DUNIYARMU-38

426 16 0
                                    

DUNIYARMU.
NA

KAMALA MINNA.

BABI NA TALATIN DA TAKWAS

Jikin Alhaji Kabeer ba karamin sanyi yayi ba saboda kalaman Alhaji Nasuru da suke tayi masa shawagi akai gabadaya ya ji jikinsa ya saki zuciyarsa ta fara bugu cikin rashin hayyaci sai faman ajiyar numfashi yake yana mai sharce gumin da yake kwaranyo masa sai kace wanda yayi gudun ceton rai.
Tun da suka baro Dorayi gabadaya shiru ya kifta ta tsakaninsu kamar mutuwa ta shigo cikin motar haka suka koma tamkar kurame ajiyar zuciya kawai suke Tk shi kasan ba karamar kaduwa yayi ba domin ya tabbata duk maganganun Alhaji Nasuru za su iya zama gaskiya koma sun zama don ya daina kokwanto akan maganar ya san Adam zai iya aikata komai don ya san shi cikida bai din sa.
Sannu a hankali suke tafiya, har suka isa Asibiti Tk yayi Parking ya fito ya buɗewa Alhaji shima ya fito jiki a sanyaye kallon juna sukayi ba tare da sun ce kala ba haka Alhaji ya shiga gaba Tk na biye dashi har suka isa dakin da Adam yake zaune suka tadda Hajiya Laila kan Sallaya da alamun sallar azahar ta idar take lazumi so daya ta kalle su ta kau da kai domin yanayin da ta gan su aciki ya tabbatar mata da akwai abun da suka gamu dashi na rashin dadi.
Sai da ta kammala lazimin ta tayi addu'a ta shafa ta saki ajiyar zuciya ta juyo tana fuskartar su.
"Alhaji sannu da dawowa".
Gyada mata kai kawai yayi yana mai koƙarin cire Babbar rigar dake jikinsa wacce ta fara jikewa da gumi bayan ya cire ya dubeta.
"ya farka ne?".
"Eh ya farka ba ku dade da fita ba nan nasanar dashi kun tafi gidan su Bahijja".
Shiru ya gifta tsakaninsu kafin Ta dubi Alhaji ta dora da cewa,
"ya akayi kun sa me ta?".
"eh mun same ta, maganar ki dai ta tabbata Bahijja 'yarsa ce kuma ita tayi aure amma ina ga da alamun auren nata ya mutu domun ta na gida".
da sauri hajiya ta gyara zaman ta jin ance Bahijja auranta ya mutu ba ta ji dadin mutuwar auran ba domin ita ma ya mace ce kuma ta san mutuwar aure ga ya mace ba dadi gareshi ba amma kuma inta tuna warakar ɗan ta ne ta samu taji dadi nisawa tayi fuskarta ba yabo ba fallasa.
"Masha Allah yanzu ya ake ciki dafatan dai komai ya samu yarda ake so".
Cikin daci da rashin samun nasara Alhaji kabeer ya ce,
"an samu matsala sosai ma kuwa wacce in ba Allah ne ya kiyaye ba abun ba zai yi dadi ba bana tunanin abin zai tabbata".
Faduwar gaban Hajiya Laila ya karu ta dafe kai gami da zaro idanu.
"matsala kuma Alhaji me ke faruwa ne?".
nisawa yayi sosai kafin ya kokarta duban Adam da izuwa wannan lokacin ya fara motsi da alamun farkawa zai yi.
"ina tunanin akwai saɓani da ya taba shiga tsakaninsu da Adam wanda ya kasance ba na dadi bane".
'Innalillahi wa inna ilair raji'u'
Abinda ta shiga fadi kenan cikin zuciyarta lokaci guda taji tashin hankalin da take ciki yana hauhawa kamar farashi zuciyarta na zillo ji take yi kamar zata faso kirji ta fito jin irin bugun da take yi.
Kurrr tayi wa Alhaji da ido tana kallon sa yanayin da ta gan shi ya tabbatar mata abin ba sauki mutuwar arne.
Wani shirun ne yasake ziyartar sai saƙar zuci sukeyi suna juya lamarin a kwakwarwasu da zuciya Hajiya Laila kawai rashin arzuki take tsinewa domin ta san komai ya faru bakin halin Alhaji dana Adam shine silar komai shi yasa ake son mutum yake mutunci da sanin daraja ko a ina ne domin bai san abin da gobe za ta haifar ba sai ka raina mutum amma wata rana sai kaje wajansa a matsayin mai bukata.
Farkawar da Adam yayi ne ya dawo da su duniyar tunanin da suka fada nan fargabar su ta karu don sun san dole akwashe ta babu dadi dashi nan suka shiga kallon kallo a tsakanin su shi kuwa ganin su Alhaji cikin dakin ya san yashi tashi zaune yana faman cizon La66a kamar zai tsinke su daga jikin sa saboda wani irin azaba da raɗaɗi da yake ji a zuciyarsa har kasar ruhinsa.
"Dady ina take?".
Abin da ya kokarta fadi kenan kamar zai fashe da kuka.
Alhaji Kabeer ya taso daga in da yake zaune ya koma wajansa ya zauna ya na mai jaho shi jikinsa sosai yana mai bubbuga masa baya alamun rarrashi.
Kawai tunani yake yi ta yarda zan fara magana da ɗan nsa ba ya so ya fadi abin da zai tayar masa da hankali ko yaya yake amma kuma ya zama dole ya tambaye ashi alaƙarsa da Bahijja domin hakan ne kawai zai ba su mafita.
Duban Hajiya Laila yayi yana mai yi mata alamun da tace wani abu amma sai ta kau da kai ya juya ga Tk wanda shi idanuwansa na kan su gabansa sai faman dukan uku-uku yake yi domin ya gama hango tashin hankali da za su fada dan gaba kadan ba ta dadi za ayi ba rausayar da kai yayi cikin rashin abin fada  Alhaji kabeer ya nisa kafin ya kira sunan Adam cikin wani irin sauti mai dauke da rauni.
Yanayin da ya kira sunan ya san Adam saurin dubansa suna hada idanu gabansa ne yayi wani irin bugu mai karfi har sai da ya dafe kirjinsa.
"kasan Bahijja".
Alhaji Kabeer ya fadi cikin karfin hali da janyo jarumta.
Cikin rashin fahimtar inda zancen baban nasa ya dosa ya dago koɗanɗun idanuwansa ya dube shi yana mai tabbatar masa da bai san taɓa.
Gyada kai Alhaji Kabeer yayi tare da zukar numfashi ya fesar sannan ya gayyaci natsuwar zuciya da jarumta ya dorawa kan sa yana mai canza fuska na nuni ba wasa a cikin maganar sa.
"Dama kasan Bahijja ta gidan Alhaji Nasuru mai tireda ne".
Ji yayi zuciyarsa tayi wani irin zillo  kamar zata tarwatse kansa ya shiga jiya masa wasu lamura ne da suka daɗe da shuɗewa suka shiga kawo ƙwakwalwarsa da zuciyarsa farmaki lokaci guda TUANA BAYA ya fado masa sumar wucin gadi yayi kafin ya dubi mahaifin sa cikin wani irin yanati na rashin hayyaci gabadaya.
"D..a.dy ban..sa.n..taba".
Ya fadi yana dandatse kalmomin kamar wanda ake shirin yankewa harshe ziciyarsa ta shiga bugu mai dauke da tashin hankali girguza kai kawai yake yi cikin tsananin firgici da razana hawaye suka zoba masa da sauri ya rufe bakinsa jin kuka na shirin kawo masa farmaki.
Yanayin da ya nuna su kan su sai da suka firgita sosai tsoron su ya kara Hajiya Laila da Tk lokaci guda suka gasgata zargi da zuciyoyin su ke yi shi kuwa Alhaji Kabeer ruɗani ya shiga ganin dan nasa yana zubar hawaye cikin ɓarin jiki ya sake janyo Adam cikin rawar murya ya fara magana.
"fada min mai yake tsakanin ku da ita Bahijjar ko mahaifinta shin akwai saɓanin da kuka taba samu ne tsakanin ku wanda yasan har zuwa wannan lokaci ba su manta ba Adam akwai ayar tambaya akan ka musamman yanayin da naga ka nuna fada min don Allah domin taka amsar ita ce kawai mafita a garemu".
ya karashe cikin laushin murya mai cike da rarrashi yana faman bubbuga bayan sa alamun neman amsawarsa.
Kuka sosai ne ya shiga yi wanda sam ba hawaye sai na zuciya tabbas abubuwa da yawa sun faru a duniyarsa sai dai ba wanda ya tsaya masa a rai kamar Bahijja kullum da ita yake kwana yake tashi a ransa itace wacce take ta zuwa masa cikin barcinsa da kuma lokacin da ya fita hayyacin sa tabbas ita ce amma sam kwakwalwarsa da zuciyarsa sun ka sa fahimtar da shi wacece ita sun kasa ganar da shi wacece ita har sai da ta samu muhalli a zuciyarsa ta gina gida babba wanda ta mamaye duk wani sashi nacikin zuciyarsa tabbas hakki ne ke bin sa ba wani abuba ne tabbas ita ce ta zo za ta kashe shi cikin Asibitin nan ya daɗe yana tunanin wacece za ta kashe shi amma ya kasa gano wa ya sha ganinta cikin MAFARKIN IDO BIYU amma sam ya kasa gane ita ce. Ita ce Bahijja yar makaranta wacce ya batawa rayuwa a cikin shekarun yarintar ta ya ci zarafin ta ya keta mata HADDI bai ji tausayinta ba bai ji ƙantaa matsayin ta na 'ya mace ba bai ga ƙanƙantar ta ba duk zuciya da KAZAMIN BURI ya debeshi da rashin imani ya aikata aikin da ya sam zai illata rayuwarta da ma duniyarta ya aikata mata abin da zai hanata kwanciyar hankali cikin dangin ta da Al'ummar gari tabbas ya yi kuskure wanda tun da yake bai taba zaton kuskuren zai biyo shi ba a gashi yanzu ita da ya lalata wa rayuwa a matsayinta na 'ya mace ita ya gani yake so yake yi mata son da bai taba ganin wani yayi wa 'ya mace ba ya tabbata HAKKI ne ke bin sa.
Jan numfashi yayi cikin wani irin yanayi na tashin hankali ya dubi Alhaji Kabeer.
"Dadya nasan ta farin sani ma kuwa tun lokacin ba ta kai haka ba".
Duk kansu sakin bakin su kayi cikin jajanta lamarin suka shiga gyada kai alamun su na jin sa.
Sai da ya shafe fiye da mintina biyar kafin yayi kokarin magantuwa.
"Dady Hakkin ta ne ya kama ni".
Ba alhaji kadai dake zaune kusa dashi hatta Hajiya Laila dake zaune kan Sallaya sai da ta zabura tana ambaton 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'u' kafin ta daura hannu akai ta fara magana.
"nasan za ayi haka dama, tuni zuciya ta san ba banza ba zomo ya shiga kasuwa".
ta ida tana mai jan numfashi.Alhaji kan sa sai da yaji bugun zuciyarsa ya karu cikin dakiku.
"me kayi mata Adam?".
Alhaji ya fadi cike da fargabar abin da zai fito amatsayin amsa daga bakin ɗan nasa ya kure shi da idanu kamar wanda aka cewa in ya kau da kai zai neme ya rasa.
"Adam da kai nake me kayi mata?".
Alhaji ya sake fadi yana mai jijjiga Adam da yayi shiru kamar wanda ba numfashi a jikinsa. Amma har zuwa wannan lokacin ya kasa cewa wani abu domin ganin yake kamar in ya fadi kowa zai tsaneshi ba ma iyayensa kadai ba har da Al'umma za suyi masa tsana mai tsanani ya sani wasu ma za su iya cewa za su kashe shi domin abin da ya aikata bai taba zaton zai kasance abun tuni ba a rayuwarsa har ya haifar masa da bakin yanayi mai dauke da tashin hankali da kayan takaici tabbas Sharri dan aike ne mai shi yake bi bai taba zaton zai yi nadamar abin da ya aikatawa Bahijja ba sai yau bai taba zaton zai ji kunyar idanun iyayensa ba sai yau bai taba zaton zai ji kunyar abin da yake aikatawa ba sai  yau da ta kasance RANAR NADAMA a gareshi ranar da ba ta da amfani cikin rayuwarsa ranar da ya fara tur! da MATACCIYAR RAYUWA da yake yi ya yi tur! da MATACCOYAR ZUCIYA da ta kasance abokiyar shawarar ga duk abin da ya aikata cikin duniyar sa.
Hawaye suka balle masa wanda yake jin zafin su saman fuskarsa yajin raɗaɗin su har kasar ruhi da zuciyarsa yana jin yarda duniyar take juya masa cikin wani irin yanayi na rashin dadi da armashi ko kaɗan. yayi da nasanin wannan rana yayi da nasanin abin da ya aikata a bayan rayuwarsa bai taba zaton a rayuwarsa zai ki rayuwarsa ba kamar yau ya tsani duniyarsa ya tsani rayuwar da yayi a baya mai dauke da KAZAMIN BURI.
Jan numfashi yayi sannan ya dubi mahaifinsa.
"dadya na ci zarafin ta na keta mata haddi cikin duniyarta tun lokacin ba gama sanin ita wacece ba..."
Wani mari da yaji saukarsa a fuskarsa ya tafi masa da azancin sa shi ya sanya shi sauri tsuke bakinsa wasu taurari ya hango sun gillamawa saman kansa ji yayi kamar jinsa sa ganinsa aka tafi da su wani irin zillo da zuciyarsa tayi ya sanya shi zabura ya na mai rike kuncinsa hawaye suka cika fal a idanuwansa ba wai yana kukan zafin marin ba ne a,a dama ya sani in kowa na duniya yaji abin da yayi dole ya tsane shi tsana mai tsanani kuwa.
Hajiya Laila ce ta zabga masa mari har biyu na lafiyayyu don  dama jiransa take ya fadi abin da ya aikatawa Bahijja domin zuciyarta tuni ta fara gasgata komai da tunanin ta ya ke kawo mata.
"ba zan tsine maka ba Adam domin in har na tsine maka na baka lasisin kara lalacewa ne cikin duniyarka ban taba zaton haka kake ba ban taba zaton haukar kuruciyar taka ta kai haka ba ban taba zato baka da imani ba sai yau wallahi ka cuci kan ka Allah wadaran irin rayuwa taka Allah ya wadaran irin son zuciya da buri irin naka wallahi ka ji kunya kuma kana kan jin ta kuma na rantse maka da Allah ba zan goyida bayan mugu mara tausayi ba ko da kuwa kana matsayin ɗana na cikina wallahi ba zan goyi bayan ka ba 'ya mace ka wulakaunta 'ya mace ka ciwa zarafi 'ya mace ka keta wa haddi...".
Wani kuka ne ya zo mata wanda ya tafi da azancin ta nan da nan idanuwanta suka shiga zubda hawaye kamar an bude famfo tana faman shassheka kamar wanda numfashin ta yake kokarin barin jikin ta.
"sam ba kayi wa kan ka adalci ba cikin rayuwa kuma ka sani duk wanda ya cuci wani Allah ba ya bari kuma ba ya barin hakki yarda kaci zarafinta ka bata mata rayuwa domin na tabbata sai ta ga takaicin rayuwa da bakin ciki cikin rayuwarta duk macen da aka ketawa Haddi a duniyarta to ta bani ta lalace in ba wani iko na Allah ba to wallahi ta dinga ganin gararin rayuwa kenan ta daina kwanciyar hankali da natsuwa kenan cikin duniyarta Adam ka tabbata yarda ka bata mata rayuwa in har ba yafe maka tayi ba to wallahi zaka ga sakamako kalar abin da kayi mata ba wai mata nake maka ba kuma ba baki nake yi maka amma wallahi indai cin zarafi ne da cin mutunci a rayuwa shi abin yi ka cigaba yanzu ka fara ganin sakamako...".
"ya isa haka Laila".
Alhaji ya katse ta cikin tsananin takaicin abin da ke faruwa sai faman numfarfashi yake yi idanuwansa sun kada sunyi jajir ya shiga gyaɗa kai yana mai duban hajiya wacce duk ta gama ficewa daga hayyaci ba abin dake dawaniya da ita sai bacin rai da takaicin abin da Adam ya aikatawa Bahijja dauke hawaye tayi kafin ta cigaba da magana.
"akan me zaka ce min ya isa Alhaji? ka barni na fada masa domin hakan ne kawai zai rage min raɗaɗin zuciya da ruhi. domin na nuna masa abin da ya aikata ba komai bane sai cin zarafi da cin mutunci na lura sam bai san wacece 'ya mace ba, bai san darajar ta ba bai san kimanta ba a idanun Al'umma. nayi kaico nayi Allah wadai da Adam ya kasance cikin sahun mutane masa zuciya wajan keta haddin ya mace nayi bakinciki nayi takaici akan haka ban taba zaton ɗan dana haifa zai kasance haka ba Allah na gani kuma yana ji...".
"don Allah Laila kiyi hakuri ki natsu mana".
Alhaji Kabeer ya sake katse ta wanda shi ma a wannan lokacin tausayinta ya fara tsargarsa ya san gaskiya take fadi komai da take furtawa gaskiya ce tsantsa dubanta yayi ya nisa cikin rashin abin fada.
"ni na rasa ma abin fadi akan lamarin nan...".
Katse shi tayi cikin jin haushin maganar tasa domin ta lura har yanzu bai bar yi wa ɗan masa makahon so ba har yanzu bai fahimci abin dake faruwa ba har yanzu bai san abin da ya dace yayi ba.
"yo dama Alhaji yaushe zaka san abin yi ai Alhaji baka da abin fada domin komai ke faruwa kana da hannu dumu-dumu a ciki kai ne ka ba da lasisin faruwar komai. Komai Adam ya aikata da sa hannunka an san komai Allah ke sakawa ya faru amma kuma ai komai da SANADI to Alhaji kai ne Sanadi Allah na gani nayi tarbiyyar Adam daidai gwargwado na kula da shi a matsayina na Uwa na yi iyakar kokari na amm duk Alhaji kasa kafa ka shure ka dauki son zuciya da makauniyar soyayya ko ka tafi da son rai wanda hakan ya haifa da matsala sosai ba ga ku ba har dani da kuke kokarin kashe ni da raina".
"Hajiya don Allah kiyi shiru ki bar ni naji da abin da ke damuna a rai da wannan zai ji da bakin cikin abin da yayi ko kuma da rashin lafiyarsa ko da rigimarki".
Wani kallo tayi masa sannan ta kalli Adam wanda duk ya gama sakin jiki tashin hankali ya gama luguiguita shi ba abin da yake keta masa zuciya da kasar ruhi sai maganganun mahaifiyarsa da irin ZAFIN HAWAYE da yake ji nata wanda ya tabbata nan ma wani tashin hankali ne mai girma a wajansa kukar uwa bala'i ga ɗa balle shi da ya hada mata zafi da yawa Allah kadai ya san yarda zuciyarta take ciki a halin yanzu.
"ta ya ya zan yi shiru Alhaji, ta ya ya kake tunanin zuciyata zata daina zafi da raɗaɗin lamarin nan nima fa 'ya mace ce kuma nasan irin zafin da yawancin mata suke shiga in sun gamu da irin wannan cin zarafin daga azzaluman wasu mazan ya kamata ka sani Alhaji abin da Adam yayi ba karamin babu bane, kuma na tabbata Hakikinta ne ki bibiyarsa kuma dama shi Allah ba azzulumin bawansa bane".
Dakin ne ya dau shiru ajiyar zuciyoyi ne kawai ke kai kawo a tsakanin junan su sai kuma sautin kukan Adam Alhaji ya nisa kafin ya fara magana.
"ban goyi bayan Adam ba Laila akan wannan lamarin ni kai na naji zafi da raɗaɗi a zuciyata akan wannan abin da ya faru sam ban ji dadi ba".
Murmushi tayi mai dauke da hawaye sabod ta rainawa maganganun Alhaji hankali sama ba ta ji ya fadi wata kalm wacce ta burgeta ba ko daya da alamun har yanzu yana sahun son ɗan nashi mai dauke da MAKANTA hanci taja gami da yin kwaɓa tana mai duban Adam tana jin tausayinsa sai dai ba zata bari hakan ya nuna a fuska ba domin abin da ya aikata ba abin a rarrashe sa bane ya kamata ace an nuna masa kuskurensa amma da alamun Alhaji bai san haka din ba ita kam ba za ta iya ba duk son da takeyi masa ba zai hana tunani bacin ran ta ba akan abin da ya aikata. Cikin gatse ta dubi Adam.
"har yanzu kana son ta ko kadai na".
Duk kan su suka dubeta cike da mamakin jin kalamanta amma sai tayi musu fuska tana mai sake tambayarsa shiru yayi kamar ba zai ba ta amsa ba domin yanzu wata irin matsananciyar kunyar Hajiya Laila yake yi cikin fiddo abin fadi dakyar kansa a kasa yace,
"Ina son ta Momy...".
Da sauri ta katse shi.
"kasan Allah wallahi ba zaka taba auran Bahijja ba in har ina raye in ba wani iko Allah ya nuna nasa domin nasan ko ka aureta rashin mutuncin naka ba daina shi zakayi ba ba ma wannan ba na tabbata yanzi cike take da kai wallahi domin daukar fansa nikam ta burgeni wallahi da ta nuna ta san mutuncin kanta da darajar kanta".
A razana ne ya shiga dubanta jin irin kalaman da take fadi hawaye na zuba a idanuwansa wata irin nadama yaji tana ziyartasa ya tabbata Hajiya Laila da gaske take kuma ya tabbata ita kanta Bahijja ba zata aure shi sai dai ya mutu da son ta a zuciyarsa wanda ya kasance masa dole yayi ba tare da son sa ko amincewarsa ba son ya direwa zuciyarsa.
"Laila ki daina fadin haka mana".
Alhaji ya fadi cikin sigar gajiyar lamarin. duban sa tayi.
"akan me zan daina fadi abin da na san ba yuwuwa zai yi gwanda nasara dashi ya fara hakurkurtar da zuciyarsa saboda ya san a duniyar nan ba komai ake nema ake samu ba kuma ba ko wani buri bane na zuciya ke cika".
shiru yayi jin abin da tace ya san da biyu take sakin maganar sai dai ba yarda zai yi domin gaskiya take fada ya gano BABBAN KUSKUREN da ya tafka cikin duniyar rayuwarsa da ta ɗan nasa a sanyaye ya dubi a jiya cikin rashin tunanin yi.
"yanzu Laila meye abin yi akan lamarin nan?".
"meye kuwa abin yi illa kuje ku nemi gafarar Bahijja da na iyayenta sannan kuma ku fara kokarin gina SABUWAR RAYUWA wacce ba son kai da son zuciya a cikin ta".
Gyada kai ya shiga yi cikin rashin abin fada yana kara gasgata maganganunta tabbas sunyi kuskure cikin rayuwarsu sosai shi da dan sa ya nuna masa so da gata mara misaltuwa wanda ya kai su ga dana sanin rayuwa ya tabbata hakki da yawa da suka dauka shi ke bibiyar rayuwarsu a wannan lokaci domin sun rasa kwanciyar hankali da natsuwa cikin duniyar rayuwarsu

Hmmmmm Adam ya take neee😁

It'x Kamala Minna😘😘

DUNIYARMU (Compelet)Where stories live. Discover now