page 24

2.8K 210 12
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Sadaukarwa gareki qawa ta gari Fulany saddy*

                   24
Ganin Ali Abbas na neman zaucewa ya sanya sarkin agadez yayi gyaran zama cikin hikima

"Tabbas kuwa nima na goyi bayan ka, gwara a raban auren nan a yanda na kulama ita kanta bason yaron take ba dole ake mata, sabida haka kai Ali Abbas tashi maza muje ka rubuta mata takardar ta kowa ya huta" da sauri Ali Abbas ya kalleshi yana mamakin kalamanshi seya hango yana mai da ido sadda kanshi yayi qasa yace

"Dan Allah kumun rai wlhy manga ce rayuwa ta,namuku alqawarin zan kula da ita fiye da yanda zan kula da kaina, zan sota fiye da yanda zanso kaina, zan qaunaceta fiyeda yanda zan qaunaci 'ya'yan dana haifa da ciki na,dan Allah ku barni da Manga wlhy matana tana sona" miqewa sarkin agadez yayi

"Babu wata magana sarki me adalci ya gama yanke hukunci, muje masauki na baka biro da takarda kurun,kuma uku zaka rubuta sabisa ka sani ba gyara har abada" sarki kuwa dad'i ya gama kamashi se murmushi yakeyi ya miqe  shima yace..
"Naji dad'i matuqa daka fahimceni Aminina wannan yaron sam baya qaunar jinin mu,sabida haka na barka dashi lallai ya rubuta ya aiko nan da kwanaki uku kona kaishi kotu niba ruwa na ka kuma sani" miqa masa hanni yace

"Bakada matsala kurun ka tsame hannun ka barni dashi,ai Ali Abbas jinina ne sabida haka lallai zan tilastashi ya sakar ma jikar ka" kallonshi yayi sabida lokaci d'aya yaji maganarshi tazo masa da alamar harshen damo yace

"Haba Abokina? Yazakace jikarta kuma? Jikar mu dai ko?" murmushi yayi cikeda takaici yace

"Gani nayi Hafsatu Manga nance masarautarta ta uba, sannan Ali Abbas bashida alaqa da kowa a gidannan dani yake da alaqa, naga kuma kamar yanda zansa ya sake maka jika haka kaima zan daura maka wani nauyin na sanya Ibrahim ya sakar mun yarinyata kaga kenan Manga na hannunka ubanta yana hannunka sun dawo masarautar su, Innoh kuma dama wahalar datash ta isheni har aikatau duk a sanidiyar muzgunawar d'anka ya aureta bayaso, kaga bayaso ya saketa kazalika Ali Bayason Manga ya saketa duk abinda Manga tagani abinda ubanta ya aikata ne ake maida masa abinsa, sabida qiyayyar Innoh yabar qasar nan dan kawai a nuna masa kuskurensa shisa tun a duniya kaga mijin 'yarsa ya mata basaja sabida qiyayya, shiya bar gida da kowa da kowa nasa yayinda surukinsa ya gudu yabar masa er tasa agida, shin wanene yake girbe abinda ya shuka anan?? Shine ko itane?" zufa ce ta soma karyowa Mahaifin Iro yasani kaf Niger republic babu wanda ze baiwa d'anshi auren 'yarsa a yanzu irin wannan mugun abin daya aikata kowace masarauta tasan ya gudu yabar garin akan anmasa auren dole gashi shi kuwa daya baiwa Iro damar auren talaka gwara yaga gawar Iro

"Yanzu Aboki irin rashin karar dazaka nunamun kenan baka kojin kunya ta? Yanzu dama ashe akwai ranar dazata zo ka nuna baka kaunar j8nina? Lallai kazo da wata magana kuma inshaa Allah Iro baze saki Inno ba har abada" mahaifin innoh kurun soma tafiya yayi yayinda dukkanin wanda yazo dasu suma suka miqa harya kai kofar barin fada yace

"Nanda kwanaki uku zan aiko da takardar sakin Manga, amma da sharad'in senaga takardar sakin Inno nanda kwanaki ukun, duk wanda ka aika yakai takardar inshaa Allah namaka alqawarin shine ze dawo da takardar sakin Manga ya kawoma" zufa se keto masa yayinda Baban Manga hankalinshi yakai maqura wurin tashi, shi akeso akashe anan ga mutuwar aurenshi da macen dayake ga harya koma ga Allah baze tab'a samun nagartacciya irin taba, ga kuma mutuwar auren ersa mafi soyuwa agareshi!!!! Haka suka fice batare da Baban Manga ya koda motsa ba, mahaifin shi ya mayarda dubanshi zuwa ga reshi yace

"Kayi hakuri zansan yanda za'ayi na karbo takardar sakin Manga batare daka saki Innoh ba, ka sani wlhy bazan bari su lalata ma rayuwa ba so yake ka auri er talaka in shiga uku na, yasani tunda ka gudu da mace babu wacce zata sake aurenka daga wata masarautar har abada, nize b'atawa suna ya sanya jinina ya auri er matsiyata yayi kad'an kuma" qurawa mahaifin nashi ido yayi,amma ya kasa furta komai aranshi yake mamakin hali irin na mahaifinshi wato shi sam beji wa'azi ba haryanzu beyi karatun ta nutsu ba, duk wannan abin daya faru beyi realizing cewar ya aikata mummunan kuskure ba, aranshi yace wannan karon sam bazan lamunci wannan rashin adalcin daga wurin mahaifina ba, a zahiri kuwa miqewa kurun yayi yabar fadar gaba d'aya batare dayace kanzil Ba....

ALI ABBASKde žijí příběhy. Začni objevovat