49

275 17 2
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

     by maman shureim
            🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
        We don't only entertain and educate,but we also touch the heart of the readers❤

#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
#IG PML WRITERS
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com


Wannan k'arin shafin naki ne miemiebee,ina matuk'ar jinki har cikin raina ina fatan wata rana Allah yasa mu had'u ko kuma idan aurenki ya tashi da...😜bari dai inyi shuru Allah ya nuna mana ameen.
       LYSM BABE💋




   Page 49
Abban Mubeenat yana zaune a office yaga bak'uwar number kamar bazai d'auka ba se kuma ya d'aga.
"Slm"
"Wslm sannu Alhaji,d'aya daga cikin ma'aikatan TAIMOOR COMPANY ne a hanyar wucewata ne naga motar Sir Farhan tayi hatsari shi da wani k'aramin yaro yanzu haka suna asibiti"
Cikin kid'imewa Abba yake furta "Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un wace asibitin kenan? To ganinan zuwa amma dai suna lafiya ko?"
"Eh to muma bamu saniba gaskiya domin doctors suna kansu,amma muna fatan suna halin lafiya dukda dai shi Farhan d'in yaji raunuka sosai ajikin shi."
Salati Abba yaketayi tare da wucewa asibitin kai tsaye bayan ya sanar da wansa wato Dad d'in Atif.
Bayan sun iso asibitin ne yake tambayar doctors "Ya masu jiki?"
"Kayi hak'uri Alhaji kad'an jiramu please muna kan aiki ne" yana kaiwa nan ya wuce ciki yabar Abba tsaye yanata addu'a a kid'ime.
Numbar Umma ya kira "Yaushe Farhan ya fita ne? Kuma shi da wa suka fita?"
"Lafiya Abban Mubeenat? Shida Mubeenat ne da kuma Shureim sunje gaida Maman Aisha"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un"
"Abban Mubeenat lafiya kuwa?"
"Hatsari sukayi a hanya,amma kuma ni Farhan da Shureim ne aka cemin an kawo asibitin ai,ina ita Mamana d'in take to?"
Bai jira me Umma zata ceba ya katse wayar tare da kiran Mubeenat,tana ganin Abbanta ne ta d'aga da sauri "Assalam Abba"
"Mamana kina ina ne?"
"Abba ina gun Maman Aisha ban dad'e da zuwa ba"
"Ke da wa?"
"Ya Farhan da Shureim ne suka kawoni,amma sun koma inaga ma basu k'arasa gida ba dan basu dad'e da tafiya ba"
"Shikenan to" sannan ya katse wayar.
Mubeenat tayi mamakin meyasa Abba ya kirata,dan haka ta kira wayan Farhan yanata ringing ba'a d'agawa,can sai taji an d'auka "Hello baiwar Allah kina magana da Mahmud ne"
"Mahmud kuma? Dan Allah mai wayar fa?"
"Kiyi hak'uri bazaki iya magana da mai wayarba a yanzu" yana fad'a mata saiya swiching off na wayan gaba d'aya ya mik'awa wani police d'in da dai sauran abubuwan da suka samu a motar.

Hankali tashe Mubeenat ta sake kiran wayan amma sai taji a kashe. Mamakine ya bayyana k'ak'ara a fuskarta dan haka ta kira Atif "Hello Ya Atif kana gida ne?"
Cikin wata irin murya yace "Muna hanyar zuwa asibiti"
"Asibiti kuma? Kai da wa?"
"Nida Dad"
"Dad kuma lafiya?"
Nanne Atif ya fahimci cewa batama san me yake faruwa ba,dan haka yace ke kina ina ne?"
"Ina gidan su Aisha Kabir yanzu Ya Farhan da Shureim suka saukeni kuma na kira wayanshi yanzu naji wanine ya d'aga sannan ya kuma kashe wayar"
Cikin jin tausayinta yace "Bari nakai Dad hospital zanzo na d'aukeki"
"Karka damu nasan Ya Farhan yana sane da cewa bayan azahar zaizo ya d'aukeni"
"Sis Mubee Ya Farhan bazai zo ya d'aukekiba domin akwai abinda yakeyi ya gayamin zanzo in d'aukoki"
Cikin rashin fahimta tace "To" sannan ya katse wayar dai-dai lokacin suka iso asibitin.
Abbane ya k'arasa gunsu inda Dad d'in Atif yake tambaya "Yasu Farhan d'in suke?"
"Har yanzu dai babu wani abu da suka ce tukunna sai sun fito."
Haka suka tsaya shorko-shorko suna ta salati can sega doctors sunata fitowa daga d'akin.
Cikin sauri suka k'araso "Doctor ya masu jikin?"
"Jiki da sauk'i,shi k'aramin yaron ya karye a hannunsa na dama da kuma k'afar hagu amma insha Allah zai samu lafiya danmun mishi d'auri baima saniba sakamakon suman dayayi."
Shi kuma Farhan Taimoor gaskiya yaji raunuka sosai dan gefen kanshima tad'an bugu yanzu dai saiya farka kafin musan menene yake damunshi amma dai ku tayamu da addu'a."
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un" shine dukkansu suke iya furtawa cike da tausayawa akan fuskarsu.

KOMAI NISAN JIFAAWhere stories live. Discover now