page 1

11K 622 36
                                    

*Haske writer's Asso.(home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS 👑*

Billy galadanchi

Sadaukarwa gareki qawa ta gari *Fulany saddy*

*Ina rokon duk wanda ya bud'e wannan shafin daya taimaka yawa er uwata fad'imatu zahrah adu'a samun rahamar Allah,Allah ya fadada yakuma yalwata mata qabarinta ita da dukkanin musulmin dasuka rigamu gidan gaskia Ameen*

*Ina rokon Allah ya bani ikon rubuta Alkhairi da kuma abinda ze amfani al'umma baki d'ayanta Ameen*

01
A hankali yake sakkowa daga matattakalar jirgin na sama wanda ya sauka a farfajiyar filin jirgin saman sultan Abubakar 111 dake birnin sokoto,sanye yake da jallabiya me asalin kyau da kuma tsada saman kanshi hulace wacce akafi sani da tab'ani kasha hadisi, kallon farko dazakai kasan cewar lallai hutu ya ratsa fatarshi tako ina, se bayan daya rage saura masa steps biyu ya qarasa sakkowa sannan ya d'ago kanshi ya baiwa idanunshi abinci, murmushi ne ya sub'uce masa ganin ilahirin danginshi suna tsatsaye suna sakar masa lallausan murmushin da kallo d'aya zaka musu ka tabbatar suna cikin d'inbin farin ciki wanda yake har cikin zukatan su, idanshi ne ya sauka masa akan me martaba,wanda lokaci d'aya ya qarasa sakkowa ya nufeshi cikeda fara'a.....

Har qasa ya duka ya soma gaidashi yayinda shi kuwa ya sunkuya ya d'agoshi ya rungumeshi gaba d'aya, yafi minti d'aya ajikinshi kan daga bisani ya d'agoshi ya mika masa hannu suyi musabiha sannan cikin isa da nuna cikar kamala ta mulkin fad'in Nigeria matsayinsa na sarkin musulmi ya furta

"Assalamu Alaikum *ALI ABBAS* muna maka barka da zuwa" murmushi ya sakarwa mahaifinshi sannan yace

"Ameen wa Alaikassalam *ABI* Ina matuqar godiya da wannan karamcin" har a lokacin hannayensu suna a had'e a haka mahaifinshi ya qara rungumeshi sannan ya sake hannunshi yamai alamu dayaje su gaisa da sauran mutane.....

A hankali ya juya yaje ya gaggaisa da sauran sukazo tarbarshi tukunna yabjuyawa zuwaga Zuhair wanda shine babban Amininsa suka rungume juna, ganin me martaba ya juya gun mota ya sanya dukkaninsu suka juya suma zuwa shiga motoci bila adadin masu dauke da fad'awa da securities da akazo dasu domin tarar *ALI ABBAS*........

Yasha gaishe gaishe acikin babban gidan na sarkin musulmi Muhammad Lawal dake unguwar kan wuri a jihar sokoto,gidane me fadi da girman gaske, wanda yake dauke da manya manyan sassa daban daban wanda suke cikeda tarihi da kuma al'adunmu na hausa, kamar yanda koban fad'aba kowa ya sani sarkin musulmin Nigeria shine yake shugaban tar d'aukacin sarakunan dake fadin Nigeria, sam shi a tsarinsa ba girman kai ko wulakanta na qasa dashi, sedai kam lallai akwai cikar mulki da sarauta a masarautar ta sokoto......

Se bayanda yaci abinci ya huta sannan yayi wanka ya nufi b'angaren fulany Adama wacce ta kasance mahaifiya agareshi....Asaman kilisarta ya tadda ita zaune,tayi zama irinna mulki wanda tun tasowarshi hakan yasan tana nata zaman, qirjinsane ya mugun dokawa ganin yanda ta kawadda kanta tamkar batasan ganinshi yanda dai ta saba, gwiwa a sace ya qarasa ya zube domin kwasar gaisuwa, bata ansashiba ya sanya ya kalli bayin yace dasu

"Ku bamu wuri" sum sum suka wuce suka bar wurin ya tattare nutsuwarshi ya mayarda dubanshi zuwa gareta,har yanzu bashi take kallo ba,cikin qarfin hali ya furta

"Barka da yamma ummu,ina fatan mun sameku lafiya" batare data kalli inda yake ba tace

"Lapia lau Alhamdulillah yaro, ina fatan ka dawo lafiya" d'an sassauci yaji koda bata kalleshi ba, be zata zata ansashi haka ba

"Lapia lau na dawo ummu,ina matuqar godiya" shiru tayi shima haka sunfi 5 mnts a haka ba wanda ya qara cewa komai, gyaran murya tayi sega wata baiwa tazo da sauri aqasa

ALI ABBASDonde viven las historias. Descúbrelo ahora