ABINDA KE B'OYE Page 11-12

2.2K 183 2
                                    

💧💧 *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      💧

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_

        *_NA_*
  *_FEEDOHM💞_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CE👈_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
*Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*

   page *11-12*

Tunda asuba Lauratu ta tashi fita tsakar gida ta iske Jummai na surfen geron da za'ayi karin kumallo dashi yau "Gwaggo jumma Ina kwana?ta fada tare da dukawa har kasa

  Yatsina fuska tayi tare da tabe wargajejen bakinta sannan tace "Lahiya"
Mikewa Lauratun tayi ta nufi murhu ta debo kakare ta hada wuta sannan ta dauki tukunya ta nufi randa zata debi ruwa……

  Da Sauri jummai ta matso tana fadin "Ke ke tsaya ruwan me zaki diba kuma?

  "Ummana zan daurawa ruwan wanka……"

Wani kallo ta watsa mata sannan tace "To bada ruwan gidan nan ba wallahi don babu shegen da yace ta haihu acikin mu……"

  "Haba Gwaggo Jumma tunda fa ta haihu batayi wanka ba ,dan Allah ki sammani na diba ko ya yane ta samu taji karfin jikinta "ta karashe maganar tana kallon kasa idanunta cike da kwallah……

  "Kar ta ji karfin jikinta lauratu!idan abun ya dameki kije ki debo mata a rafi mana ina jin kinsan inda zaki debo mata!Muma mazajenmu suka debo mana don muyi amfani dasu ba dan ayiwa Shegiya wanka ba……!ta karashe maganar tana tada jijiyoyin wuya

  Juyawa tayi ta dauki tulu ta fita ba tare da tace komae ba sae dae zuciyarta dake tafasa kamar ta kone……Da tsaki Jummai ta raka tana fadin "Shegu masu abun kunya"

  Cikin Sauri ta debo ruwan ta dawo ta sake hada wata wutar har sae da sukayi zafi sannan ta leka bangaren Inno ta aro katuwar ruba ta juye rabi……
Sauran kuma ta zuba a bokiti ta kai ban daki……

Jaririyar ta amsa daga hannu Umman tace "Umma ki tashi kije kiyi wankan na kai maki ruwa a bandaki……"
A Hankali tace "Nagode ……"sannan ta mike ta fita tayo nata wankan……Jaririyar ta saka cikin ruwan ta gasata sossa……

  Tana gama mata wankan ta ladeta cikin kallabinta tana kallonta ,Tausayin yarinya ya kamata sosae ganin ko Dan kamfai bata dashi,Daukarta tayi ta goya sannan ta fita daga gidan……

Gidan mai unguwa ta shiga ta tambaya ko akwae Surfe,Cikin sa'a suka bata masara tiya goma suka ce a surfa zasuyi tuwon sadaka da ita ……

  Haka ta ja masaran ta koma gida lokacin mutanen gidan sae karin kumallo suke ,Bukkarsu ta nufa ta iske Umman a zaune ba'a kawo mata komae ba ,hawaye taji suna niyyar zubo mata ta fita da sauri tana tambayar Jummai ina abun karin kumallon su……
Matan gidan suka dauki sowa suna fadin "Ashe har abinci gareku bayan abun kunyar da kuka dauko mana "
Wata ta amshe da fadin "Shi kwarton uwar taki bai kawo maku komae ba?ko bai san ta haihe mashi diya ba ?

  Jummai ta amshe da fadin "Ke nifa ban yarda da yadda Ard'o ya k'irba yarinyar nan ba! don wallahi kadan yake saka tabaryar a ciki ko diyar bata tabawa"
  "Nima wallahi abunda nake son fada kenan,kawae raina mana wayau yayi don ya fahimci shegiya ce……"

Inno dake tsaye tana jinsu ta kira lauratu ta mika mata nata abun karin kumallon ta juya a sanyaye ta koma dakinta ……
Lauratu kam Umma ta kaiwa abun karin kumallon ta juya zata fita ta kira ta tace tazo ta zauna taci ……
Duk da irin yunwar da take ji murmushi tayi tace "Nasha nawa Umma"

Ta dade tana kallonta sannan ta gyada mata kai tana share hawayen da suka zubo mata ,Da sauri lauratun ta fita ta fara surfan masarar ……
Kafin rana ta take ta gama surfewa har an bata kudinta naira d'ari ……Jaririyar ta kwanto tana fadin "Umma ki bata abinci yanzu zan fita da ita……"

  Cikin sanyin jiki tace "Ina zaku je Lauratu?
  "Umma dan kamfai zan sawo mata da riga a Gwadabniya nan garin ba'a siyarwa……"

  "Ina kika samu kudi?
  "Umma surfe nayi yanzu"ta fada tana rike kafar Jaririyar……
Shiru tayi tana kallonta har sae da jaririyar ta dauke kai daga MaMan sanna lauratun ta dauketa suka tafi……

【】

*M*a'aruf yana isowa aka bashi Guard mace sannan suka nufi Ward din cikin HLuxur……,Focal person suka dauka sannan suka nufi Gwadabniya……Ganin yarda suke keta daji ya sashi sakin tsaki lokaci lokaci ,Bai taba tunanin akwae mutanen da ke rayuwa ba a wannan dajin ……
Saukin suma Hluxury ce ba'a cika gane wahalar tafiya da ita ba don bata raina tudu da gangare ……
Gidan Mai unguwa suka sauka Ma'aruf na cikin motar bai fito ba .Mai unguwar ya leko yana washe jajjayen hakoranshi ,daga mashi hannu kawae yayi sannan ya bude motar ya fito Guard dinshi na a bayanshi……

  Gidn Malan Lado suka nufa tare da dandazon yaron da suka zagayesu……Har cikin bukkar ya Shiga ya dubashi sannan ya fito yana karewa ilahirin mutanen dake gidan kallo ……
Uban wari ke fita ta ko'ina ga ruwan da ya kwanta tsakar gida ……Dan karamin tsaki ya sake ja lokacin da Maitafasa ta iso gabanshi tana fadin "Yaro yaya kaga jikin nashi?dan Allah ku taimaka ya warke ko ya dauki Fansa a kan cin amanar da matarshi ta mashi ……"

Banza ya mata ya juyar da kai gefe guda tare da fita daga gidan suka tsaya jikin motar yanawa Focal person magana ……

Lokacin Lauratu ta iso garin tana hango dandazon yaran da matan aure da itama ta kutsa kai cikinsu ta tsaya gaban Ma'aruf din tana sauraren abunda yake fada duk da dai ba ganewa take ba saboda mafi maganarshi turanci yafi yawa ……

Uban Ihu Jaririyar ta saki tana kuka …
Kallonta yayi ya dauke kai saboda baya kaunar kuka yana fadin "Bar nan gurin……"Fuska a daure

  "Ina Saurarenka ne Bature……"ta fada tana jijjiga yarinyar,Cigaba da kukan jaririyar tayi tana mutsu mutsu a bayanta ……Kukan ya fara isarshi cikin tsawa yace "Shut up ki bar nan gurin……"

  Dariya tayi tace "Ba sunana Shutu ba Sunana lauratu!yar kanwata kuma Hafsatu……"

  "Hafsah……"ya fada yana kallonta "Kawota mu gani……"ya karashe maganar tare da mika mata hannu

Da mai unguwa ake kokarin kwanto yariyar tare da mika mashi"Me yasa ba'a saka mata kaya ba?ya fada idonshi na kan yarinyar……

"Bata dasu Bature shegiya ce ita ce warda Uwarta taci amanar mijinta da ka dubo yanzu……"Cewar mai tafasa sannan ta kalli lauratu tace "Karbeta ki bar nan tun kafin na fasa maki kai……"

  Fitinannen kallo ya watsawa Mai tafasar sannan ya fito da kudi akalla sunkai 50k ya mikawa Focal person din yace "Ka sayar mata duk abunda ya dace……"Mikawa lauratun ita yayi ya bude mota ya shiga Sannan Focal person din ya karbo sample Urine din da akace a kawo suka shiga motar suka tafi ……

  Mai tafasa da sauran mutanen garin Mamaki ya hana su magana har sae da suka bar ganin kurar motar su sannan Mai tafasar ta juyo da niyar Zazzagawa Lauratun ruwan masifa amma ta nemeta ta rasa……

Lauratu kam bayan gida ta zagayo ta shigo ta karare ta shige bukkar Malan Lado ……Kwance ta iskeshi kamar kullun idonshi a rufe sae dae hawayen dake zubowa……kwanto jaririyar tayi ta daura mashi saman kirji ,ya dube ido da sauri yana kallonsu ,lokaci guda ya fara gyada kai yana murmushi dake dauke da hawaye yana kallon yarinyar ……
Jikin lauratun yayi sanyi tace "Baffa yarinyar ka ce ko?

Gyada kai yake da sauri yana murmushi ,Itama murmushi tayi ta janyo kwanon furan da ta gani gefe tana fadin "Baffa ka sha?

  Girgiza mata kai yayi yayin da murmushin fuskarshi ya bace ,Shiru tayi sannan ta dauke diyar daga jikinshi ta dago kanshi tana bashi furar……
Sae da yasha sossae Sannan Jaririyar ta tsangare da kukan da yasa Mai tafasa da kumdum suka nufo bukkar suna fadin "Wane Shegene anan ciki?

Kwantar dashi tayi da sauri ta dauki jaririyar ta fice ta yar kofar dake bayan bukkar ta bi ta karare ta fita ,Suna shigowa suka ga babu kowa……

Kundum tace "Lado hala wannan Shegiyar yarinyar ce ta shigo……"
 

*HAJJA CE👈*
  &
*FEEDOHM💞*

ABINDA KE B'OYEWhere stories live. Discover now