ABINDA KE B'OYE Page 15-16

2.3K 173 2
                                    

💧💧 *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      💧

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_

        *_NA_*
  *_FEEDOHM💞_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CE👈_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
*Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*

    Page *15-16*

*M*aganganun Madre su shigesu sosae ……Sun dade suna waya sannan ta yanke , Lokacin sumayya na zaune kusa da ita ta kalleta tace "Madre wae Yaya Ma'aruf bara yayi aure bane……?

Dariya Madre tayi sannan tace "Wane irin Aure Sumayya?Duka Ma'aruf din nawa yake?He's 24yrs idan wannan month din ya mutu,Kawae Allah ne ya bashi sa'ar rayuwa……"

Bata Fuska tayi tana fadin "Amma Madre ai yana da abunda zai rike mata yanzu!kuma wallahi baki ga yarda yan mata ke sonshi ba a waje,don babu wanda zaice bai kai 30years ba gaskia a nema masa yarinya cikin family dinmu yayi aure kawae……!

  Dariya kawae Madre din tayi ba tare da tace mata komae ba……Ita kam bara ta kashe danta ba tun yana yaronshi tafi son shekarun shi su kai 32 sannan yayi auren don lokacin ta tabbata ya san yarda zai zauna da Mace ……

  Sumayya kam haushi taji da Madre bata yarda da zancenta ba Ita idan san samu ne tafi son da ta gama secondary School a mata aure dashi tunda yanzu SS3 Take domin a tsarin rayuwarta babu batun cigaba da karatu……

*Ma'aruf*

Ma'aruf Muhammed Ma'aruf shine cikakken sunanshi !D'and'a ne Ga Alh M Ma'aruf da Hajiya Hafsat Madre!Suna Zaune a garin Kaduna Unguwar Sarki Mahaifinshi Babban Dan kasuwane yana da company a Ibadan da suke fitar da sweet ta Splash sannan yana da wani a kaduna da suke buga robobi……Yaransu biyu Maryam ce babba sae Ma'aruf !amma ita tayi aure har da yaranta biyu……Ya tashi cikin gata da kulawa tare da tsantsar addini daga gurin iyayenshi da yar'uwarshi ,Yana da shekara Sha bakwae ya gama secondary school dinshi cikin shekara daya ya samu admission kasar Egypt cikin Cairo anan yayi karatunshi tsawon shekara 4 bangaren Laboratory sannan ya dawo Nigeria! Allah ya bashi sa'ar rayuwa ya samu aiki a World health organization a matsayin WHO Consultant……!
 
  Sumayya yarinyar k'anin Madre ce tun bayan rasuwar Babanta ta dawo hannun Madre da zama, tun lokacin da ta dawo ta dauki Son duniya ta daurawa Ma'aruf  bata da wani tunani sae tunanin ta aureshi……Shi kanshi Ma'aruf din ya sani saboda tasha fada mashi amma ko kallonta bayya yi……!

【】
 
  Ma'aruf Bayan Madre ta yanke wayar Ya dauki siririn farin glass dinshi ya saka sannan ya janyo laptop ya duk'ufa yana yan bincike ……

Focal person din kuwa suna rabuwa da Ma'aruf LGA meeting suka shiga sae da suka gama sannan ya shiga central market ,yan kayan jarirai ya sawo mata da basu wuce na 10k ba sannan ya dawo ya kawo ma mai ungua yace ya kai masu ……

Mai ungua ma sae da ya tsintarwa yarinyarshi sannan ya taka da kanshi ya kaimasu ,Lauratu ta amsa tare da godiya sannan ta kaima Umman nata……

《》《》《》

Rayuwa su Hafsuwalle suke cikin k'yara da tsangwama Dukkan gidan babu mai zuwa kusa dasu hatta yara k'anana an hanasu zuwa inda suke zaune ……Sae dae kullun Lauratu zata dauki kanwarta suje Gurin Baffa a sace ba tare da kowa ya sani ba……

Haka Hafsuwalle ma takan Saci jiki taje ta gano mijinta ba tare da kowa ya sani ba wani sa'in sae taje take bashi abinci sannan ta gyara mashi inda yake kwanciya……

  Abinci da zasu ci ya fara gagaran su don Sau daya ake basu abinci a rana shima sae da daddare kuma ko Lauratun bara ya isa ba bare su biyu……don haka Hafsuwallen da Lauratu suka dage suna surfen kudi……da kudin suke samu su sayi gero da yar masara suyi abinci duk ranar da basu da abunda zasu ci haka zasu wuni da yunwa ko da za'a zubar da abinci gabansu……K'ara ma Inno wani sa'in tana kula dasu ……Abunka ga Uwa sae ta fara tausayinsu ta je ta samu Ard'o tace ya masa kamata suje gidansu Malan Lado suji me ake ciki……

  Bai musa mata ba ya shirya shi da Hafsuwallen da jaririyarta suka tafi ……Suna shiga garin yara suka taresu da "Ga Gayyar Tsiya……"

  Ard'o Ya kalli Hafsuwallen a sanyaye jin abunda yaran garin suke fada ,Duk'ar da kai tayi k'asa tare da gyara goyonta ,Cikin k'ank'ani lokaci mutane suka fara fitowa daga gidanjensu don ganin su waye Gayyar tsiyar ……

  "Lallae Gayyar Tsiya ……"Cewar Kundum tare da komawa cikin gida ta samu Mai tafasa Da ke zaune tana tsige tafasarta tace "Abun kunya baya karewa su Hafsuwalle "

A Zafafe Mai tafasa tace "Ke kundum ni bana son munafunci!dan kinga bana son ko jin sunan Hafsuwalle shine da gulmarki ta motsa sae ki dinga k'ira man ita ……"

  Watsa hannu tayi tana fadin "A Hayye ……Maida wukar Mai tafasa!Hafsuwalle da tsohunta na gani sun nufo gidan ga Shi yasa na zo na fada maki don ki tanadi kalamun ci masu mutunci……"

  Zumbur ta mike tare da hankad'e kwaryar tafasar ta zube kasa tayi waje tana fadin "Da kwarankwatsa yau garinnan sae nayi kisan kai !Banda dibar Albarka bayan cin amanarmu da akayi shine za'a kwaso kafufuwa ace za'a shigo mana gida!Uban me ya kawoku kai kuma tsohon banza ka kwaso lauyayyen wuyanka kamar rakumi ka taso yarinya gaba me zaku fada mana!

  Tsaye sukayi kamar an dasa kara suna kallonta har ta karaso gaban Ard'o ta tsaya tana watsa hannuwa baya"Na ce me ya kawoku kuma? ……Lallae Ard'o ka cika babban banza tunda har baka ji kunyar shigowa garinmu ba ……Da kwarankwasa kunji kunya maciya amana kawae……"

Danne Fushin shi yayi yana fadin "Kiyi hakuri Tsohuwa mu shiga ciki sae muyi magana……"

Hannunta ta watsa saman fuskarshi"Anki a shiga d'in Tsohon kawae marasa mutunci watsatstsu masu gadon abun kunya!Mu shiga ciki kayi mani me yan iska?wallahi Ard'o ni da ku sae rashin mutunci a tsakani "

Juyawa yayi a fusace yana kallon Hafsuwalle "Kinji Kunya Hafsatu kin saka an wulakantani a inda ba'a isa ba, tur dake!

Kuka ta saki da karfi tana girgiza mashi kai "Ka Gafarceni Ard'o Wallahi ban aikata abunda suke zargi ba"

"Tur Dake Hafsatu!Me yasa lokacin da Ladon ya nemeki baki nuna mashi aibun da abun zai haifar ba kin biye mashi kin saka an wulakanta mu !kin haifar mana da abun kunya a zuri'armu wa zai yarda d'iyar Lado ce ……!

  Kundum tace "Can ta matse maku munafukai Sae a k'ara gaba Don Mai tafasa ba sakarai bace da zata karbi Shege!

  "Bana son fa munafunci Kundum idan ina tsiyata ki daina saka man wagegen bakinki……!Mai tafasa ta fada tana watsa hannu gaba sannan ta shige gidan tana fadin "Wani kukan ma Sai ranar da Ladona ya warke……"



*HAJJA CE👈*
   *&*
*FEEDOHM💞*

ABINDA KE B'OYEWhere stories live. Discover now