NI DA ANAM

2K 112 1
                                    

*NI DA ANAM*   
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞     

💞🌟💞
         

✍🏼 _Rubutawa:_

       

*QUEEN MERMUE*

    _Tare da:_
         🤴🏻
*KING BOY ISAH*

BABI NA BIYU(02)




Da asuba Anam ya farka bayan yayi sallah yayi addu'a ya shafa tukun ya kama tunanin rayuwar sa.
Karfe bakwai ya tashi ya shiga kitchen fuskarsa sam ba walwala, Zuciyarsa cike kunci ga yunwa da take neman illata shi dan jiya da dare ko abinci bai ci ba ya kwanta, Ya kuwa yi sa'a ya iske kayan shayi madara ce kawai babu.
Bayan ya jona hita ya saka ruwa ya fita ya sama wani ma'aikaci ya aike sa ya sayo masa madara peak kwali da biredi babba daya Da kuma sigari pack daya, Haka kawai yaji yana so ya gwada shan sigari ko zai sama sasauci kamar yanda yaji mashayanta suna cewa tana rage damuwa.  Ya kuma falo ya zauna ba a jima ba wanda ya aika ya dawo yayi masa knock ya bude masa ya karbi kayan tukun ya kulle kofar. Kwalin madarar ya bude ya dauki guda ya nufi kitchen lokacin ruwan yayi zafi ya hada shayi ya dure a wani filas da ya gani ya debi dai-dai wanda zaisha ya hada a kwafi ya fito ya karya.  Bayan ya kammala break din ne ya bude kwalin sigarin ya zaro daya yana kallonta. A zuciya yake cewa, "Shin da gaske ne in nasha wannan zata rage min damuwar da nake ciki? Da gaske zanji sanyi a raina in na sha?". Kitchen ya tashi ya shiga ya daukko ashana. Tun daga can ya bankawa sigarin wuta abunda da ko warinta baya so. Abokansa ma baya bari su sha a kusa da shi.  Haka ya kai baki ya zuka. Ai kuwa ya fara tari, bai dadara ba ya kara zuka. Nan ma tarihi ne ya mai-maita kanshi. Dan tuni idanunshi sunyi jajur sun ciko da kwalla.  Haka yaci gaba da zuka yana tari har ya shanye ta tas. Amma baiji wani sauyi ba. Ya kara kunnawa wata wuta ya shanye amma ina. Kawai ba komai ke mai yawo a kwanya ba sai kalaman mahaifinsa. Wanda yake jinsu tamkar saukar aradu a duk sanda ya tuno. "Wai nine gay, nine dan luwadi".  A fili yake fadar haka daki ya koma ya daukko makulin motarsa ya fito. Fita yayi daga gidan shi kanshi baisan ina zaije ba. Zafin nan da radadin da zuciyarsa ke yi shi kawai yake su su daina. Yayi tafiya mai dan tsayi a gefan hanya ya ga wani beer shop. Cikin kwarin gwiwa ya tsaya ya saya kwalba biyar ya. Ya zuba a mota ya koma gida. Yana shiga gidan nashi sai da ya kulle tukun yaje ya zuba kwalba hudun na giyar a fridge ya bude dayar kuwa. Bai taba shan giya ba sai wannan karon haka kurin yaji ya gwammaci yasha abunda hankalinsa zai gushe ma gaba daya dan ya daina tuna abinda ya faru. Ai kuwa ya fara didika sai da ya shanye tass! Nan take kuwa hankalin sa ya gushe. Ya ta surutai yana layi irin na mashaya. Zuwa can kuma barci ya kashe shi a kan carpet ya kwanta tsakar falon.
***************************
Mopping din katan falon take tana dada goge baya dan tasan halin masifaffiyar hajiyar nan yanzu haka sai ta zo tace bai fita ba. Tana tsakar tunanin nan kuwa taji karan takalmi alamun sakkowa daga saman beni. Ai kuwa ta kara azama wajen goge tayis din dan ita da gaske take tsoran matar nan. Tun kafin ta karasa saukkowa ta fara fadin. "Kai! Kai! Kai!...". Tana yamutse fuska. "Dan ubanki haka kika ga ana mopping a garin ku?. Dubi nan  fa". Ta nuna wani gu da yatsa. Manal da tayi saurin mike wa dan tsoro tayi saurin doban wajen. Bata ga ko jurayi ba. Kawai abunda ta kula dai muguntar matar nan ce ta motsa. Tsawa taji an daka mata, "Ba zaki zo ki goge ba kika wani yi tsaye kina kallona kamar wacce ta hadiyi rodi? Ko na gaya miki tsayuwar sojoji nace ayi min?".  Sumi-sumi Manal ta daukko bokitin kumfan da sauran kayan da take mopping din.   Zata duka ta fara goge gun kenan hajiyar ta wanka mata wani wawan mari. Wanda yasa ta saki kara ta rike fuska. "Yi mun shiru munafukar banza. Na lura tunda kika zo gidan nan ba abunda kika iya sai ha'inci. Ni bansan godiya zan wa Hajiya da ta bani ke ba ko Allah ya isa. Domin daga ganin ki ko an kaiki madina ma ba wani daraja zakiyi ba. Banga kuma  dalilin da zaisa na biya miki kudin jirgi zuwa chaina ba. Domin bakin jinin ki yayi yawa". Manal bakin ta ta matse dan kuka na neman kwabtowa. Hajiya Lawisa ta gama masifar ta hade da cewa. "In kin gama kije ga kaya na can ki wake su tas. In kin gama ki dora girkin rana. Kuma in kayan sun bushe ki goge su kafin girkin dare. Domin ni banga amfanin ki a gidan nan ba in ba wannan ba". Tana fadar haka ta wuce abunta tana waya. Manal kuwa kuka ne ya kubce mata. Ta daga hannu sama tana rokon Allah ya fitar da ita daga cikin wannan gida wanda ya zame mata tamkar gidan yari. Hawaye suka shiga kwaranyo mata. "Meyasa Mama zatayi kyauta dani? Me yasa in ma kyautar ta zama dole ne ta bawa mai imani ni. Wanda yasan hakkin dan Adam ba kamar hajiya Lawisa ba?". Tambayoyi ta shiga jerowa wanda ita kam bata da amsar su. Kuma ba wanda ke jinta balle ya bata amsa.
************************
A bangaren Anam kuwa yau kwanan shi biyar a secret house din nan. Kwanakin nan biyar sun bashi dama da ya zama cikakken mashayi. Yanzu in ka daga fridge dinsa. Ba abunda zaka samu face kwalaban giya iri-iri. Taba kuwa tuni ya kware da sha. Har ta hanci ya iya buso hayaki. Zaune yake a kan kujera 3stars ya jawo center table gaban shi wanda ke dauke da kwalbar giya  hannun sa kuwa sigari ce sai zuka yake. Dan wadan nan abubuwan biyu su kadai ne ke sa zuciyar shi sanyi. Wato sigari da giya. Fuskar sa a murtuke. Ba alamar murmushi, sai ka rantse ma ba a taba shimfida murmushi a kanta ba. Falon ya kare wa kallo wanda duk yayi kaca-kaca da shi. Ya ja tsaki. Tukun ya fiddo wayar sa. Ya kira wata number ya kara a kunne. Sai da wayar ta kusan katsewa tukun aka dauke hade da fadin, "Hello". Anam cikin muryar ta isassu mai nuna ya isa. Yace, "Wai ku haka gidajen nan suke ba wasu masu aiki dama?".  Daga can Hajiya Lawisa tace, "Au! Sorry Anam ko? Na manta ne ashe ba a baka 'yar aiki ba, please sorry ina busy ne but yau za'a aiko maka da 'yar aiki".  "Ok amma ni dan aiki namiji nake so ba wai mace ba"  hajiya tace. "Ai mu bama da maza yan aiki sai mata dan haka gashi zan tura maka". Bai kara cewa komai ba ya katse wayar hade da yin tsaki ya wurgar da ita gefe guda. Ya jawo kwalbar giyar sa ya fara kwankwada. Ba' a jima ba barci yayi gaba da shi. Bayan kamar awa biyu da faruwar haka. Tsaye take a kofar falon tana kwankwasawa amma shiru. Ta dan jima a gurin ganin anki bude wa yasa ta dan tura. Dan tayi tunanin ko mai gida baya nan ne. Tana turawa kofar ta bude, a zuciya tace, "Bari in shiga inyi aikin da ya kawo ni kawai". Kanta tsaye ta shiga falon.  "Innalillahi wa'inna illahir raji'un, me zan gani haka? Dama gidan arna Hajiya ta turo ni. Arnen ma mai shan giya so take ya sha giya ya hallakani wataran wato?". Tsayawa tayi gaban shi tana kallon fuskarsa. "Amma kuma wannan baiyi kama da arna ba. Kai amma kuma in muslimi ne wannan gaskiya baya da halin kirki. Kai! Kai! Kai! Tashi". Anam na cikin barci yaji ana tashin sa. A hankali ya bude ido har yanzu giyar bata idasa sakin shi ba.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now