ABIN DAKE B'OYE Page 73-74

2K 157 1
                                    

💧💧 *ABUNDA KE B'OYE……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      💧

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_

        *_NA_*
  *_FEEDOHM💞_*
&
*_K.A.S.Precious HAJJA CE_*👈

       *SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
*Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*

          Page *73-74*

      "Zo nan Ina Auntyn ki……?

  Ba tare da ta juyo ba tace "Tana kitchen……"

  Tabe baki yayi yace  "Zo ki zauna anan ……"

A Hankali ta dawo ta zauna a kasa tare da tallabe yarinyar ta sunne kai k'asa……
  Cike da zolaya yace " Baki fad'a man me na ci ba a waje……"

  Still rufe fuskarta tayi da hannu ……
"Kunya ko Hafsah!Good……Gobe zan mayar dake gida kin ji ko!ko a bari sae wani month din bakya son komawa?

Da sauri ta girgiza kai tana fad'in "Ina so mana……"

Dariya yayi mai sauti yace "Kenan kin yarda ki koma ki ci gaba da cin tuwo kullun……"
 
Murmushi tayi kanta na k'asa !Sumayya ta shigo ta zauna gefenshi tana fad'in "Yaushe ka dawo ban ji ba……"

  Kallonta yayi a hankali yace " Kina can kitchen dama ya zaayi kisan na dawo!Me kike had'a mana naji kamshi ya cika mana gida……"

Far tayi da ido tare da kama hannunshi sannan tace "Daddawa nake soya mana zamuyi kwad'on wainar da Madre ta aiko mana d'azu……"

  Mamaki ya hanashi magana na tsawon yan mintina sannan yace "Kwad'on Waina a gidannan Sumayya a matsayin Lunch dina?

  Fari ta kuma tace "Ai yaji albasa……"

  Tsaki ya saki da karfi yana fad'in "Ba zanci ba gaskia!Zan kai K'arama tawa Madre bankwana ki samar man abunda zanci kafin na dawo……"

  Turo baki tayi tana gunguni!banza ya mata yana fad'in "Bata ita ki dauko Hijab Hafsah…"

A Hankali ta juya ma Sumayyan baya ta cire yarinyar amma sae cewa tayi "Ki je da ita mana……"

  Kallonta yayi ya tabe baki had'e da girgiza kai yace "Idan ta maki yau gobe bara ki ganta ba……"

  Da sauri ta kalleshi tace "Ina zata……?

  Kai tsaye yace "Gidansu……"tare da mikewa tsaye……shiru tayi tare da binta da ido kamar mai nazarin wani abu yayin da jikinta yayi sanyi sossae……

  Bata ce komae ba ta shiga daki ta dauko Hijab suka tafi!

  Bankwana sukayi da Madre sossae ta hada mata yan kayan sawa tare da chocolate masu yawa tace ta bawa yan garinsu tsaraba sannan ta tsinto tsufaffin kayanta tace ta bawa yan garinsu suma!Ita kanta Madre din daurewa kawae take amma har ga Allah bata son K'arama ta tafi!lokacin da ta rakosu harabar gidan ta bawa Ma'aruf 100K din da Abban ya bawa K'arama tace ya biya da ita super market ya mata sayayya!Ma'aruf din yana lura da Madre da ta juya ta goge hawayen da suka zubo mata!A sanyaye ya amshi Udutti dake ta tsala kuka ya shiga motar yayin da K'arama ta shiga itama tare da hade kai da guiwa ta saki kuka mai sauti……

  Driving kawae yake amma sam kukan ya hanashi natsuwa!Cikin lallashi yace "Bakya so ki tafiya ne Hafsa……"

  Girgiza kai tayi har lokacin tana duke tace "Ina son ganin Ummata da yaya Lauratu!kuma bana so na bar Madre na kuka……"

ABINDA KE B'OYEWhere stories live. Discover now