ABIN DAKE B'OYE Page 79

2.4K 165 0
                                    

💧💧 *ABUNDA KE BOY'E……*
        《Almost True Life Story》

                   🍁🍁
                      💧

© *HASKE WRITER'S ASSO*
_Home of expert & perfect writer's_

        *_NA_*
  *_FEEDOHM💞_*
   *&*
*_K.A.S Precious HAJJA CE👈_*

*SADAUKARWA……*
*HAFSAT* 《Ummana》
*HAFSAT* 《Miss Xoxo》
*Da dukkan masu suna HAFSAT dake duniyarmu*

     Page *79*

Sunkuyar da kai Umma ta sake yi tana matsar hawaye, ya zata yi dole ta yadda domin zaman K'arama a gurin su shine mafi jin dad'inta da kwanciyar hankalinta, cikin rawar murya tace mai,

  "Mun gode Ma'arufu Allah ya saka da alheri ya baku zaman lafiya da duka matan naka, nasan baka son auran K'arama dole aka yimaka kayi hakur...."

Saurin katse ta yayi ta hanyar cewa, "a'a Umma ki dena cewa haka, dama can Allah yayi Hafsat mata tace so babu yadda zanyi ki dena damun kanki."

Mik'ewa yayi tare da zaro 10k ya ajiye mata kusa da kafarta dan yasan idan ya ce sai tasa hannu toh zasu d'auki lokaci shi kuma sauri yake dan jirgin karfe tara da rabi zai bi, da sauri yabar rumfar jin zata fara mai magiya akan kud'in daya bata,mota ya shiga drive yaja shi zuwa airport be dad'e ba jirgin su ya lula.....

*******

Gidan Madre ya fara zuwa, yana shiga yaji tsit ba kowa a parlor sai ya nufi kitchen dan ya san ba'a raba Madre da shiga kitchen yana zuwa nan ma bata nan. Kanshi ya girgiza sannan ya nufi upstairs nan ya fara jiyo muryar Madre na waya, a hankali ya murd'a handle d'in ya bud'e ya shiga, zaune ya tarar da Madre a bakin gado waya take da Yaya Maryam tana bata labarin auran Ma'aruf da K'arama.

   "Bari kawai Maryam ni kaina mamaki nake sai dai ba'a mamaki da ikon Allah,

   "Oho ni kaina ban san ta inda za'a fara sanar mata ba kinsan inajin tana bawa kawayanta labari akan duk ranar da Yaya Ma'aruf yayi mata kishiya haka tace ko ita, ko shi ko amaryar sai sun bakunci lahira, bari kawai Maryam ni kaina bansan yadda zanyi da Sumayya ba bari anjima mayi wayar kin ganshi nan ya dawo..."

Katse wayar tayi tana kallonshi duk yayi wuri-wuri kamar marar gaskiya, shagwab'e fuska yayi kamar yadda yake mata idan yaga suna waya da Maryam kamar zasu cinye juna cikin halin gajiya yake fad'in,

   "Madre nayi tafiya na dawo amma kinyi min banza sai biyewa ya Maryam kike ina shan wahala."

Dariya tayi tana k'okarin bashi amsa sai ga K'arama ta shigo d'akin jikinta d'aure da towel tayo wanka kunnanta duk kumfa,kallon ta suka yi daga shi har Madre baki bud'e yayin da ita kuma tana ganin Ma'aruf ta b'oye fuska alamar kunya ta k'arasa wajan Madre tana cewa,

    "Nayi wanka."

    "Kinga kunnanki kuwa Hafsat? Duk kumfa sai da nace ki bari nazo nayi miki amma waike kin girma bakyaso harda ce min yanzu Udutti za'a dinga yiwa wanka gashi nan ai duk baki fita ba."

Madre ta fad'a tana janyo ta jikinta tare da d'akko cotton bud tana goge mata kumfar, K'arama kuwa bata juyo ba ta fara k'ok'arin gaida shi.

    "Uncle ina kwana ina Udutti zanje wajanta."

Yana kallonta ya tab'e baki tare da cewa "ke yanzu duka-duka guda nawa kike da zaki ce an dena yi miki wanka? Lallai ma toh gashi nan duk wankan beyi kauba...."

Ba tare da ta damu ba ta kuma kallon Madre "Ina kayan da zan saka uncle ya kaini wajan Udutti...?!"

    "Gasu nan akan gado."

ABINDA KE B'OYEWhere stories live. Discover now