MATAN ALI

1.8K 141 22
                                    

MATAN ALI.
(the most lovely story of nice family)

 
BILKISU BILYAMIN

     *1  END*

    Ya kasa yanda zai mayi shari'ar duk wani tunaninshi ya tsaya,harwani sashi na zuciyarshi yana tunanin baima shi Alin Adalci ba, da ya kasa nema mashi yara masu tarbiyya,bayan Ali ya dawo daga rakiyarsu ya iske Munayya har lokacin tana rusar uban kuka,har inda take ya karasa ya dan duka dai dai yanda zata iya jin duk wani harafi da zai furta,sannan ya bude dakakkiyar muryarshi yace"ban taba ganin asararra ba a duniyarnan irinki,wai ke anya jikin ki na aiki da hankali,to bari in fada maki bazan taba barinki kibar gidan nan ba har sai na tabbatar da na ladaftar dake akan wahalar da kika bani,saboda haka tun ban lalata maki kamanne ba ki tashi maza ki zagaye falan nan da tsallan kwadi,ki maya sau goma"

     "wallahi baka isa ba,bazanyi ba, ka sake nin kuma sai kayi man mugunta"

   "wallahi sai kinyi,ba kuma shi kadai zakiyi ba,akwai wani da zai zo bayan kin gama wannan,na dauka kinsan wa kika aura?"

    "na sani mana, mugu tsautsayi yasa na aura"

    Ai kuwa bata gama rufe baki ba ya daura mata mahaukacin mari a saman bakinta,kamar cizan kunama taji saukar marin,wata kara ta saki sanna ta dafe bakinta,daga bisani kuma jini ya wanke mata hannu,belt ya cire ya dinga nasarta kamar daman an halitta mashi ita danya jibga ne,bayan yayi mata iyakar bugun da yaga ya gamsar dashi,sannan ya dakata,ya fiddo wata farar takarda ya wurga mata yace"wannan bugun na wasa da hankalina da kikayi har kika samu nasarar da na kusance jakka,kazama,kilaki irinki ne,wannan kuma takardar saki ukku ce wadda sanadiyar bin mazanki ya jaza maki,minti biyu na ba ki dauku duk wani abu da kika san naki ne ayi gaba,kika dara haka kuda da sakan daya ne,zaki dana sani a gaba daya duniyarki ta yan iska"

    Da kayr ta iya tashi saboda mugun bugun da yayi mata,duk ya fasa mata jiki ta nufi dakin da ta zauna ta debu yan abubuwan data san zasuyi mata amfani,ta zo ta wuce ta gabanshi ya ci gaba da aika mata zagin da duk ya iya.

   Duk abinda yake faruwa Deji da Aminatu suna kallo ta sakalan kofa,kuka Deji take kamar anci uwarta ta mutu,dariya ita kuwa Ameenatu take tace"saura Waccan mai kama da dangin karunar,nasan ita nata daban ne"

    Kumai tana kallo daga kofar dakinta ganin yanda ya keme Munayya yasa ta kuma daki ta saka key dan bata shirya cin na jaki ba a wajan Ali,zata jira har zuwa sanda zai bar gidan sannan ta tafi,bugun kofarta yake kamar zai balla amman kememe tayi banza dashi ta'ki budewa, tasan idan har ta bude kofar nan tabbas mutuwarta ce ta karatu,saboda haka bata shirya ma,ban kwana da kumai nata ba.

    Jin an daina buga kofar yasa ta tashi da niyyar tafiya,sai ta tuna mugunta irin ta Ali,dakyar inba safayn makulle yaji daukuwa ba ya dawo,ai kuwa da sauri ta kara tura makullen cikin gidanshi,ai kuwa sai taji ana amfani da wani makullen ta baya,jin akwai makulle yasa ya kara buga kofar daga can taji yace"samun saukin whalarki ki fito yanzo,idan kika bari nayi yanda nayi na fiddo ke to abin bazai maki kyau ba,dan billahil lazi sai nayi fatafata da naman jikin ki"

    Da yake ta iya tauren kai da,ke fadi, girman kai sai tace"An gaya maka kuwa banza ne da zai tsaya ka dinga cutarshi,ni ba sakara baci,saboda haka bazan bude ba,idan yasu ka sauke ginin gidan ka fiddo ne"

     Ranshi ya gama baci da duk harafinta daya, wani mugun bugu ya kaima kofar dakin da hannunshi,sai ga jini ya na fitowa amman ku a jikinshi,da saure Aminatu ta fito daga dakin Deji tayi saure ta rike hannunshi tace"please kayi hakuri Ya Ali"

     Wani mugun kallo ya watsa mata wanda da sauri ta sake hannunshi,da saure ta kuma daki ta dauki wayanta ta buga ma Ommar wanda shigowarshi garin kinan daga wata semina da bankinsu aka turashi,ku ida sa shiga gida baiba ya samu wannan waya daga wajan Ameenatu,minti biyar cikakkiya ta sadashi da gidan Alin.

MATAN ALITempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang