page 20

2.8K 211 9
                                    

*HASKE WRITER'S ASSO. (Home of expert and perfect writer's)*

*👑ALI ABBAS👑*

*Billy Galadanchi*

*Sadaukarwa gareki qawa tagari Fulany saddy*

*Pheey wannan shafin nakine ke kad'ai kiyi yanda kikeso dashi, ke kadai ce kika kirami a waya tun bayan da sanarwan rashin lafiya a ya sameki, ina roqon Allah ya sanya Alkhairi da Albarka arayuwarki, Allah ya shiryar miki da zuri'a ya baiwa 'yata Amira lafiya ya kuma bar zumunci....Ina yinki sosai pheeeyyyy.....*

20
Zama a bakin gadon yayi ya dafe kanshi, duk yanda yake tunanin kunyar nan data bashi abin ya wuce hakan agareshi, yaya zanyi da Manga? Ya tambayi kanshi miqewa yae jiki ba qwari ya sameta a parlor kallon shi tayi bayanda ya zauna a kusa da ita, qamshin datake fitarwa be saba jin irinshi a jikinta ba yanayin shigar da tayi yanzu ta tafi da imaninshi, riga ce acikinta iya cinya ta d'ame ta asama yayinda qasan yake a bud'e rigar kalar pink ce ta taje sumar kanta tayi parking dinta a tsakiyar kanta jelar ta sauka har gadon bayanta, qafarta d'aya akan d'aya tana riqe da cup da milkshake data hada da kanta tana kurba a hankali, yatsun qafarta ya kalla yaji wani yar yanda suke zara zara farare qal nails dinta sunsha ado da lalli baqi....tayi masa kyau ainun, yanda yake bin ko ina nata da kallo haka takebin qwayar idanshi dake juyawa da kallo, sa'ilin da ya mayarda dubanshi zuwa gareta suka had'a ido seda yaji wani jiri ya dauke shi, yauce rana ta farko da yaga idanuwanta manga da kwalli sam bata shafa kwalli, kuma seya masifar fito da dara daran manyan eye balls dinta dake black shar ga wani blue dayake kewaye dasu me daukar hankali,gefen farinnan ya qara haske sosai se lumshe masa su takeyi tana murmushi ganin ya kasa dauke idanshi acikin nata ya sanya ta kawar da nata maganar mama ta tuna

"Manga mesa bakya sakawa idanki kwalli?" murmushi ta mata

"Mama kwalli ai qauyancine yanzu ba'a yayinshi ni tun ina secondry school rabon dana shafa" tsaki maman tayi..

"Kufe garin neman a sanku ake mantawa daku, bari kiji wlhy hafsat kwalli shine mace duk wata kwalliya dazakiyi bazata fito ba seda kwalli, shi kwallin nan da kuke rainawa ba kamar wai sauran kwalliya bane da zakiga kinyi iyakar ta fuska, bari kiji abubuwan da kwalli keyi

*Kwalli yakan taimaka wurin kare cututttuka daga shigar wa mace ido*

*kwalli yana isar da saqon zinariyar mace acikin zuciyar mijinta, duk sanda kika saba ida idanuwanki suka sarqe dana mijinki zakiga ya masa dauke nasa a naki,akwai abubuwan dashi yake ganinsu amma ke baki san dasu ba*

*Kwalli kwalliyace dake tsayawa a zuciya da idon namiji ko bayan kin wanke, saqon dayake isarwa har cikin b'argon sa yake shiga ko bakwa tare zeke tunawa da wannan qayataccen ruwan zaibar dake zagaye da baqin idanki yana jin wata kasala*

*Duk yayinda kika sanya kwalli kafin kuyi kwanciyar aure da nijinki ki tabbatar idanuwaku sun gauraya da nashi na tsawon sakan goma ko fiye zakiji banbanci*

*Kwalli shine yake raba gaddama tsakanin wanene namiji wanene kuma mace......ki kula duk sanda bakida kwalli koya kika kai qarshe wurin iya kashe ido bazeyi tasirin idan kika saka kwallin ba*

Murmushi Manga tayi sabida taga sauyi sosai a wurin Ali Abbas yau, ya kasa dauke idanshi a nata, ajiye cup dake hannunta tayi sannan ta sanya hannayenta duka biyu ta zagaye bayanymshi ta d'aura kanta saman qirjin sa tace a hankali

"Na manta ban sanar maka ba" dan d'agota yayi yace "Menene?" murmushi ta sake sakar masa sannan tace

"Dama zan sanar maka ne kayi kyau matuqa" murmushi ne ya sub'uce masa,lokaci d'aya yana mamakin sauyawarta yanzunnan fa ta gama masifa,hannu ya sanya ya shafi sumar kanta dake matuqar burgeshi sannan ya sumbace ta a goshi yace

ALI ABBASWhere stories live. Discover now