29

360 18 2
                                    

🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸
KOMAI NISAN JIFA
🌳🌸🌸🌳🌸🌸🌳🌸🌸

      by maman shureim
             🌺sad-nas🌺

*©Pure Momment Of Life Writers*
          We don't just entertain and educate,we also touch the hearts of the readers



Page 29
"Farhan lafiya,me yake faruwa?" Abba ya tambaya.
Cikin b'acin rai yace "Bakomai Abba"
"Kamar ya ba komai bayan naji hayaniya?"
"Mund'an samu sab'ani ne dashi amma ya wuce kayi hak'uri."
"Kai da wa kenan?"
"Da Atif"
"Atif d'in yazo ne?" Cewar Umma.
"Eh yana ciki" sannan ya wuce zuwa d'akinsa Abba yana binshi da kallo.
"Kai,gaiskiya akwai abinda yake faruwa a tsakanin su biyun,duk nasan bazai wuce akan Mamana ba"
"Ni wlh Alhaji wannan lamari yana bani mamaki kamar wani dramer'n hausa? Allah yayi mana mai kyau to."
"Ameen" cewar Abba

Mubinat tana kwance a d'aki tana kallo se taga Atif,da sauri ta tashi suka rungume juna sannan tace "Dama zaka zo?"
"Me zai hanani zuwa,d'azuma babu yadda zanyine shiyasa na tafi but i'm sorry okay?"
"It's nothing Ya Atif,but ai dakamin bayani amma kawai senaji tashin motarka."
"I'm sorry for that" ya fad'a yana murmushi.
Itama murmushin tayi tare da janyoshi ya zauna akan gadonta.
"Sis Mubee"
"Na'am"
"Farhan yazo kunyi magana ne?"
"Nop,nifa tunda na shigo gidanma banga fuskar shiba har yanzu"
"Ok,please Sis Mubee bana so inga kuna zama dashi ko kuma wani hira,kiyita zamanki a cikin d'aki tunda kinga har yanzu akwai aurena a kanki."
"Insha Allah zan kiyaye" ta fad'a tana shafar fuskarsa da hannunta.
"Thankyou,kinga yanzu kuna gida d'ayane dashi,bawai ban yarda daku dukka bane sedai kinsan shaid'an yana iya yin komai right?"
"Hakane,na kuma fahimceka,babu abinda zai faru insha Allah"
"And banda walliya babu sa english wears bana soma ki fito parlour ki zauna kiyita zamanki a d'akinki tunda ga kayan kallonki sannan duk wani abu da kike buk'ata karki tambayi kowa ki sanar dani i will do anything for you love" ya rungumeta.
"Okay" ta fad'a suna yiwa juna murmushi.
Bayan fitar Atif daga gun Mubinat ne seya wuce parlour'n Abba,suka gaisa nan dai ya sake basu hak'uri akan abinda ya faru tsak'aninshi da Sis Mubee,magana sosai sukayi da Abba sannan ya tafi.

Farhan kuwa sam ya kasa bacci a wannan daren,ya kwanta da tunanin Furucin da Atif yayi masa,shikuwa yasa a ransa seya gano gaskiyan lamari da yardan Allah.
Washe gari bayan sun gaisa dasu Abba ne yaje ya shirya zuwa 7:00am ya fita ba tare dayaci komaiba. Kodaya fita seya rasa ta inda zai fara,haka dai yayi ta yawo ko zaiga wani daya san lokacin da hatsarin ya faru amma sam babu wani abu daya samu a wannan ranan haka ya sake dawowa gida.
Tunani sosai Farhan yayi,bazai iya zama tare da Mubinat ba a gida d'aya yana kallonta,dan haka yacewa Abba zai koma karantarwa a Islamiyya kamar yadda ya saba a weekends,sauran ranaku kuwa yana company.
Abba yaji dad'i hakan sosai dan koba komai yanzu Farhan ya samu lafiya kamar yadda yake ada.
"Hakan yayi kyau Farhan Allah ya taimaka Allah yayi maka albarka"
"Ameen Abba nagode"
"Mahaifinka ma ya kusa dawowa ai ko?"
"Eh Abba yace wani sati zai dawo,sedai idan ya dawoma Umrah zai tafi"
"Eh lallai haka ya gaya min,su Hajiyana ma wani satin zasu dawo"
"Ok Allah ya dawo dasu lafiya"
"Ameen Farhan nagode"
"Bakomai Abba."

Mubinat da shureim ne suke zaune tana ce mishi "kaje gidansu Amal kace wai tazo ina gida"
"To" yace sannan ya fice da gudu yaje ya sanar da Amal.
Bayan yadawo da minti talatin sega Amal tazo rik'e da wayan Mubinat a hannunta.
"Dama ashe agunki nabar wayata"
"Eh wlh tun lokacin da kika fad'i ai Ya Farhan ya bani wayan yace in rik'e miki,yanzu ma kuwa nacewa Ahmad yazo ya kaini gidanki sega Shureim wai kina kirana dama kuma aiki nakeyi sedana gama na fito."
"Kullum cikin aiki Amla,bakya hutu sam?"
"Hmmm kedai bari,yadda kika sani ada har yanzu babu wani canji,kawai na gaji da zuwa gayawa Abba ne kullum kayita kawo k'ara yau da gobe za'a gaji dakai wlh shiyasama nayi gum da bakina wahala bata kisa ai Mubee komai lokacine idan nayi aure ai shikenan."
"Wlh bazai yuba,danta samekine shiyasa take iskancin dataga dama makira maciya amana wlh k'arshenta bazai mata kyauba insha Allah."
"Ni dan Allah kibar wannan maganan,yaushe kika zo?"
"Ai tun jiya ina nan,daga can gun doctor muka wuce akamin gwajin aka ga babu,amma doctor yace se anyi sau uku tukunna mu gaskata result d'in" nan dai Mubee ta gayawa Amal komai har dalilin zuwanta gida da kuma zaman da zatayi a gida.
"Ikon Allah,nima ina da laifi kenan tunda nima na bashi wannan shawaran nace karyayi k'ok'arin tab'aki yad'an baki lokaci."
"Ki dena damuwa Amal haka Allah ya k'addara"
"Hmmm" cewar Amal
"Me kuma na cewa hmm?"
Nan Amal ta shiga tunanin wani rana da wata take gayawa k'awarta cewa Atif ya nemi dayayi alfasha da ita amma sam tak'i. Ita kuwa Amal a lokacin sam bata yardaba dan tasan ba haka halin Atif yake ba,lokacin da ita wancan d'in tabar gurinne se Amal take cewa k'awar nata "Kodai son Ya Atif d'in takeyi shine zata mishi wannan sharrin?"
"Anya kuwa Amal,gaskiya saratu baza ta mishi sharriba saboda kinsan saratu da iya bad dressing maybe idan an ganta se'a d'auka ko 'yar iskace zaiyu ya nemetan ai tak'i."
"To irin wannan banzan shiga kana d'an musulmi ai dole ayi tunani koba ta gari bace,Allah ya shiryar damu baki d'aya."
Se yanzu maganan ya fad'o mata arai tace wato dama wancan maganar gaskiyace kenan?"
"Ke Amal tunanin me kikeyine haka?" Cewar Mubinat
"Bakomai,Allah ya bashi lfya,ke kuma Allah ya kareki yasa sauran result d'in baya ma muga alkhairi."
"Ameen,yaushe ne bikinku da Ahmad ne?"
shuru Amal tayi tana tunani sannan tace "Mubee agaskiya bana so inyi aure harse an gano inda Mahaifiyata take,idan kuma mutuwa tayi to ina son ganin gawarta" tana kaiwa nan ta fashe da kuka mai k'arfi.
"Please Amal kiyi hak'uri,da nasan kuka tambayar nawa zata janyo miki daban yiba"
"Ko baki yimin tambayar ba kullum burin Ahmad shine yaga an d'aura auren mu,amma inata b'ata mishi lokaci Mubee ya zanyi?"
"Dan Allah ki dena kukan haka ya isa,insha Allah za'a samota da yardan Allah."
Ita kanta Mubinat ta fad'i hakanne kawai dan hankalin Amal ya kwanta,kusan shekara biyu kenan amma babu labari har yanzu?
"Mubinat kukan waye nakeji haka?" Cewar Umma.
"Amal ce Umma"
Umma ta shigo cikin d'akin tare da tambaya "Amal me kuma ya faru?"
"Umm tunawa da Mahaifiyarta tayi" cewar Mubinat.
"Kiyi hak'uri Amal muci gaba dayin addu'a insha Allah zamu ganta kinji?"
Cikin muryan kuka tace "To Umma nagode"
Sannan Umma ta fita tana mai tausayawa Amal,mutum kusan shekara biyu babu shi babu labarinsa? Gaskiya wannan abu akwai d'aurewar kai.
Amal ta kalli Mubeenat tace "kinsan Sagir ya dawo jiya kusan goma na dare,bayan ya gama gaisawa da Uwar tasa da Baba ne yayi musu seda safe ina jinsu seya nufo d'akina yanata buga k'ofar a hankali wai in bud'e ya ganni yana so yaga yadda nayine yanzu ko komai nawa ya sake ciccikowa,maganganu narasa dad'in ji wlh niharma na tsorata dan gani nake zai bud'e da k'arfi ya shigo min,wlh Mubee na fara gajiya da zaman gidan Allah."
Tausayinta ya sake shigan Mubee tace "Subhanalillah,wato shidai bazai tab'a canjawa bako,d'an iska tsinanne wlh sena had'ashi da Ya Farhan dan wlh idan ba'a taka mishi birkiba to lallai wataran zaiyi abinda yake da niyan yi."
Haka sukaita hira tana baiwa Amal hak'uri harta mik'e tace "Naji dad'i ai yanzu tunda kina gida zaki dinga d'ebebin kewa Mubee."
"Insha Allah zan dinga shigowa dan Allah ki dena kuka komai zaizo k'arshe da yardan Allah."
"Nagode Mubee sena sake shigowa da dare"
"Base kin zoba nima zanzo miki hira anjuma bari Ya Atif yazo in tambaye shi"
"Ok sekin zo" sannan ta fice tana goge k'walla.

Hankali Mubee a tashe ta fito daining tana cin abinci sega Shureim da Ya Farhan sun shigo. Tunda yaga Mubee zaune akan daining seya juya tare da cewa Shureim "Kaje kaci abinci nise anjuma zanzo naci nawa"
"Me yasa ka fasa ci yanzu Ya Farhan,kodan kaga Sis Mubee ne agun?"
D'ago da kanta tayi suka had'a ido dashi se tayi saurin sunkuyar da kanta tana tunani "Kodai Ya Farhan ya fara gudu nane saboda halinda Ya Atif yake ciki,yana tsoron karna rab'esu kenan? Kai amma sam Ya Farhan bazai min haka ba,to me dalilin hakan tunda nazo ban ganshiba se yanzu kuma nasan dole Shureim zai gaya mishi ina gidan yama san komai."
Ganin zai fitane ta mik'e tare da cewa "Ya Farhan" tsayawa yayi cak ba tare daya juyoba yace "Yes Sis Mubee"
"Ya Farhan i wana talk you"
Juyowa yayi,ita kuwa ta k'araso kusa da inda yake tana kallonsa yayinda shi kuma yake kallon Shureim zaune akan daining.
Ta lura ko kallonta baya sonyi a yanzu,dan haka tahau tunanin kodai Ya Atif yayiwa Ya Farhan maganane kamar yadda yayi min akan sa?
"Sis Mubee i'm here" ya fad'a yana kallonta babu ko murmushi a fuskarsa.
Jikinta yayi sanyi tace "Ya Farhan is everything okay?"
"Yeah,just go on ina sauraron ki"
Shuru tayi tana kallonsa har cikin ido amma sam yak'i kallonta.
"Sis Mubee are you ready to talk?"
"I don't know,sabida kak'i ka bani dama"
"In tafi kenan?"
"Duk yadda ka gani Ya Farhan"
Kansa ya mayar zuwa gareta suna kallon juna "Me yake faruwane Ya Farhan,ko wani laifin nayi makane ka sanar dani."
Harcensa ya fitar ya lashi lips nashi tare da kallon Shureim "Baki min laifin komai ba,ki dena tunanin wani abu ki gayamin abinda kike da niyar fad'a min"
"Amma aini naga canji daga gareka,ko kallona baka sonyi,me dalili Ya Farhan,kodai ka fara k'yamata ne?"
Da sauri ya juyo yana kallon ta "Me yasa zaki min irin wannan fassaran Sis Mubee,har abada Farhan bazai tab'a k'yamar kiba ako wace irin hali kike,dan haka ki cire wannan tunanin a ranki please"
"To me hakan kenan?"
"Sis Mubee please,ki gayamin abinda kike son gayamin,bana so Umma ko Abba ko Atif suna yawan ganina dake sabida gudun zargi."
Jikinta yayi sanyi ta kuma ji tausayin shi sosai "Shikenan na fahimceka Ya Farhan,wato Ya Atif ne yaje ya sameka ko,shine nima zaizo ya kafa min dokoki akan ka,hakan yayi kyau sosai."
"Please Sis Mubee bana son wani tashin hankali please kibar wannan magana,ni babu wani abu da Atif ya gayamin kawai nine naga hakanne ya dace."
"Yanzu ki gayamin abinda kike son gayamin,kodai dama shine maganan?"
Ajiyar zuciya ta sauke "Shikenan tunda kace haka,dama magana ce akan Amal"
"Ina sauraron ki"
"Ya Farhan Sagir ya dawo a daren jiya,sannan koda ya dawo da wasu yanayi ko kuma ince halayya ya dawo marasa kyau,tunda jimawa yakan yi iya shejensa amma bata kulashi kuma kota gayawa Mahaifinta se Matarsa tasa baki shikenan maganan ya wuce ba tare da an d'auki wani mataki ba,to jiya kuma d'akinta yaje yanata bugawa tare da wasu irin maganganu marasa dad'in ji wai seta bud'e mishi k'ofar d'akinta."
Shuru Mubeenat tayi tare dajin kunyar abinda ta gayawa Farhan.
"Shikenan?" Ya tambayeta yana kallonta
A hankali ta d'ago suka had'a ido ta d'aga mishi kanta alamun
"Ehh"
"Ba damuwa,zan san yadda zanyi,shikenan?"
"Eh,nagode"
Harya juya zai fita se tayi saurin cewa "Ya Farhan kaje kaci abincin ka,nina gama."
Murmushi yayi yana binta da kallo harta shige d'akinta sannan ya wuce daining ya zauna kusa da Shureim se suka jiyo sallamar Atif "Salamu Alaikum..."

                               Yeam #KNJ

KOMAI NISAN JIFAAWo Geschichten leben. Entdecke jetzt