zaune da Amal suna hira. Ita kuwa yadinkon Amal tana tsaye tana sauraron dukkanin hiransu batare dasun saniba.
Amal tace "Amma fa kinyi kyau sosai kodai mun samu baby ne?"
Wani irin bahagon kallo Mubinat ta jefeta dashi tare da cewa "Bana son wulak'anci yaushe akai auren dahar zaku samu baby? Ke nifa gaskya babu abinda ya tab'a shiga tsakaninmu."
Amal ta tashi zaune "Me kikace Mubinat,amma dai daga gurinkine dan nasan halinki"
"Hmmm towai dan Allah ku har zakuyi zaton wani abu anan kusa? Kowa shaidane akan bana son Ya Atif dan haka baikama kuyi tunanin abu makamancin hakaba a tsakaninmu tunda shi kansa yasan hakan."
"To amma dai Mubinat ai yanzu kam ya kamata ace kinyi hak'uri tunda ya zama mijinki,kuma ki sani wlh Allah zai kamaki muddin kika hanashi hakkinsa... "Dan Allah ya isa haka malama Amal,ni dubaki dajiki nazoyi kuma naganki Allah ya k'ara sauki" ta mik'e daniyan tafiya se Amal tace "Oo danna gaya miki gaskya shine zaki tafi ko? To shikenan ameen nagode kigaida gida"
"Kina nufin bazaki rakaniba kenan?"
"Wani irin rakiya kuma keda bakya so agayamiki gaskya,wai Mubinat yaushe kika zama hakane?"
Murmushi Mubinat tayi "Yaushe na zama haka kamar yaya? Bazan iya sauraran maganganunkibane kawai."
"Wlh kin canja tunda kika rasa Ya Farhan gabad'aya halaiyarki suka canja,sam bakyajin magana yanzu wlh,Allah ya kyauta nidai na gayamiki gaskya Ya Atif yana da hakki mai girma akanki garama ki ajiye komai agefe kibashi hakkinsa kodon samun rahamar Allah atattare dake.
"To naji na kuma gode semunyi waya" daidai nan yadikkon Amal tabarsu zuwa d'akinta.
Koda mubinat ta shigo gida tunanin kalaman Amal kawai takeyi wanda gaskiya Amal tagaya mata,dalilin dayasa Mubinat take k'aunar Amal sosai kenan,komai d'acin da zakaji tofa lallai seta gayamata gaskiya,haka ake son k'awa tagari ta kasance da fad'an gaskiya...

Mubinat bata samu kowa a palon Umma ba,kuma taga motar Ya Atif acikin gida,wanda hakan ya tabbatar mata da cewa Atif ya dawo kenan.
Parlour'n Abba ta wuce kai tsaye,duk suna can suna hira inda shureim yake kwance aciyar Atif.
  "Slm,sannu Abba" cewar Mubinat.
"Yawwa sannu mamana kindawo,ya jikin Amal d'in?"
"Da sauk'i sosai"
"To alhamdulillah"
"Dama yanzu nake cewa shureim yaje ya kiraki kutafi"
Sunkuyar dakanta tayi batare datace komaiba.
Umma ce tace "Sekije ki d'auko muku abincinku kutafi dashi."
"Toh" tace tare da ficewa daga parlour'n.
Sam bata son tabar gidansu,amma yazama dole,haka ta d'auko hand bag nata tare da wayanta da kuma abincin ta fito.
Abba da Umma ne suke biye da Atif hargun mota,inda shureim ya karb'i abincin yak'arasa dashi mota sannan suka wuce.
Tunda suka fara tafiya babu wanda yayi magana har kusa kai tsawon minti biyu sannan Atif yace "Wato shine kikabar wayanki a gida ko?"
"Banyi tunanin zaka kirabane that why"
Hannunta ya kamo da d'ayan hannun nashi yana murzasu ahankali batare dayace komaiba.
Jin shurun yayi yawane seya kira sunanta "Sis Mubi lafiya naji kinyi shuru?"
"Banso tafiya bane kuma Abba yace mutafi"
"To amma ai dama bamuyi dake cewa zamu kwanaba"
"Nasan hakan,kawai dai gidanne bai isheniba"
Shuru yayi nad'an wani lokaci sannan yace "Tokiyi hak'uri,wani sati zan kawoki da safe kizo ki yini hakan yamiki?"
"Da gaske kake?"
"Yeah"
"Nagode sosai" tana jin dad'i acikin ranta dayake tasan kafinnan lokacin Ya Farhan yadawo.
  Bayan sun isa gida seda sukai wanka sannan sukaci abinci se bacci.
Tunda ta kwanta take tuno hiransu da Amal amma ina, batajin zata iya baiwa Atif kanta ayanzu sedai wani lokacin.
Shikuwa yana manne da ita yana mata wasanni da hakan sukai bacci...

Yau take ranan laraba, kuma yaune Ya farhan zai shigo gari. Bacci sosai Mubinat takeyi yayinda Atif yaketa wasa da gashin kanta.
Mik'a tayi tare dayin magana cikin muryan bacci "Please Ya Atif kabarn"
"No, tashi zakiyi kinmanta yaune zamuje yini gida?"
Furgit ta tashi "Are you serious?"
"Yes,kinsan yaunema Farhan zai dawo so gara mucika gidan kamar yadda muke ada"
Rungumeshi tayi cikin farin ciki tare da fad'in "I love you Ya Atif"
"I love you too Sis Mubi,sannan suka fara tsunbatar junansu. Sun jima ahakan sannan ya janye lips nashi ahankali yayinda take rufe da idanunta tana lashe lips nata da harshenta.
Sam tak'i bud'e idanunta,ganin hakan yasa Atif sake kai lips nashi kan nata suka sake sabon shafi.
Hmmm abun nasu babu sauk'i sam,tun suna zaune har suka koma suka kwanta. Ita kanta Mubinat abun mamaki ya bata saboda sam bata so Atif ya saki lips nata,wanda lokuta da dama itace ke fara janye jikinta daga nashi.
Ganin yadda Mubinat ta saki jikine yau Atif ya samu daman sarrafata yadda yakeso,azuciyarsa yace Allah ya d'aurani akanki yau dadare zan gwada neman hakkina agareki Sis Mubinat.
Idanunta ta bud'e tana kallonsa cike dajin kunya,da wuri ta kare fiskanta da hannayenta tana murmushi.
"Yadai Sis Mubi?" Ya tambayeta yana cire hanunta daga fiskanta.
Mik'ewa tayi zuwa toilet tana dariya tare da kallonsa. Shima toilet d'in ya nufa amma seta sa key. "Ni kikawa haka ko? Zamu had'u anjuma ai" ya furta sannan ya wuce d'akinsa don shiryawa shima.

Anko galila ash colour sukayi wanda yasha aiki mai kyau sosai. Mubinat riga da skeet ne,shi kuwa tazarce sunyi matuk'ar kyau fiye da tunani sannan suka kama hanya.
  Hira sukeyi cike daban sha'awa har suka isa gida. Shureim yanata murnan zuwansu da kuma na dawowar Ya Farhan d'insa.
Dama tea da bread sukasha kawai agida,dan haka sukaci abincin Umma sannan suka zauna hira.
10:20am Mubinat tacewa Atif zataje ta taya Umma aiki,hakan yasa yace da ita zaije gun friends nashi kafin isowar su Farhan.
Hira sosai Umma takeyi da 'yarta tana maijin dad'i aranta,danta lura yanzu kamar babu wata damuwa atattare da Mubinat,addu'a tayi acikin ranta na Allah ya basu zaman lafiya yasa ta mance da Farhan  gabad'aya tunda taga babu wata matsala kuma Atif ma bai tab'a cewa komaiba koda Abba yake tambayarsa ranan seyace wlh babu wata matsala suna zaman lafiya.
Umma ta gama komai cikin sauri dake itada Mubinat sukai aikin. Hakan yasa suka wuce yin sallan azahar,ai kuwa se suka jiyo horn.
Da gudu Shureim ya fita yana "Oyoyo Ya Farhan"
Muryan Farhan taji yana cewa "Ooh my Shureim,I missed you so much"
Dariyan Shureim take jiyowa da muryan Ahmad yana cewa "To shureim shikenan hankalinka ya kwanta ko?"
"Sosaima Ya Ahmad,idan kaga dama karka sake zuwa dubani yanzukam tunda Ya Farhan d'ina ya dawo."
Muryan dariyansu takeji dai-dai nan ta idar da sallan tana murmushin itama. Da hijabin ajikinta ta fito,sukuwa sun shigo parlour'n tare da sallama.
"Wa'alaikumus salam,Ya Farhan sanu da dawowa" ta furta yayinda sukeyiwa junansu kallon kewa. "Yawwa Sis Mubi nasameku lfy?"
"Lafiya lau yakabaro su Ummi?"
"Alhamdulillah lafiyansu k'alau suna gaisheku" yafad'a yana mai kallon yadda ta k'ara haske.
Gaisuwar da takeyiwa Ahmad ne yasa ta katsewa Farhan tunaninsa. Umma ce ta fito,nanma aka sake gaisawa sannan suka wuce sides d'insu Farhan danya watsa ruwa. Seda suka isa sannan Farhan ya tuna da cewa bai karb'i key d'in d'akinsaba gun Umma,gashi su Shureim sunje mota kwaso kayansa,hakan yasa yayi niyan komata gun Umman kawai seka Mubinat rik'e da key d'in Umma ta aikota.
Kallon juna suka tsayayi sannan ta mik'a mishi tace "Wai inji Umma tamance bata baka key ba"
Hannunsa yasa ya karb'a yace "Nagode"
Juyawa tayi ta koma, yana tsaye yana binta da kallo azuciyarsa kuma yace "Ooh habibty, I miss you" duk akan idon Atif...

                                 Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAADonde viven las historias. Descúbrelo ahora