30

318 19 2
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
       We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers💐



👯👯👯👯👯
Wow! Murna nake sosai,sabida #KNJ ya samu makaranta har sama da 1k a wattpad❤nagode sosai da bibiyar novel nawa da kukeyi Allah yabar zumunci ameen.
      🌹🌹🌹🌹🌹🌹



Page 30
"Wa'alaikumus salam" suka amsa yayinda Farhan ya janyo plate d'in da Mubeenat taci abinci ya zuba nashi akai ya fara ci se Shureim yace
"Ya Farhan a plate d'in da Sis Mubee taci kake ci baga nan plate dewa anan ba?"
Karaf a kunne Atif,dan haka ya tsaya yana kallon Farhan tare da plate d'in.
"Eh naga plate d'in ai,bana so musa Umma aiki ne shiyasa naci a natan" ya k'arasa maganar yana kallon fuskar Atif.
Cikin jin haushi ya wuce d'akin Mubeenat,shi kuwa Farhan yayi murmushi tare daci gaba da abinda yake yi.
Mubeenat kuwa duk taji yadda sukayi,dama hankalinta gaba d'aya yana gunsu.
Shigowar Atif ta gani babu ko sallama dan haka tace "Ya Atif babu ko sallama?"
Rai a b'ace yayi magana "Me yasa da kika gama cin abincin ki baki kai plate naki kichine ba?"
"Naga su Ya Farhan sun shigone kuma kace kar'in bari muna ganin juna sosai shiyasa kawai nabar plate d'in agun,akwai wani abu ne?"
"Ba komai"
"Haba Ya Atif menene ya faru haka naga dukka sauya min?"
"Ba komai daga yau idan kinci abincin ki kikai plate d'in kichine"
"Ok,in zubo maka abincin ne?"
"No ki bari kawai naci abinci agun mom"
"Are you sure?"
Kallonta yayi tare da rungumeta yace "Yeah,please Sis Mubee ki guji duk wani abu da kika san zai b'ata min rai."
"Insha Allah Ya Atif,yawwa dama ina so in tambaye ka zan dinga shiga gurin Amal muna hira"
A hankali ya saketa tare da cewa "Sis Mubee gaskiya bana son yawan fitan ki"
"Eyyah Ya Atif kafa san yadda nake da Amal,sannan kasan halin da take ciki dole in dinga shiga ina d'ebe mata kewa tunda muna kusa" ta k'arashe maganar cikin shawab'a tana jingine a jikin sa.
Fuskarta ya shafa "Ok naji,but please kar fitan yayi yawa sosai kinji?"
Murmushi tayi mishi "Yes my love"
Jin sunan data kira shi dashi ne yasa shi shiga wani yanayi,nan suka tsaya kallon junansu kowa da tunanin da yakeyi a ranshi.
Lips nata ya koma kallo ji yake kamar yayi kissing nata amma babu halin yin hakan a yanzu dan haka ya mik'e tsaye tare da cewa "I'm leaving,mezan kawo miki idan zan dawo anjuma?"
Itama mik'ewa tayi cikin jin tausayin shi ta rik'o hannayen sa biyu tare da janyo shi ya fad'o a kafad'arta ta rungume shi.
"Duk abinda kaga yayi maka ka sayo min,sannan please ka dena sa tunanin komai a ranka Ya Atif bana so kaje ka sake fad'awa cikin wani hali please?"
Kameta yayi sosai a jikin shi shima yana shak'ar k'amshin jikinta "Yanzu shikenan nida Matata amma babu halin inyi wani abu da ita? Abin yana damuna sosai Sis Mubee,wai ko kissing naki bazan iya yiba yanzu?"
Tausayin shi ya sake kamata a karo na biyu,cikin dad'in murya dason kwantar mishi da hankali tayi magana "Kana felling d'inane Ya Atif?"
Kansa ya d'ago yana kallonta "Haba Sis Mubee,taya zaki min wannan tambayar bayan ko idanuna kika gani zaki iya ganewa?"
Kansa ta kamo kamar wani k'aramin yaro ta d'aura akan k'irjinta shi kuwa seya samu dama har wani juyi yakeyi da kan nasa cikin wani irin salo,tace "I'm sorry Ya Atif,aduk lokacin da kake cikin irin wannan halin kayi gaggawan zuwa gurina insha Allah zaka samu farin ciki a tare dani."
Ya dad'e a hakan sannan ta d'agoshi tana mishi murmushi tare da lumshe idanunta "Kaji my love?"
Peck ya manna mata a lips nata tare da sake rungumeta sosai yace "Thankyou"
"Shhhhh karka sake min godiya,miji bayayiwa matarsa godiya sedai ita tayi mishi a nawa fahimtar."
Dariya yayi sosai yace "I love you Sis Mubee"
"I love you more Ya Atif"
Kamar bazasu rabuba dak'ar yayi mata sallama ya fito daga d'akin.
Karaf suka had'a ido da Farhan,nan Atif ya shiga masa mugun kallo shi kuwa Farhan abincinsa yake kaiwa baki tare da k'arewa Atif kallo.
"Shureim mik'awa Atif wani plate yaci abinci"
"To Ya Farhan"
"Bari Shureim,jeka ka d'auko min ruwa" cewar Atif.
Nan Shureim yabar gurin,Atif ya kalli Farhan yace "Da dai da yunwa na shigo,amma yanzu a k'oshe nake domin naci abinda yafi wannan dad'i yanzu."
Murmushi Farhan yayi tare da kai spoon na k'arshe a bakinsa sannan ya lashi lips nasa ya mik'e tsaye "Ba dad'in abincin bane yasa nake cin abincin haka sosai sedan d'and'anon bakin Habibtynah da yake jikin spoon d'in."
Lips nashi ya sake lasa yaci gaba da cewa "Verry sweet,infact sweeter than honey,gaskiya yau bazan goge bakina ba saboda bana son wannan d'and'ano mai dad'in ya k'auracewa bakina."
Wani irin takaicine ya kama Atif,harya yi yunk'urin kamo rigan Farhan sega Shureim yazo rik'e da goran ruwa yace "Ya Atif ga ruwan nan"
Lokacin suna yiwa junansu wani irin kallo yayinda shi Farhan yayi murmushi yace "Yawwa Shureim bashi ruwan yasha dan dama akwai wani abu daya tsaya mishi a wuya yanzu ko Atif?" Ya k'arasa maganar cikin raha sannan ya wuce tare da kashewa Atif ido d'aya.
Ruwan Atif ya karb'a a hannun Shureim da yake binsu da kallo dukkansu.
"Lallai zan koya maka hankali Farhan,wato abin naka harya kai nan? Zan nuna maka banbancin d'an Nigeria da Balarabe! Ya fad'i hakan a cikin ransa.

Mubeenat tana jiyo komai daga bakin k'ofa da take tsaye,dan haka taketa dariya a cikin zuciyarta tare da tunanin "Yaushe kuma Ya Farhan suka fara haka da Ya Atif?"
Nan dai taci gaba dayin dariya tana sake tuna magan ganunsu tana jin dad'i har cikin ranta,wato dama har yanzu Ya Farhan yana sona? "Wai Habitynah" hhhhh...
Atif ya koma d'akin ya sameta se dariya takeyi.
"Ya Atif,dama baka tafi bane?"
Kallonta yakeyi cikin tuhuma,ganin hakanne yasata wayancewa dan bata so ya ganota.
Rungumesa tayi da sauri tace "Tunda ka tafi nake tsaye a inda ka barni gani nake kamar baka tafiba se kallon gurin nakeyi ina murmushi ni kad'ai"
Jin yayi shurune yasa ta sake cewa "Garama da baka tafiba my love,please kazo mu kwanta ka huta inyaso zuwa anjuma seka tafi please Ya Atif?" Ta k'arashe maganar cikin shagwab'a kamar zatayi kuka tana janyoshi zuwa kan gadonta.
Nan dai gogan ya mance da komai ya fara washe baki tare da cewa "Are you serious Sis Mubee,taya zan kwanta anan,idan akazo aka samemu fa?"
"And so,kowa yasan mijine tare da matarsa please let's sleep Ya Atif?" Ta fad'a cikin wasa tare dayi mishi cakulkuli.
"No Sis Mubee please stop it,i say stop it please" yana dariya sosai itama haka.
"Sis Mubee" suka jiyo muryan Shureim daga parlour.
"Na'am"
"Umma tana kiranki"
"To ganinan zuwa" sannan ta kalli Atif shima ita yake kallo.
"Ka jirani ina zuwa kaji?"
"No i'm leaving,k'ilama Umma ta jimu duk kece ai i'm telling you to stop amma kink'i"
"Kana tanka minne in sake maka wani?" Tayi maganar tana d'aga mishi gira.
Cikin sauri yayi magana tare da rungumeta "No my love i'm sorry,nizan tafi sena zo anjuma"
"Ok you take care" ta manna mishi peck a goshinsa sannan ya tafi.
Dariya sosai Mubee tasa tare da cewa "Huuh,Allah na gode maka dabai ganoni ba" sannan ta fice tana murmushin kanta...


                            Team #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now