Da kallo kawai tabishi harya kurewa ganinta, ahankali ta sauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu tana tunanin yadda zata shawo kan Elmoudan gabadaya gareta, domin yanzu taga wani tashin balagar tsintsaye yake ji dashi don haka zata nuna masa cewar amata ita dabance wato tana da banbanci dasauran matan dayake tunani, har duniya ta nade namiji be isa ya taka ta yazauna lafiya ba duk da matsanancin son datake masa, bade akan siblings nashi da hajiya yake mata haka ba?? Jinjina kai tayi tareda yin kwafa irin I am going to deal with you dinnan, daga nan toilet tafada ta sheqa wanka da kwalliya tadawo kan gado tasoma aikin danne dannen waya, babu dubaga ga dattin da dakin yyi dakuma zuwa taya su hajiya hada breakfast, bin lafiyar gado tayi hankali kwance suna hira da Ziyada ta WhatsApp, kiran Haj Halima ne ya katse mata hirar, cikin hanzari tayi picking wayar tareda karawa bisa kunnenta, "hello mummy ina kwana ".. "Lafiya kalau sweetest daughter "cewar hajiya halima ta dayan Barin, tachigaba da fadin "hope kina lafiya sannan dafatan baya takuraki, if yes yana takuraki kifada min tun wuri dan wllhi if I find out baze ji da dadi ba ".. Njmfashi taja ahankali tace"mummy kinsan de bana boyemiki damuwata ko? Then believe me when I say this baya takura min "... "I believe you dearest Kinsan am so indebted to you banason wani slightest abu yasameki domin komai kankantarsa it is super infectious to me".. Wani sanyin dadine yake shigar duk wata kofa ta jikin inteesar "I know mummy, shiyasa nake mutuwar sonki, Allah ya barminke cikin koshin lafiya ".. "Amin mummy. ''Tachigaba da fadin "namanta ban fada miki Muna kaduna ba. ".. "Me kukaje yi? ". Cewar Haj halima with much serious. "Oho musu jinayi yace zaije shine nima nabishi sabida tsaro, kilan rashin ganina yasa asoma munafurci, dan Naga tsananin mamaki written all over thier faces"... "Dan bakin ciki sede ya mutu, dan haqarsu bazata taba cimma ruwa ba dagashi har uwarshi,Wato so suke su ganki alalace bbu kyan gani d'ansu na gara ki ko? ".. "Yeah haka suke nufi from there expressions "... toh kuwa over my death body 'yata tashiga halin kunci saboda wani d'a namiji.".. "Wallahi kuwa "inteesar tafadi tana dariya, haka suka chigaba da hirarsu hankali kwance kimanin mintuna ashirin sannan suka katse kiran.Tabangaren Elmoudan kuwa cikin tafiyarsa ta cikakken namiji mai jini ajika yanufi part din hajiya, afalo yaganta zaune itada su Ashnoor, ganinsa yasa ta fadada fara arta, se kuma ta tsuke fuska tace"ina diyata? "Yana shirin zama yace"tana bacci".. Kallon tsanaki Hajiya tamasa sannan tace"ohhh ohk"daga nan tayi shiru tana tunanin rashin kwanciyar hankali dake tattare da Elmoudan gamida rashin kulawar matarshi gareshi, girgiza kanta tayi a hankali tana me bakin cikin rashin dacen matar da Elmoudan yayi wanda by mere looking at him zaka gane,gabadaya ya canza ya tashi daga gwarzon namiji yakoma wani shushushu, runtse idanuwanta tayi tana adduar All ah yakawo masa sauki yakuma yaye masa, sannan itama zata kuma tashi tsaye akanshi da addu'oi. "Hajiya tunanin me kikeyi? "Ta tsinkayi muryar Elmoudan, kallonshi tayi tareda sakin murmushin yake tace"naam Elmoudan me kace?". Kallon tsanaki yamata sannan yace"hajiya something is bothering you, fada min mene ne? ".. Murmushi tai tace"bbu komai".. "Hajiya sau kusan uku ina gaidaki baki amsa bafa sannan kice min you're alright? ".. "Elmoudan I'm very fine I promise you".. Jinjina kanshi yyi a sanyaye sannan yazamo daga kan kujerar ya dukar dakanshi yace"ina kwana hajiya? Dafatan mun tashi lafiya sannan babu wata matsala ko? "... "Lafiya kalau Elmoudan, matsalar kuma da sauki Allah ya rabamu da ita gabaki daya".. "Amin"gabadaya sukace harda baby da Ashnoor kafin daga bisani suma su gaida yayan nasu, ahankali Hajiya tafurta"kana ganin lafiyar inteesar kalau kuwa".? ''Meya faru? ".. "Kalli time, it's 30minutes past eleven fah".. Murmushi yyi yace "lafiyarta kalau"jinjina kai Hajiya tayi sannan takuma cewa" ga abinci can a dinning bismillah don mu tun wurin 9 muka karya". "Toh Hajiya Allah yabada lada"yafadi tareda mikewa ya nufi dining yana cewa"baby come and serve me mana", mikewa tayi jiki bbu kwari ta isa dinning din, tajuyo da plate ta zuba masa French fries da omelet se plantain da liver sauce, gabadaya falon ya bade da kamshin abincin, "thank you"yace ma baby bayan tahada masa Lipton, cin abincin yyi sosai yana wani lumshe Idanu domin baze tuna when last yaci abinci me dadi da gardin wannan ba, ahanzarce yakarya dubaga kiran Muhd daya riqa shigowa wayarshi, batareda yyi picking ba ya mike yakoma falo inda har yanzu su hajiya suke, tsugunnawa yyi agabanta yace"hajiya zan fita inga su Muhd"."OK toh Allah yakiyaye ya tsare yadawo dakai lafiya, katafi cikin aminci kadawo cikin aminci "Hajiya tafada tana sakin wani kayataccen murmushi, shima murmushin kawai yakeyi domin bakaramin jin dadin adduar data masa yyi ba, mikewa yay yafita cikeda tsananin son hajiya, wata kaunar ta me tsafta nakuma shigarsa, shi kadai yake ta faman murmushi har yyi driving off.
