DUNIYARMU-37

395 17 0
                                    

DUNIYARMI.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA TALATIN DA BAKWAI.

Lamarin Adam dai yanzu sai du'a'i kawai domin gabadaya ya susuce ya zama tamkar wanda ya shekara yana hauka cikin duniyarsa sambatu kamar wanda aka bude kwanyarsa aka zuba masa kullum aikin kenan duk wani mazantaka da kwanji da aka san namiji dashi duk sun zabge a jikinsa duk wani isa da ji da kai da kwalisa sai ka rantse bai taba yi a duniyarsa ba duk wani kyau da takama da kudi da yake ji da su suna yi masa rana duk yanzu sun gajiya wajan samo masa abin da yake so duk ranaku da ya samu a baya yayi amfani da su yanzun kam babu so yana nema amma sai fallewa sukeyi suna guduwa domin ba su ga wajan zama gareshi ba iyayensa kan sa yanzu abin a tausayawa ne musamman Alhaji kabeer da ya kwallafa rai da makahon so gareshi ba ya ganin laifinsa ko aibun sa in ya aikata ba daidai ba ya fifita ɗan nasa fiye da kowa cikin duniyarsa sam ba ya tunanin halin rayuwa komai zai iya sauya kamar yarda ZAMANI YA CANZA cikin duniyar nan  rayuwar Adam gabadaya ta sauya ya rasa gane mai ke yi masa dadi cikin duniyarsa kullum maganar sa daya ne muradinsa abin da zuciyarsa da ruhinsa ke so abin da idanuwansa ke son gani kullum bakin sa cikin furucin son ganinta ne ya rasa zai ganta a zahiri kullum gizo take yi masa cikin duniyar rayuwarsa amma zahiri ya kasa ganinta ta wanzu a zahiri sai dai ba da kayan alheri ba amma kuma ya ji dadin ganin nata a hakan zai so ace ta kasance dashi ko da kuwa zata dinga yankar namansa ne zai iya zama da ita da wannan bala'in da yake fama dashi na ciwon zuciya da ruhi gami da CIWON RAI wanda bai san maganinsa iyayensa ma ba su san maganinsa ba kudi sun ƙasa yi masa rana is da iko gami da gadarar shi wani duk ba su yi masa amfanin cikin duniyar tashin hankalin da yake ciki ba.
Alhaji kabeer shi kasan kasancewa yayi kamar zautacce kullum yana har gidan Mansoor domin kuwa ganin da yayi yana kokarin rsa ɗansa daya tilo da ya mallaka cikin duniyar nan a baya lokacin da Bahijja ta so daukar ran ɗan nasa ya yi fushi akan ɗan sa ko zai mutu ba zai aureta ba amma ganin ɗan nasa yana kokari ransa hakan ya kara tsoratar dashi yaje gidan Mansoor yafi a lissafa amma ba abin da yake gamuwa dashi sai cin mutunci da cin fuska don akwai ranar da su kusan dambacewa dashi da Mansoor a kofar gidan nasa da kyar a ka shiga tsakin su ganin tashin hankali ba zai haifar masa ɗa mai ido ba ya shiga rarrashi da alkawarin duk abin da yake so zai yi masa wannan kalaman sun yi matukar baiwa Mansoor haushi duban sa yakeyi cikin ido sosai dauke da rainin hankali.
"haba Alhaji ka dube ni sam da kasa kasan dai dangina ma basa alaƙa da rashin babu balle ka dauko wata banzar dukiyarka kace zaka yaudare ni da ita kai ƙsan abin da ba zai taba yuwu bane ko a mafarki".
"Mansoor na hadaka da Allah da annabi na hadaka da iyayenka ta taimaƙa ka ceci ran ɗana".
Mansoor ya kan dube shi cikin salon raina kalamansa.
"da yake ran ɗan naka na hannu dole ka gayyaceni na cece shi malama kasan Allah zan yi maka rashin mutunci in har baka rabu dani ba ai ba uban wani ya sanya dan naka ya kamu da son taba".
Irin bakaken maganganun da suke shiga tsakanin Mansoor da Alhaji kabeer kenan domin yayi hakurin yayi kawaicin amma bai ga alamun Alhaji Kabeer zai sakar masa mara yayi fitsari ba shiyasa ya juya aƙalarsa izuwa salon rashin mutunci aiko ya na shuka masa rashin mutunci sai dai da alamun zuciyar Alhaji Kabeer tayi laushi sosai wacce ba ta iya aikata komai na daukar fansa saboda irin MAKAUNIYAR SOYAYYAR da yake yi wa ɗan nasa duk ta rufe wani kwajinsa da hanzarinsa lokaci da dama haka zai dawo jiki a sanyayye nan Adam zai tambayeshi ina take tun yan cewa ta na nan zuwa gareshi har ya gaji da kirbwa ɗan nasa karya Hajiya Laila kuwa tun zuciyarta na bugawa da halin da ɗan nata yake ciki har ta hakura ta mikawa Allah lamarin domin ta ga abin akwai wani BOYAYYEN SIRRI cikin sa wanda su kan su sun ka sa gane wa maganar Bahijja na amsata kuwwa so sai ta kalmar 'Fansa na zo dauko' ta tabbata akwai abin da ɗan nata ya aikata mata kuma Allah ya makala masa son ta wanda zai iya zama ajali a gareshi domin ita tun da take ba ta gani So mai dauke da hauka ba irin wanda ɗan ta ke yi wa macen da ta nemi ransa tabbas ta kara gasgata lamarin da zuciyarta ta dade tana zargi akai. Duk da hakan tana matukar tausayin ɗanta tana jin son sa ranta tana jin kaunar sa tun daga kasar ruhinta sai dai hakan ba yana nufin ta nuna fifiko da son zuciya kamar yarda ubansa yake nuna wanda hakan shima ya je fashi cikin hali na rashin natsuwar rai ya hana shi tafiyar da lamuransa yarda ya kamata sannan ya jawo masa cin mutunci da zarafi a gun yaron cikin sa rayuwa kenan. Lokaci da yawa in ta zauna tunane tunanan dake ɗawainiya da ita kenan idaniyarta tayi ta zubda hawaye cikin rashin abin yi da mafita.
Yau ma kamar ko yaushe suna zaune jigun jigum shi kuma Adam ya ishe mutane sambatu an dakara masa Allurar barci an samu yayi hakan ne ya sanya su samun 'yar natsuwa.Tk ne ya shigo dakin a hargtse kamar wanda aka jeho daga sama kallo daya zakayi msa kasan baya tare da hayyacin duk kansu suka dubeshi cikin yanayi na meke faruwa numfashi ya shiga ajjewa kafin ya saita kan shi ya dubi Adam da yake ta barci wanda ba a son ran sa yake yin sa ba sai da aka hada masa allurar gyada kai yayi cikin yanayi na tausayawa kafin ya juya ya kalli Alhaji kabeer sannan ya kalli Hajiya Laila irin kallon da yake yi musu ya dan fadar musu da gaba da saurin cikin neman ba'asi Hajiya Laila tace,
"Tukur lafiya kuwa na gan ka duk a hargitse kamar wanda ya kwato daga bakin kura".
Gyada kai ya shiga yi yana faman motsa baki amma maganar da yake son yi ta ki fitowa sai da Alhaji Kabeer ya sake tararsa,
"Tukur kayi magana mana wannan wani irin shiririta ne ai sai ka sakamu cikin yanayi kuma na rashin dadi".
Nan ba bai yi magana ba nan suka shiga kallon kallo a tsakaninsu kafin Tk ya kokarta dubansu yace,
"wai ashe yarinyar nan yar Dorayi ce yar gidan Alhaji Nasuru mai tireda".
Zumbur duk suka mike suna duban shi kamar wanda suka ga BAKUWAR FUSKA mamaki tu'jibi ya karyarmu su da duk wani hanzarin su sun ko gasgata maganar har zuciyarsa Hajiya Laila ce tayi kokarin dubansa zuciya na harbawa,
"wai kana nufin 'yarsa Bahijja da tayi Aure a garin Minna".
yanayin da tayi magana ya sanƴa Tk mutuwar jiki domin yaji ta ambato aure wai Bahijja na da aure anya ita ce kuwa.
"nidai 'yar an sanar dani yar gidan ce domin na bibiyeta sosai tun lokacin da ta shigo nan ta tayar mana da hankali na shiga bibiyar ta han nagano gidan yanzu haka tana can kuma an tabbatar min 'yar gidan ce Bahijja".
Hajiya Laila sakin baki tayi domin har yanzu ba ta gasgata lamarin ba domin ita dai ta san 'yar Alhaji nasuru guda daya ce tilo kuma tuni akayi mata aure ba ma a nan kano ba can jahar Neja Minna aka kai to ya akayi hakan ta kasance anya ita ce kuwa girgiza kai ta shiga yi cikin rashin yarda da lamarin.
"ba ita bace Tukur...".
Alhaji da tunda ju yake jujjuya maganar ya tare da sauri.
"akan me zaki ce ba ita bace kika sani ko auran nata ya mutane ".
Sakin baki tayi tana kallon ikon Allah yarda Alhaji ya hayayyako ta dai kace ita ta kar zomon girgiza kai tayi kafin ta tsuke bakin ta don ta ga lamarin na Alhaji har yanzu bai bar halinsa.
"kai Tukur ka tabbata 'yar gidan ce?".
Tk ya gyada kai alamun eh nan Alhaji ya mike yace "tashi muje in kuwa yar gidance ai ta kwana gidan sauki". yana magana ya na mikewa ya dauko babbar rigarsa dake yashe can gefe Hajiya na ganin haka ta mike ita ma.
"haba Alhaji daga jin magana shikenan kuma zaka dauka ba tare da kayi bincike ba ya kamata ace kayi wani abu domin ni dai nasan Bahijja tayi Aure kuma ba nan jahar aka ajjeta ba...".
Wani kallo yayi mata wanda ya sanyata saurin gimtse bakinta ya juya wajan Tukur da shi yake ganin rawar kafar Alhaji akan lamarin ba abin da ya iya cewa haka Alhaji yasanya shi gaba akan sai ya kai shi gidan ba yara ya iya haka suka fito daga cikin asibitin jikinsa a sanyaye su ka shiga mota Tukur ya ja Alhaji dake gidan baya a hakimce sai faman zare idanu yake yi shidai burin sa kawai su isa yasan Alhaju Nasuru farin sani makuwa ya san ba zai samu matsala ba ko da kuwa ya samu zan yi amfani da kudi da duk wani karfi nasa domin ya san yafi Alhaji nasuru karfi ta ko ina a wannan tunanin zucin da yake yi wanda yake ganin zai haifar masa ɗa mai ido suka isa Dorayi ba su zarce ko ina ba sai gidan su Bahijja kofar gidan sukayi Parking Alhaji Kabeer ya fito sai faman baza babbar riga yakeyi shi wai mai mutunci da girma tsirarun mutanan nayin dake zaune sai kallon sa sukeyi cikin mamaki ganin Alhaji kabeer kofar gidan talaka wanda wanda shi da yanuna sam ba ya son talaka ba ya rabarsa ko sha'ani akeyi sai dai na masu farcan susa ba wanda bai san Alhaji kabeer cikin unguwar ba ba su taba gani ya zo gidan wani talaka ba da sunan biki ko jaje ba amma yaushi yazo tabbas akwai abin mamaki.
Tk ya tura yayi masa sallama da mai gidan ba musu ya isa ya dankara sallama amma bai ji an amsa masa ba sai da yayi ajere sannan yaji an amsa ance ana zuwa nan ya dawo kusa da Alhaji ya tsaya yana sanar dashi abin da akace yatsine fuska yayi gami da yin ƙwaba ba abin da yake zantawa a zuciyarsa sai wai shi ne ya zo gidan wani wai da yashi komai da komai amma ya zo neman wani wani abu gurinsa tabbas wannan zubda girma ne amma bakomai in dai zai samu abin da yake so ai shikenan dalilin ɗansa ne yake yi komai haka. muryar Alhaji Nasuru ce ta katse masa tunani in da yake tambayar Tk ko su suke sallama dashi tk ya gyada kai yanayin da ya ga Alhaji  nasuru ya tafke fuska kamar tunda yake a rayuwa bai taba wata aba wai ita dariya ba duban su ke yi tun daga kasa har da motar da sukayi msa parking kofar gida kafin ya dire kallonsa akan Alhaji Kabeer da yake ta faman fankama da shan kamshi shi ala dole nan mai mutunci ya zo gidan kasa dashi ba ya bukatar wani raini murmushin takaici Alhaji nasuru yayi kafin ya yi masa sallama da ta zame masa dole a matsayinsa na musulmi in ba don haka ba, ba abin da zai sak shi tsinka masa ko da harafi daya ne. A dakile ya amsa sannan ya dubi Alhaji nasuru
"dafatan kana lafiya wajanka muka zo".
Yanayin da yayi maganar cikin isasa isa ya baiwa Alhaji Nasuru dariya Tk kuwa faduwar gaba ya shiga yi domin in dai a hakan ne Alhaji yake tunanin za su samu biyar bukatar su aiko ba za su taba samu ba.
"ina jin ka mai ke tafe da kai?".
Ba tare da wata fargaba ba yace
"maganar tamu mai muhimmaci ce Alhaji Nasuru mu samu waje mu zauna..".
"a,a nan ma ya isa kayi maganar ka kawai".
Izuwa lokacin Alhaji nasuru haushin da yake dannewa daga kasar zuciyarsa ya fara turnukoshi in har Alhaji Kabeer ya cigaba da neman gaya masa magana zai nuna masa ba shi da wayo domin a wuya yake dashi don ya lura sam bashi da hankali cikin lamuransa ya na jin shi wani ne ba a isa a taka saba to zai nuna masa shi ba kowan kowa ne illa wamda bashi da tunani da karfin mallakar zuciyarsa ya sarrafa yarda ta dace.
"Alhaji Nasuru abin arzuki ne ya zo dani wato ɗan waje nane ya ga yarka yake so...".
wata irin zabura yayi gami da cilla wa Alhaji kabeer wani irin kallo wanda ya san yashi saurin katse zancensa mamaki haushi takaici bakin ciki duk suka tunkaro Alhaji nasuru lokaci guda zuciyars da kasar ruhinsa yaji sun shiga wani irin tashin hankali ma tsananci sai faman kartwa suke yi duniyar ya ji tana juya masa kamar za ta jirgitar dashi kalaman Alhaji Kabeer jin su kaye yi kamar ana kwara masa ruwar dalma jiki saboda tsabar zafinsu da kaifin bakin ciki da suke dauke dashi sai 'yar sa ɗansa ke so wannan wani irin cin mutunci da cin zarafi ji yake kamar ya shako wuyar Alhaji Kabeer amma ba zai yi haka ba domin shi yasan mutuncin kan sa amm duk da hakana ba zai hana shi ga ya masa magana ba.
"wa ya ce maka ina da 'ya har da zan auran da ita to ni bani da 'ya kowa ma ya gaya maka to ya fadi ba daidai ba..".
"a,a Alhaji Nasuru kar muyi haka da kai zancen arzuki ya kawo mu bana tsiya ba".
"na san na arzukin ya kawo ku shiyasa nima na zo muku da arzukin na lura ba ka fahimci abinda nace ba shi yasa".
Shiru ya gifta tsakanin su kafin Alhaji kabeer yace,
"ba kai bane mahaifin Bahijja?".
"ni ne mahaifinta sai akayi yaya kuma".
"to ita ɗana ya gani yake so shi ne na zo neman masa".
Wani irin kululun bakin ciki ne ya takora wa Alhaji Nasuru wuya ya shiga nishi kadan ƙadan ya na dubansa ji yake yi kamar ya kafta masa mari cikin ɗacin rai ya ce,
"ni 'ya tayi aure ba ni da wata 'ya da bata da miji".
Jin abin da yace nan da nan jikin su yayi sanyi Tk ya ji wat irin kunya ta kamata shi da ya tuno maganar Hajiya Laila ashe da gaskiyarta amma aka ki yi mata uzuri.
"Alhaji Nasuru yarona na cikin wani hali na tsakanin mutuwa da rayuwa tun da ya ga 'yarka ya kamu da son ta yanzu haka ya na kwance a asibiti sam bai san in da yake ba ina neman alfarmar ka don Allah ka yi wani abu akai ni nayi maka alkawarin komai kake so a wajena na zan baka shi".
Cikin takaici ya shiga duban Alhaji kabeer da irin banzayan kalamansa da yake saki kamar wani zautacce tabbas wannan mutumin ba shi da hankali sai yayi maganin sa kafin su rabu ya lura ba ya bukata su rabu cikin salama har shi zai duba yayi masa barazanar wani abun da zai bashi Allah ya sauwake aiko da yana yawa tsirara haihuwar uwarsa ba ya bukatar wani abu daga hannunsa balle kuma Allah ya rufa masa asiri sai shine ma ya so tona masa.
"Amma Alhaji me ke damunka wacce irin magana ce wannn nce maka 'ya tayi aure ko so kake yi naje na kaso auran nata ta zo ta auri ɗan ta tun da shi yafi kowa ni 'ya'ya na cikin duniyar na shi ne ɗa sauran 'ya'ya kuma duk daga sama suka fado. Ya kamata ka saita hankalinka tun kafin ya guje maka".
ya karasa yana kokarin barin wajan don jin zuciyarsa yake kamar zata bugu saboda tsabar takaici in yana kallon sa bai taba tsanar mutum tsana mai tsanani ba kamar Alhaji kabeer domin ya lura ya na da son kai da na zuciya cikin lamuransa in ba da dakikanci da jahilci ta yaya za ace mace na gidan auranta amma ka fara kokarin cewa a fito a aura wa danka saboda baka so ya shiga cikin wani yanayi saboda shi kadai ne ɗa cikin duniyar nan wanda iyayensa ke so suke son farin cikinsa.
Har ya kai kofa zai shiga Alhaji Ƙabeer ya kira shi cikin hanzari yana mai ambaton sunansa cak ya tsaya cikin bacin rai ya juyo ya dubeshi.
"ina sha dai nine mai 'yar ko to wallahi da ba ta da aure akan ta kai bari ma kaji Bahijja na nan a gida ba ta  da aure amma na rantse maka da Allah in shure-shure ɗanka ke yi ba zan taba aura masa 'ya ta ba domin masu mutunci da kima da sanin darajar dan adam ake haɗa alaƙa da su ba  irinka ba maras tunanin mai son zuciya da son kai  shi ɗan naka ɗan naka don bashi da kunya bai gaje ta ba ya rasa wacce zai so sai Bahijja yarinyar da ya lalata wa rayuwa ya jefa cikin kunci da takaici ya zama silar wargaza duk wani farincikinta da na iyayenta ya zam silar mutuwar rai mai matukar muhimmanci a gareta shi ne zai ce yana son ta haba Alhaji ka binciki kwakwalwar ɗanka domin na tabbata ba shi da hankali mahaukaci ne lamba daya".
Magangaunsa sunyi matukar firgita Alhaji Kabeer domin gabadaya yaji duniyar na juya masa ya rasa ma abincewa ya rasa inda maganganun suk dosa kawai ji yayi suna amsa masa kuwwa cikin kai cikin karfin hali da gayyato jarumta ya dubi Alhaji Nasuru dake kokarin shigewa gida.
"ban fahimce ka ba, ban fahimci inda maganganun naka suka nufa ba, nifa ba na zo nan bane don ka ci mani mutuncin harkar arzuki ce ta kawo ni gareka...".
"harkar arzuki".
Ya katse shi da fadin haka kafin ya dora da cewa.
"kai ba mutumin arzuki bane Alhaji kabeer sam ba ka dauki ko da daya daga cikin halin arzuki ba cikin rayuwarka ka ƙoya wa ɗan son duniya da kyale-kyalen cikin ta ka nuna masa mai dauke da yaudara ka nuna masa batattun abubuwa wanda za su bata msa rayuwa ba ka son laifin sa ka nuna masa ya taka uban kowa yana da damar hak domin ka daure msa kugu tunaninka dukiya da ka tara ta iya yi maka komai da kake so to bari in gaya maka BAYA DA KURA ka bari wallahi kuma bari na sanar da kai wani abu kaje ka tambaye ɗan ka wacece Bahijja Alhaji Nasuru ta unguwar su nasan zai tuna kuma zai san wacece".
ya na gama fadin haka ya tsartar da miyau ya fada cikin gida cike da kunar rai da tarin bakinciki da ya cushe masa zuciya.
shikuwa Alhaji kabeer rasa abin yi yayi jin furucin Alhaji Nasuru ya gama gasgatawa akwai wani lamari a boye wanda su ba su sani ba tabbas dole ya bincika domin hakan ne kawai mafita a garesu har da ɗan su da wannan rikitaccen tunanin kwakwalwar nasa ya ja jiki ya shiga mota Tk shi ma cikin jan jiki ya isa cikin motar domin ya ji komai kuma ya gasgata akwai wani abu a kasa boyayye da ba su sani ba cikin wannai yanayin suka ja jiki suka bar unguwar cike da fargaba da ta rarrabi cikin zuciya.
A bangaren Alhaji Nasuru yana shiga cikin gida ya ci karo da Bahijja tsaye cikin wani irin hali na tashin hankali domin tun da akayi Sallama da baban nata sam taji ba ta natsu da ko suwaye su ka zo ba yana fitata biyo shi ta laɓe.
Yanayin da ta ga mahaifin nata cikin yanayi na daci da takaici ya fadar mata da gaba kallon ta kawai yayi ya shige cikin dakin sa da sauri ta bi bayansa izuwa lokacin idanuwanta sun fara zubar hawaye tana shiga ta tadda shi tsaye sai faman safah da marwa yake yi dubanta yayi lokacin da ta shigo.
"Na lura mutumin nan bashi da hankali sam hauka ke ɗawaimiya dashi in har bai yi hankali ba wallahi zan bashi mamaki zan nuna masa shi ma talaka mutumin ne mai daraja da kima".
Yayi shiru yana mai da numfashi cikin tsananin bacin rain ya dora da cewa.
"na lura mafiya mutanan duniyarnan sam ba su san darajar ɗan uwansu ɗan adam ba son zuciya da son kai shi suka mai da abin a dole in ban da jahilci da rashin tunani har yana da kafar da zai dauko ya zo kofar gidana har yana da bakin da zai iya budewa yayi min magana har yana da idon da zai kalle ni kaicon wannan rayuwa kaicon wannan duniyar tamu ta wannan zamanin da wannan bakar rayuwar da ake yi aƙe tunanin za a zauna lafiya da wannan abubuwan kazantar da ake aikatawa cikin duniyar ake tunanin komai zai daidaita cin amana ha'inci cin zarafi keta haddi kashe rayuka ace su ne suka zama ado  DUNIYARMU cikin wannan zamanin aiko ba za a taba samun zaman lafiya ba in dai haka aka ce za a tafiyar da zamani".
Maganganu yake yi cikin zafin rai da takaici da tarin bakin ciki ba abin da yake hangi sai cin zarafin da akayi masa aka illa ta msa rayuwar iyali sannan kuma yanzu an zo ana neman ya ba yarsa ga wannan ya bata wannan wani irin rashin tsohon Allah ne? Idanuwansa sunnƙda sun yi jajir sosa ya dube Bahijja dake durkushe gabadaya ta gama firgicewa da zantukan mahaifinta domin ta tabbata duk abin da ya fadi haka yake.
"Bahijja wallahi ki kiyaye duniya na roke ki da ki ji kan kan ki domin duniyar nan da kike gani ba komai bane a cikin ta sai tashin hankali da ruɗin zamani Bahijja na roke ki don Alah karki koma rayuwar baya da kikayi kia dauki Ƙaddara a yarda ta zo miki ki rungumeta hannun bibbiyu".
Ba ta san lokacin da ta fashe da kuka ba saboda tausayin mahaifinta da halin da ta ga ya shiga domin ita kawai tabbas mahaifinta na son ta yana bukatar tayi rayuwa mai inganci ta yarda ta aminci iyaye abin tun kaho ne duƙ mutumin da bashi da iyaye cikin duniyar nan ba karamar a sara yayi ba musamman ya rsa kulawa irin ta su. Cikin yanayin kukan ta isa gareshi tana mai dafa kafafuwansa cikin rawar murya.
"in Allah ya yarda abba nayi maka alkawari har in koma ga Allah ba zaka sake shiga damuwa ba a dalilina".
Shafa mata kai yayi cikin jin natsuwar zuciya.
"shikenan Bahijja Allah ya inganta mana rayuwa ya bi mana hakkinmu agun wand suk cuce mu ALLAH YANA JI KUMA YA NA GANI".

It'x Kamala Minna.😘😘😘😘😘

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now