NI DA ANAM

1.3K 80 0
                                    

*NI DA ANAM* 
_(Matsalar rayuwa)_

💞🌟💞  

💞🌟💞

✍🏼 _Rubutawa:_

       
*QUEEN MERMUE*

_Tare da:_
         🤴🏻
*KING BOY ISAH*

BABI NA DAYA (10)

'             '👨🏻‍💻👩🏻‍💻'          '
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*​

​​Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร​.

📚 ​​Zaku iya samun littafan mu a Facebook​​ 👇🏽
Fb.me/ZAMANIWRITERSASSCIATION

📩 ​​Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu​​ 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com

Ga baki daya ya rude da Kiran da Abba Tahir yayi masa na cewa lallai-lallai gobe ya biyo jirgi ya dawo Kano.
Sake-sake ya shiga yi amma ya kasa saka komai.
Baya jin idan yabar lagos a wannan karon zai kara dawowa yafi so ya bar kasar  ga baki daya kamar yadda yake shirin yisan haka Laminde ya kira ya sanar mata zai tashi.

Cikin sanda ta fito falon ganin baya nan ta fice da sauri tana zaton ko ya wuce masallaci sallar asuba, bata tsaya ko ina ba sai gidan Hajiya Lawisa
Kicibis sukayi abakin get lokacin da ake zuba kayan Hajiya a mota,
"ina kwana Hajj..."
"ke meye haka zaki zo min tun da asuba? To gwara ma da kika zo yanzun nan zan maidaki gidan ku dan ni yau zan wuce china kuma babu inda zani dake dan haka ki shiga yanzu fajaru ya fara sauke ki,"
Ta juya ga drivern ta tace,
"kai zo ka kaita gidan su ka cewa Hajiya ni na wuce wannan bata da amfani a waje na,"
Tura keyar ta tayi acikin mota yayin da ta koma cikin gida.
Manal kuwa ran ta yayi mugun baci taso ko sau daya ne ta zubawa hajiya rashin mutumci amma tana tsoron taci duka, gaban ta ya fadi lokacin da ta hangi Anam zaune a kan wata kujera dake babban garden din gidan, duk da haske bai gama bayyana ba amma ta gane shi.
"shikenan yanzu na bar gidan nan? Me zan tarar acan kuma?"
Kuka taji yazo mata amma tayi kokarin hadiye kukan.
Haka ta tsurawa gefen hanya ido har suka iso bakin get din gidan su inda anan suka ci karo da Motar Hajiya Maryam tana magana da masu gadi.
Fajaru driver ya faka a gefe ya nuface ta,
Anan yake gayamata sakon Hajiya Lawisa yayin da hankalin ta yakai kan Manal da take fitowa daga motar,
Kayan jikin ta ta kalla wadan dasu tabar gidan wando ne mai mugun fadi sai kot wadda acikin ta take saka shirt.
Tsaki taja a bayyana kana ta jefa mata muguwar harara, kallon fajaru tayi kana tace,
"kai malam ka maida ta inda ka dauko ta ka shaidawa Lawisa mun riga ta mun cire ta daga 'ya'yan mu dan haka ta kyautar da ita a wani wajen,"
Da sauri Manal ta rugo tare da durkushewa ta kama kafar Maryam tana Kuka,
"Mama dan Allah kiyimin rai ki maidani gidan mu, wallahi Hajiya muguwa ce Dan Allah ki barni anan dan Allah Mama"
Kuka ta kara fashewa da shi yayin da Hajja Maryam tayi fatali da ita,
"tsinanniya mai bakin aku wallhi bazan maidaki ba kuma idan bakiyi gaggawar barin nan ba zan sa a illata ki, kai Fajaru ka maida ta ita Hajiyar in ta isa tazo min da zancen da ta aikoka dashi ta gani idan rayuwar ta bata bace ba."
Tana kaiwa nan ta shige hamshakiyar motar ta nufi ainahin cikin gidan.
Masu gadi kuwa jinjina kai sukayi tare da tausayi Manalin su.

Kuka take kamar ran ta zai fita har suka iso bakin get din Hajja Lawisa.

Ya gama kimtsa kayan sa so yake yabar garin kasacewar ba a jirgi zai tafi ba da motar sa.
submitting keys yazo yayi  yana kawo bakin get din gidan Hajiya Lawisa yaga ana fatali da manal.
"ke kam kin zama alakake ki shiga duniya yafiye miki tun da uwar ki taki ki a kowa bazai so ki ba mai mugun hali, wallahi ba inda zani dake kuma ita Hajiyar zamu hadu da ita idan ni zata shukawa rashin mutunci, maza ki tashi kibar nan kafin nasa karti su fyade ki su yadaki a titi."
Jin furucin ta na karshe yasa shi kasa karasowa a wajen, Manal kuwa hancin ta jini take zubar wa akan marukan da Lawisa ta yi mata.
Hajiya Lawisa bata ko ga Anam ba akan idanun ta sun rufe ta shiga mota drivern ta Fajaru yaja ta zuwa hilin jirgi.
Manal da jini ya gama wanke mata fuska ta mike cikin tsananin jin nauyin jikin ta, ta gaban shi ta wuce ba tare da tace masa komai ba ta nufi hanyar fita.
Dan karamin tsaki yayi ganin yana bata lokacin sa ya shige motar sa bayan ya bada mukalayyen gidan.
Mamaki yake a ran sa wace irin uwa ce ga Manal? Wani mugun hali take dashi da har uwar ta zata ki ta, tabe baki yayi da ya tuna lagos ne fa komai na rashin imani zai iya faruwa.

Tafiya take tana hada hanya bataji bata gani burin ta motar da take mata horn ta buge ta ko zata mutu ta huta da rayuwar ta.
"ke wace irin kurma ce? Ko kin haukace ne?"

NI DA ANAMWhere stories live. Discover now