NI DA ANAM

1.4K 73 0
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

_Tare da:_
         🤴🏻
*KING BOY ISAH*

BABI NA DAYA (14)

'             '👨🏻‍💻👩🏻‍💻'          '
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

Karfe daya na dare cikakkun 'Yan daba suka shiga gidan sj Ali da niyayyar hallakashi sai dai wayam suka gani babu kowa duk da Abba ya hada nashi inashi yabar garin.
Hankalin Hajiya Maryam ya tashi dan haka cikin tsananin bakin ciki tasa a kawoni office din ta da karfe ukku na dare.
"ke dan Uwarki ki fadan inda Saurayin ki yaje!"
Murmushin bushewar zuciya nayi nace,
"Yabar kasar nan dan yana son rayuwa dani amma kada ki damu ni na sanar dashi plan dinki kuma zai dawo kamar bubuwa ya hallakaki da azzalumin mulkin da karfin imanin sa, zai dawo ya daukeni ya rayuwa dani fiye da yanda kika rayu koma zai shaidawa duniya duka mummunan ayukkan da kika aikata da manya manya yan siyasa da masu kudin da kike tallafawa dan cin zarafin marayu. Marayu yaya ne masu yanci zamu..."
Wani wawan shuri da tayi dani har saida naga wuta.
Ta ko ina take jibgata har saida wani yaron ta ya rike.
"haba Hajiya kada kijwa kanki ciwo ki barta mu kashe ta kawai."
Wani wawan mari ta dauke shi dashi wanda yabawa sauran mamaki banda ni da abubuwan mamaki suka kare a rayuwa ta.
"kana hauka? Ko acikin ma falki kada kayi tunanin kashe wannan *ita kadai ce dani.*"
Cikin hasala ta juyo ta cire min kaya ta maidani tsirara kana ta karbi kayan wani yaron ta tulluki dashi ta bani.
Ita ta aske dukkan tsawon gashi na ta maidani Namiji zahuran dama wurin saka yan kunne na ya bace ya like.
A wani daki tasa aka kaini bayan dogon suma da nayi.
Daga wannan lokacin ta sallamani ga kawar ta Lawisa da sunan ta wuce dani a kasar China dan aikatau kamar yadda sauran matan suke Makka da sauran garuruwa.
Hajiya Lawisa tayi duk yanda zatayi Namiji ya so ni ya kusance ni amma hakan ga gagara akan ka tayi ta duka na ta sani fitar da tsiraici na ta sani zuba maka magani amma duk a banza kasancewar kai baka son mata."
Labarin ta ya girgiza zuciyar Anan sosai ya tausaya ma labarin amma sam baiji tausayin ta ba sai haushin uwar ta da tayi cikin shegen ta tayar.
Cikin Kuka Manal tace,
"Dan Allah ka kaini wani gun ko aikatau nayi har na samu kudin zuwa Sokoto zan nemo Ya Ali a duk inda ya shiga, bazan iya rayuwa babu shi ba ina son saaaa..."
"ki saurara min pls!"
Cikin tsawa ya tsayar da ita.
"naji labarin ki da sakarci irin naki dana uwayen ki da basu amfane soyayyar da sukeyiwa juna ba wata kila kuma a yawon ta zubar ne aka same ki, a binda nake so dake a yanzu kici gaba da aikin ki anan gidan zan taimaka miki wajen nemo wancan saurayin naki zan dinga biyanki duk wata kudin girki da gyaran gida sai ki adana. Kije ki kwanta gobe da safe mayi magana."

A wurin Hajiya Ladi kuwa a firgice ta koma gida cike da bakin cikin wannan auren da akayi masa tana zuwa ta fada falon ta acan ta sami 'ya'yan mata biyu Sareena da Yayarta Mulikat,
"Ai wallahi da sake! Munafikin banza dama na dade da sanin dukiyar Alhj yake so, tun da ya aura masa kanwar sa ta mutu bata ci gadon ba shine yanzu zai likawa dan yar sa ko? To wallahi bazata sabu ba sai ya sake ta kuma sai  na walakanta wannan yaron..."
Bambamin fada takeyi kamar ta tashi fada hakan yasa Sareena tace,
"Mom whats happening?"
"barni dasu! Alhj Tahir ne yanzunan suna can sun daura auren Anam da Shegiyar  Minal dinnan..."
"what? Aure? Kuma Minal? Haka Daddy zaiyi min? This is unfair wlh bazan yarda ba, za'ayi bura'uba kuwa dan billahilazeem sai ya aureni..."
Fuu ta shige daki yayin da tabar uwarta da tarin bakin ciki, Mulikat kuwa tabe baki tayi tana jinjinawa karfin hali da zuciya irin tasu.

Yana shiga daki ya fitar da paper ya yage ta ya zuba a a toilet yayi flusion, kwantawa yayi ringine kansa nayi masa mugun sara, tabar sa ya jawo ya dinga kunnuwa yana zuka har sai da yaji ran sa yayi masa sanyi.
A buge ya kwana dan ji yayi idan bai sha giyar ba  zai iya haukatawa.
Da safe koda ya tashi Manal har ta kammala komai kamar yadda ta saba, har kasa ta gaidashi "Gudmrng Sir!" shi kuwa sai abun ya bashi  haushi ko kallon ta baiyi ba ya wuce a gaban ta.
Jikin Manal yayi sanyi ganin kwabar giya a dakin sa wani tsanar sa ta kara ji ita dama can ta tsani mashayi gashi shi wannan ya hada manya-manya zunubai guda biyu.
Sai azahar ya shirya cikin farar shadda mai kyaun gaske ya fesa turaruka sosai kana ya fito dan tafiya Gidan Abba Tahir.
A karo na farko da Manal ta ganshi da shigar Hausawa sai taga ya canja mata sosai, bai ce da ita komai ba yayi niyar ficewa, da sauri tace,
"Sir! Ur lunch is ready"
"Bana ci"
Daga haka ya fita sai Gidan Abba Tahir.

"Akil kasan dalilin da yasa nayi maka wannan auren ba tare da tambayar ra'ayinka ba ko na tambayi wacce kake so?"
Cikin girmamawa yace,
"a,a Abba"
Abba ya jinjina kai yace,
"to sabida na cire ka daga zargi da tuhuma da Mahaifinka yake maka, kasan komai shi shaida ne akan abubuwan da kake aikata, Akil me yasami kan ka? Wallahi da Mata akace kana bibiya bazamu ji zafi ba kamar wannan mummunar tabi'a da ka dauko ka kawo mana acikin zuri'a haba Akil anya kana so Mahaifiyar ka kwanta a kabarin ta lafiya?"
Cikin karfi Anam ya saki wani irin Kuka mai ban tausayi da tausaya kansa da zuciyar sa haka kuma ya kasa musanta abinda ake zargin sa dashi.
Abba Tahir yaci gaba da cewa,
"Akil dan mu samu kwanciyaf hankali yasa na aura maka 'yata kuma yar uwarka kuma masoyiyar ka,

Nasan acan baya kun so juna shiyasa na zaba maka ita dan wannan matsalar taka Sirrin mu ce idan wannan al'amarin ya bayyana mutunci mu ya zube a idon duniya kima da darajar wadan nan gidanjen namu ta zube shiyasa nake so ka nutsu duk abinda kake ji a Namiji zaka samu fiye dashi  a wajen mace kadaina halayyar 'ya'yan awakai.
Ga matar ka can, nasa a gyara maka gidan ka dake Abuja   kuma daga wannan satin zaka fara aiki a companyn Baban ka, ina so kayi duk wani abu da zai maida kauna dake tsakanin ka da mahaifin ka. Ka tashi ku tafi Allah yayi muku albarka."
Kuka sosai Anam yake yi har saida yasa Abba Tahir yayi hawayen shi a zaton sa nadama Anam yake yi.
Karfe Biyar na maraice suka halarci falon Alhj Nura, yayi masa fada sosai da jaddada masa ya gayara halayar sa muddin yana so ya gama da duniya lafiya.

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now