page 22

2.9K 226 28
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

*Kota yaya zan soma kwatanta kirkinki agareni pheey? na sani alqalamina ma bashida qarfin daze iya rubuta yawn alkhairanki agareni,Allah ya saka miki da alkhairi ya sanya alkhairi da albarka me tarin yawa arayuwarki*

22
Har manga ta juya ta hango yanda huddy ke murmushi seta juyo gaba d'aya ta had'e jikinta da nashi wuri d'aya,sumba ta manna masa a goshi sannan tace tana riqe da hab'arshi

"Amma Boo kasan baze yiyu mu shiga hakkinta ba ko, kwana na nawa dakai? Idan dai ba rigima kakeso kamun ba kuma kasan yanzu banida maganin qishirwarka yana hannun Aunty huddy,nayi qoqarima kasani fa bawai sabawa nae ba amma haka nake daurewa,yau kuma Allah ya qwace ni seka zo da rigima,dan Allah ka ka tausayamun" tsororo yayi yana mamakin sauyawar akalar zancen lokaci d'aya ya gano wata wutar takeso ta kunna masa

"Amma manga dukda haka cikin gidan zasumin wani kallo ida.....bakinta ta had'e da nashi ta hau tsotsa tayi 1mnts tana aiki d'aya shiko yakasa komai kurun dai ya riqo qugunta ne, sakeshi tayi tana murmushi

"Nasan wannan zakafi missing, ga shinan na d'an baka, yau Allah ya qwaci bakinnan nawa, da kake kwana kana dirxa" murmushin dai ya sakar mata ya gano ta rigada ta gama da matsalarshi hannunshi ta riqo

"Kayi hakuri na kwana a d'akinnan,bandani dakai se kuma huddy waye zesan an raba mana kwana, kaje ka bata haqqinta datake ta magana akai, sanin kankane cewar babu macen dazata had'a jiki dakai taso kuma ku rabu koda na wuni d'aya ne, banaso kayi tunanin ban damu dakai ba yanda zakayi rashina na kwana daya haka nima zanyi matuqar kewarka kaji" ta qarashe maganar tana me shafar sajensa ta langwab'ar dakai" murmushi ya sub'uce masa lokaci d'aya yaji gaba d'aya ta burgeshi yama manta da huddy a wurin, janyota yayi ta fad'a jikonsa yace yana shafar sumar kanta a hankali

"Tunda kin matsa ba komai, amma kiyi adu'a kafin ki kwanta plss,kuma ki riqa tunawa dani kima tabbatar kinyi mafarki na kinji Hilwa?" qayatacce murmushi ta sake masa sannan ta zame jikinta a nashi

"Ko tare dakai na kwana mafarkanka ke cikashe faifan baccin danake boo,karka damu kaima sekayi nawa, ka tabbatar yau munyi komai damuka saba a mafarki" manna mai sumba tayi a wuya ta juya sannan tace

"Aunty huddy seda safe, yaa Ali acika alqawarin daka dauka yau plss" shiya gane inda Manga ta dosa na zancen alqawari yayinda huddy ta cika ta batse sabida ta zata alqawarin mafarkin dasuke Manga ke nufi, miqewa tai fuuuuuu ta wuce zuwa d'akin nasu kasa ma daurewa tayi ta sanya kuka, shi kuwa sun barshi sororo a wurin yana mejin dad'in qalaman Manga ya qurawa d'akin data shige ido ya kasa janyewa, matsawa yayi kusa da d'akin ya soma knocking a hankali, matsowa Manga tayi ta rungumi qofar sosai hawayen datake ta hanawa su zubo sanda sukayo ambaliya zuwa kuncin ta gashi tayiwa qofar key koda batawa qofar key ba bazata tab'a bud'e masa amma kam tanajin wani qaunarshi da sha'awarsa na fizgarta.....a hankali tace

"Waye?" cikin rarrashi yace

"Manga dan Allah ki bude sallama kurun zan miki" murmushi tayi me quna tace

"Yaa Ali kayi hakuri banaso in ganka zan shiga tashin hankali kasani na soma sabawa dakai gwara ka barni haka nan plss,kuma dan Allah karka kuma bud'e bakinka jin muryanka kad'ai bakasan kalan kasalan dayake saukar mun ba, indai kana sona ka juya abinka kawai" jiki a mace ya juya zuwa d'akin da huddy take a kwance ya tadda ita tana ruwan hawaye da sauri yayi kanta ya riqota yace

"Haba hudaisa,menene ya sanya kike so ki b'ata rawarki da tsalle? Yayana ana yabonki sallah zaki kasa alwala? Kinsan kuwa shirmen da kika tafka agaban qaramar yarinya, bansanki da haka ba yaya zaki bari kishi ya rufe miki ido ki janyowa kanki raini awurin qaramar yarinya sabida qaddarar kishi ta had'aku, sam ki sauya tunani idan haka kika shirya yi" tsaki taja masa ta miqe tana wurga masa wani kallo....

ALI ABBASDonde viven las historias. Descúbrelo ahora