NI DA ANAM

1.6K 78 1
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

*BABI NA ASHIRIN*
20

Tsaki kam! yafi hamsin da yayi, kafin bacci mai nauyi da sauke gajiya ya ɗauke shi.
Ana kiran salla ya tashi ya fito dan zuwa masallaci.
Kofar Minal ya karasa tare da k'wank'wasa mata.
"wai meye haka Yaya?"
Cikin muryar ta, ta bacci tace hakan.
"Sallah."
Iya abinda kaɗai yace.
Har ya nufi kofar fita falon. Sai kuma yaji yana son tashin Manal itama, a ganin sa hakk'in sa ne. Kamar yadda Daddy yake masa tun yana k'arami.
Tsaye yayi a bakin k'ofar ɗakin, yana nazarin ya k'wank'wasa ko ya bari.
Bai ahama ba yaji an buɗe kofar ɗakin.
Bokiti a hannun ta cike da kayan wanki.
Ganin sa a bakin k'ofar, har sai da ya ɗan tsoratar da ita, da sauri taja baya tare da cewa.
"Am..an...gudmorning sir."
Murmushi yayi, ganin yanda ta daburce,tana faman jan ɗaura k'irjin da tayo.
"dama zan tashe ki ne amma..."
So yayi ya tambayeta meyasa take wanki a cikin dare, sai kuma ya katse maganar ganin yanda ta tsare shi da ido, kamar bata taɓa ganin shi ba.

A hankali ya juya ga barin wajen.
A jiyar zuciya ta sauke, wanda sautin sa har sai da ya ziyarci dodon kunnen sa.

Jin ficewarsa ga baki ɗaya yasa da sauri ta nufi ɗakin wanki.
Bata bukatar sake wanke su a injim, dan kuwa ta murje su da hannu son ran ta.
Busar dasu tayi, kana ta fara gogewa, duk yadda marar ta ke yi mata azabar ciwo, bata bar wajen ba har sai da ta goge su tsab.
Cikin sauri, ganin agogon falon ya nuna mata k'arfe shida da rabi, yasa ta shige kitchen.
Babu isassun kayan da take buk'ata, tun daga kan kayan aiki da sauran kayan abincin.
Cikin gaggawa ta haɗa kayan karya kumallon, ta koma ɗakin ta.
Sosai marar take yi mata ciwo. Ga tashin zuciya da ya hana ta kurɓa ruwan shayin.

Minal, ce ta fito daga sama. Daga ita sai 'yar k'aramar riga mai bayyana shafukan sassan jikin ta.
Anam da ke zaune yana kurɓa ruwan shayin, ko kallo bata ishe sa ba, kamar yadda itama ɗin bata damu da ya kalleta ɗin ba.
Zaunawa tayi a gefen sa tana k'okarin haɗa shayin a kofi.
"Morning Baby."
Ta manna masa peck a kuncen sa na hagu.
Da kyar ya iya buɗe baki yace.
"Morning."
"Baby ina Manal ne? Meyasa ba zata dinga tsayawa tana haɗa mana ba? Bari, na kira ta."
Wani kallo ya bita dashi ganin ta nufi ɗakin Manal, da sunan tazo ta haɗa mata shayi.
"Baki da kai wallahi."
Ya faɗa yana tauna soyayyiyar doya mai haɗe da naɗin kwai.

"Baby! Yarinyar nan ba tada lafiya, ko cikinta, yake ciwo ne? Na tambaye ta,ta kyale ni, nayi-nayi tak'i faɗamun."
Minal ta k'arashe zancen tana kurɓa shayin da ta haɗa da kanta.
Mik'ewa  yayi cikin sauri ya nufi ɗakin.
Durkushe ya ganta a gefen katifar, ta ɗora duka hannayenta akan, kanta.
Kuka takeyi ciki-ciki. Kukan da ya taɓa zuciyar sa a cikin rashin tsammani. A cewarsa baya son kuka. Koda na k'aramin yaro ne.
Da sauri ya isa wajen ta, hannayen, ya janyen. Tare da dago kan ta.
"Meya same ki?"
Cikin raunanniyar muryarsa ya fidda sautin.
Ganin kwayar idanun ta, ya k'ara ɗaga masa da hankali, ba kaɗan take jin jiki ba.
"Meya sameki nace?"
Yana mai ɗago habar ta.
Cikin shesshekar kuka ta janyo hannun sa ta ɗora a k'asan cikin ta, cikin wani irin yanayi.
Yanayin da ya saukar masa da wani bak'on al'amari mai wahalar fassarawa  a kai tsaye.
"Uhm...period ne?"
Ya tambaye ta lokacin da ta zagaye bayansa da hannayenta, tana mai ɗora fuskarta a tsakanin k'afafun sa.
D'umin ruwan hawayen ta, ke ratsa shi, suna bibiyar laps dinsa kamar an sanya masa k'aramin k'adangare  a tsakani.

"Sorry kinji. Bari in ɗauko miki magani kisha."
Da kyar ya kwaci kan sa daga irin k'aton rami da take k'ok'arin kifa sa.

Ta gaban Minal yabi ya wuce.
Wandon shaddar sa ta,tsurama idanu ganin yanda ya jik'e a gaba. Da yake singlet ce a jikin sa hakan ya bata damar ganin hakan.
Taɓe baki tayi, ganin yanda yake wani sham k'amshi.

"Baby. Nidai banson kazanta, kace idan ta samu sauk'i ta fito ta gyara falon nan."
Ta jefo sa da aiken. Lokacin da ya sauko daga sama, ya nufi kitchen.
Bai tankata ba, face ruwan zafin da ya dawo ya ɗiba daga fulas dake ajje a saman teburin.
Minal, hankalinta ya koma akan wayar dake hannun ta.

A yanda ya barta, hakan ya sameta. Kofin ya ajje a gefenta ya tashe ta zaune.
Ruwan zafin masu ɗauke da sinadarin ganyen na'a-na'a,haɗi da neskafi marar sukari ya bata.
Da kyar ta iya shanye k'aramin kofin. Farasitamol guda biyu ya bata.
Ta shanye da ruwa.
Janyota yayi, ya ɗora kan ta a saman cinyar sa, yana mai goge mata hawaye.
A hankali ya kai hannun sa a k'asan cikin ta yana ɗan dafa wajen.
Ba tayi k'okarin hana sa ba, jin yanda sauki yake kusanto ta.
A haka tayi bacci a jikin sa.
Ganin lokaci na tafiya. Ya maye gurbin sa da filo a gare ta.
A bakin kofar ɗakin ya samu Minal, tana k'okarin shigowa.
Ja tayi da baya, tana faman tura baki.
"Wai me ka keyi aciki ne? Ka barni ni ɗaya, kamar mayya.  Kuma fa kayi late a office wallahi."
Tana cewa, tana k'okarin rungumesa ta baya.
"Baby, ni gajiya nake ji, yau ka fasa zuwa aikin mana. Anjima ka rakani gidan Uncle, kasan akwai kaya na acan. Kuma yau, su Fareeda zasu dawo."
Har suka isa ɗakin sa tana lafe a bayan sa tana zuba masa surutu.
Shi kuwa a yanda yake jin kansa ba a natse ba. Ruwan sanyi kawai yake so, su ratsa shi.
"Uhm! Nidai sake ni, zanyi wanka ko?"
Dan zaro idanu tayi, tana mai komowa ta gabansa. Har yanzu hannayen ta akan kugunsa.
"Baby kayi wanka fa, yanzu pass nine fa. Meya bata maka wando haka harda majina?"
Tana kai hannun ta a gefen wajen.
"Minallll!"
Ya kira ta cikin jan sautin.

Kafin yayi k'okarin cewa, wani abun. Ta rufe bakin sa da nata, cikin wani irin yanayi na rashin iyawa.
Gogan kuwa dama yana cikin wani hali.
Ganin ya fara wuce gona da iri, ya daburce yana mai bukatuwa sosai. A dai-dai lokacin da ta dawo hayyacin ta. K'okarin ture sa ta dinga yi, amma inaa! Tsuntsun da ya janyo ruwa, hausawa kance. Shi ruwa suke duka.
Allah ya ceceta. Duk yanda yaso ya biya buk'atar sa, ya kasa. Nan take guiwukan sa, sukayi sanyi.
A gefe ɗaya ya koma ya dunkule. Yayin da yake jin wani irin tashin hankali yana kusanto shi.
Minal kuwa. Tana ganin hakan, taja jiki tabar ɗakin a dari ukku da sittin.
Yafi mintuna talatin a hakan, kana ya samu k'arfin mik'ewa ya shige bayi.
A can ma sai da ya shafe kusan rabin sa'a kana ya fito jiki a mace, babu daɗin rai.
Goma da rabi.
A gogon sa ya nuna masa.
Dakin Minal ya nufa, bacci take yi abin ta.
Dorowar ta ya buɗe ya dauko audugar mata guda biyu, da kananan wanduna biyu.
Ya nufi ɗakin Manal.
Yana shiga, tana fitowa daga wanka. Ya gano hakan ne ta sandiyar sauran ruwa da bata tsefe ba a jikin ta.

"Ina kwana."
Ta faɗa tana sadda kai.
Yayi takun sa cikin nutsuwa ya isa a gareta.
Haɓar ta ya ɗago ya sauke idanunsa acikin nata.
Ganin yanda idanun ta suka kumbura ya daɗa masa tausayin ta.
Hannun ta ya kama ɗaya, ya ɗora mata Audugar da wandunan.
Zaro ido tayi, sai kuma taji kunya ta kamata a karo na farko.
"Babu abinda kike buk'ata?"
Cikin kulawa da sanyin murya, ya faɗe hakan.
Girgiza kai tayi, alamun babu.
Cikin sanyi jiki ya juya da niyar fita daga ɗakin.
"Amm.. Sir, a store babu kayan abinci isassu."
Juyowa yayi yana mai kafe idanun sa a kan ta.
A yanzu al'amarin ta ya daina bashi haushi, sha'awa take bashi, yanda take acting kamar wata matar gida.
"Vabu damuwa, zanyi magana da Auntynki."
Ya faɗa yana ware idanuwan sa.
"Wacece Aunty ta?"
Cikin yanayin rashin ganewa tayi tambayar.
"Ameena,Minal mana."
Taɓe baki tayi, sai kuma tace.
"Ina ta zama Aunty ta? Bata girmeni ba, kuma ai ba ita take girkin ba, bale ka tambaye ta abin bukata. Any way"
Ta ware kafaɗun ta tana mai ci gaba da cewa.
"Ka tambayeta ɗin, sai ta dinga girka maka."

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now