Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace "alright muje to"ta fadi hakan ne tana me yin hanyar bedroom dinta,da kallon mamaki yabita kafin yayi wani motsi yaga ta fito jikinta sanye da mayafi,murmushi ta mishi ta mishi sanda suka hada ido hakan yakuma karyar masa da zuciya,sai da yabari tazo daf dashi sannan ya jawo hannunta yana mai kallon kwayar idanunta,kawar da kanta gefe tayi tana kallon wani wurin cikin wani irin yanayi,.Kallon fuskarta ya shigayi batareda yace komai ba har na tsawon mintuna uku,"muje"yace ya soma tafiya,bayanshi tabi suka karasa part din inteesar wacce ke zaune afalo hankalinta ya karkata ga tv,sallamarsu ce ta dawo da ita daga duniyar kallon datakeyi ta mik'e fuskarta dauke da murmushi ta rungume Jidderh sukayi musabaha,tsananin mamakin inteesar Jidderh keyi,murya can kasa kasa Jidderh tace "ina kwana anty?mun tashi lafiya?"tana me jan Jidderh tace"lafiya kalau Jidderh hope same?"gyada mata kai tayi tareda sakar mata murmushi sede ganin sunyi hanyar fita yasa Jidderh kallon inteesar da mamaki,murmushi kawai inteesar din tayi bata ce komai ba,daga inda yake yace"my forever ina zakuje?"..juyo tayi tace"yanzu zamu dawo"bata tsaya jin abinda zaya ce ba suka shiga part din Jidderh,direct dining suka nufa,da murmushi inteesar tace"taya ni dauka'".kallon inteesar din tayi da mamaki tace"yaya fah yace a site dinki zamuyi breakfast".."bana son jin wata magana,ki dauka mutafi"narai narai Jidderh tayi da ido tace"idan fah yayi fad'a?"wani mamakine yakama inteeesar wanda seda ta dago tana kallon fuskar Jidderh,wannan yarinyar ce ke yin wannan maganar?murmushi tayi tace"kada kidamu bazaiyi fada ba Insha Allah "ba dason ranta ba suka dauki warmers din zuwa part din inteesar.yana zaune yana daddanna wayarshi suka shigo,kallo d'aya ya musu baice komai ba yashiga da abinda yakeyi,inteesar na daga wurin dinning tace"mijinmu bismillah,ko a falo zakaci"duk yadda yaso daurewa kasawa yayi yace"a dining zanci".yana fadi hakan ne yana me mikewa daga zaunen dayake yakoma wurinsu,zama yayi yana kallon yadda inteesar ta shaqe masa plate da abinci,wanda rabi nata ne rabi kuma na Jidderh,haka zalika suma haka ta zuba musu cikin plate d'aya,da murmushi tace ma jiddeeh"bismillah muci"d'an nokewa tayi inteeesar takuma fadin"to ko da mijin namu zakici?"waro ido tayi cikeda mamaki gamida kunyah ta girgiza kai kawai tana me fara cin abincin,"shine ni kika wa re ni ko my forever?"yafadi yana mai shan tea.dariya tayi tace"inason kaci abincin da kyau ne amma daga yau bazamu kuma ware ka ba"kafadarshi ya daga yace"noo kibarshi sai ma dana roka?"tayi farr da ido sannan tace"sanin kanka kafi karfin hakan ko sisina?"tana mai maida akalar maganar ga Jidderh,murmushi kawai Jidderh tayi batareda tace komai ba,"bawani nan dadin baki kawai kike son yimin"ta waro ido tace"kai my forever shaidar dazaka min kenan?"yace"to ai shaidar kirki ce"tace"awurinka ba?"yayi murmushi yace"har awurinki ma"dariya tayi tareda girgiza kai.Wayar jiddeeh ce tasoma ringing,kallon mai kiran tayi sannan tadauki kiran da murmushi tace"ina kwana rabiu?"daga can bangaren yace"lafiya kalau Jidderh amaryar ahmed "murmushi tayi tace"tsokana ko?"yace"ai tun ranar dana kawo miki past questions na fahimci wani al'amari daga gareshi,yana sonki jidderh"lumshe ido tayi tace"waya fad'a maka?"yayi murmushi yace"ai abu ne mai sauki ba sai an fada min ba,it's written all over your faces"ta washe haqora tace"sharri dai zaka mana"yayi dariya yace"ba wannan ba guess what?:"ta dago kai alamar tunani suka hada ido da elmoudan,ganin irin kallon dayake mata yasa tasha jinin jikinta,tace"kafada min kawai.bazan iya guessing komai ba"yace"as if I know,kin samu admission a BUK"nan da nan tasaki wani kayataccen murmushi tace"which course?"yace"B.Pharm".. tace "Alhamdulillah nagode da wannan albishir din"yace"worth more zaki iya zuwa gobe ki karbi admission letter dinku"tace"alright nagode sai anjima"tana sauke wayar inteesar tace"congratulations wani course suka baki?.tace"thank you B pharm"..inteesar tace"wow congratulations once more".."thank you Jidderh takuma fadi akaro na biyu,da mamaki inteesar ke kallon elmoudan ganin yaji sarai abinda yasamu Jidderh amma yayi biris baice komai ba,koda yake matarshi ce kila bata wannan sigar zayayi congratulating nata ba,tabangaren shi kuwa wani azababban kishi ne ya dirar masa,seyayi maganin wannan lamarin,cikin fushi ya mik'e yashige bedroom din inteesar.da kallo kowacce tabishi batareda sunce komai ba.Dining din suka gyara sannan suka nufi kitchen,Jidderh tace"Anty barshi kawai zan iya yi ni kadai"inteesar tayi murmushi sannan tace"alright"tana me zama akan kujerar dinning din dake kitchen,saida ta bari Jidderh tafara wanke wanke sannan tace"Jidderh inason yimiki wata magana"juyowa Jidderh tayi mamaki tace"toh anty ina jinki"inteesar ta nisa sannan tace"baki lura mijinmu yaji haushi ba?"dagangan Jidderh tace"haushi kuma?"saboda ta tabbatar da kila ma tafi inteesar fahimtar yayi fushin,inteesar tace"ehh,kuma ba komai ya sa yayi fushin ba sai yadda kika yi waya da rabiu,kisani fah mijinmu nada matukar kishi"ajiyar zuciya tayi tace"yanzu wayar ma tazama laifi?"girgiza kai inteesar tayi tace"yin waya ba laifi bane amma kidena sakankancewa tamkar yadda kikayi dazu idan kin duba ai shi yaron ba muharraminki bane"jijjiga kai Jidderh tayi alamar gasagata maganar inteesar sannan tace"nagode anty insha Allah zan gyara"murmushi inteesar tayi tace"babu komai,ai haka zaman taren yake,sai kema kiyi kokarin fahimtar dani aduk sanda nayi ba daidai ba,idan kin kammala sai kije kibashi hakuri,komai zai wuce"hawaye ne yasoma zubowa Jidderh takasa controlling dinsu "anty kin min halacci arayuwa,you'll always be remembered"mikewa inteesar tayi ta rungume Jidderh tanajin son yarinyar na kuma shigarta.elmoudan dake bakin kofar kitchen din yaji wani farin ciki ya mamaye masa zuciya,hakika babu abinda yafi samun nutsuwa da farin ciki dadi arayuwa,bai taba tsammanin zaiyi witnessing irin wannan ranar ba,se gashi Allah alhakamu ya nuna masa,ayadda yakeji yafi kowa sa'ar mata aduniya,batareda sun ganshi ba yakoma bedroom ya kwanta yanajin wani sanyin dadi na ratsashi.Bayan Jidderh ta kammala aikin tace"Anty me za'a dora?"tayi dariya tace"kada kidamu,nayi ma Mami waya nace ina sha'awar danbu,zata aiko mana dashi,ai zakici ko?"murmushi Jidderh tayi tace"sosai ma,danbu x one of my favourite ai"daga nan ta nufi site dinta tana tunanin ta yadda zata baiwa elmoudan hakuri,saida tayi sallar azahar sannan ta shiga wanka,wata riga da skirt din lace mara nauyi tasaka,dinkin ya zauna daram ajikinta yayi mata matukar kyau,powder da lip gloss tayi applying sannan ta kuna burner tasaka turaren wuta da roomfreshner,a kan doguwar kujerarta ta kwanta tana me kiran Mami awaya,tamkar jira takeyi tadaga wayar,"ina yini Mami?ya gida da abba?"murmushi Mamin tayi tace"lafiya kalau,ya naku gidan?".."lafiya Lau,Mami nasamu admission a BUK"tafada cikeda murna,dariya Mami tayi tace"gashi anan ma dan har abbanki ya karbo miki"cikeda murna tace"Alhamdulillah,sai nazo karba kenan"Mami tace"a'a kibari zan aiko miki dashi ko kuma mijinki yazo ya karba,din yadda ake ciki dai zan sanar dake"ajiyar zuciya Jidderh tasaki tareda lumshe idanu tace"bazaki aiko da abinci ba?seki hado dashi"dariya Mami tayi tace"Lamtana zan baiwa admission letter din taki?"dariya jiddeeh tayi tace"a'a a'a kibarshi dan Allah inde ba so nake ta la'anta shi ba"suna cikin wayar elmoudan yashigo part din bakinshi dauke da sallama,rasa yadda zatayi tayi daga karshe dai tayi shiru tachigaba da waya da maminta,dakinshi straight yawuce batareda yakuma cewa komai ba,se bayan mintuna goma sannan suka katse kiran,dafe kirjinta tayi tana tunanin ta yadda taza shiga dakin nashi,dakyar ta saisaita kanta ta bishi dakin kirjinta na dukan tara tara.Mirda handle din kofar tayi ta shiga dakin bakinta dauke da sallama,amamakinta yaji yace "waalaikumussalam "saide ciki ciki yayi maganar,kasa motsi tayi bayan wasa da fingers dinta data somayi tama rasa ta inda zata fara,murya na rawa tace"yaya kayi hakuri"dagowa yayi ya kalleta tsabb sannan yace"hakuri kuma?ni me kika min?"dagowa tayi takallashe shi alokacin ya saukar da idanunshi daga gareta,murya can kasa tace"akan wayar danayi da rabi"u"murmushi yayi yace"ki karasa shigowa dakin in har magana kike son muyi "tamkar mai ciwon kafa haka ta rinqa jan kafafunta harta karasa gabanshi,tunda tasoma tafiyar yake kallonta da mamaki,cikeda dan rudewa yace"yadai kafar taki?meya faru?"murmushi tayi tace"babu komai"..."ban gane ba komai ba"cikeda karaji yayi maganar,jin yasoma fad'a yasata sulalewa ta zube awurin hawaye na zubo mata. ...aduk tunaninsa batada lafiya hakan yasanyashi saurin zama akasa yana me jawo ta jikinshi,wuyanta yasoma tabawa kozaiji zazzabi,jin homeostasis din ta is normal yasashi sauke ajiyar zuciyar dabai shirya yinta ba.ahankali yasa hannu yana share mata hawayen voice can kasa kasa yace"hayatee stop crying,,tell me meke faruwa?are you sick?"ajere yake mata tambayar,saida ta d'an zame jikinta daga nashi sannan tace"nace ba komai I'm just scared kada kaji haushi"murmushi yayi yana me kuma jawota zuwa jikinshi yace"my naughty hayatee,kina son nasamu heart attack ko?"cikeda firgici ta dago da fuskarta tana kallonshi,ga tsananin tsoro daya bayyana akan fuskarta tace"Allah nima heart attack din zaya kamani".."are you kidding?"yace yana mai yin dariya,murmushi tayi tace"nide ban ce ba,in fact banyi magana bama"dariya yayi yace "I see"ta d'an gyara dankwalin kanta tace"I'm so sorry ya omri,insha Allah bazan k'ara ba"yana kuma rungumeta yace"you did nothing wrong hayatee,I love you baby"murmushi tayi batareda tace komai,yace"won't you say you love me too?".farrr tayi da ido tace"same"yace"ban yarda da wannan wayon ba" tace"Allah ba wayo bane"ya girgiza kai sannan yace"toh ban hakura ba kuma bazan dena yin fushi ba"arud'e ta ce"I'm sorry"yayi dariya cikin ranshi yace "Allah bazan hakura ba har se kin ce min I love you ya omri,sannan kiyi kissing mawa with all you got,make me feel more like a king mana"tunda yafara magana take sauraron yadda yake fitar da words din one by one yana wani lumshe idanu,kasa cewa komai tayi banda kallon kafarshi datakeyi wacce take tamkar ta mace sabida laushi,santsi dakuma taushi,yakuma cewa"tashi ki tafi tunda bazakiyi ba"narai narai tayi da ido tace"yi haquri "yace"ni babu abinda kika min,dan haka kidena bani hakuri just get out of my room"jin yama sounding serious yasata mikewa tayi hanyar fita,shima da mamaki ya mike yana me juya mata baya,bai ankara ba yaji tabashi wani arnen hugg tabaya wanda yasanyashi sakin ajiyar zuciya yana murmushi,birkito da ita yayi ta gabanshi yayi cupping face dinta tareda lumshe idanu,babu zato babu tsammani tayi sauring owning lips dinshi,sai bayan five minutes sannan tasaukar da kanta tana sauke ajiyar zuciya,murmushi yayi yace"I love you hayatee".."I love you tooo ya omri".wata runguma yakai mata cikeda tsananin so da kaunar juna yana jin dama wannan moment din should last forever.*1 month later*
Misalin karfe goma sha biyu da mintuna na ranar asabar Jidderh tagama shiryawa cikin wata atamfa super gold edition dinki Riga da skirt,fasalta yadda kayan suka zauna ajikinta bata lokaci ne,zama tayi afalo tana jiran elmoudan yadawo daga part din inteesar dan mata sallama,tunanin zamansu tachigaba dayi tana ganin tamkar komai amafarki yake faruwa,yadda inteesar ke mu'amalantar ta da juriya gamida hakuri ga tsantsar kaunar da mijinta ke mata,har wata yar kibar kwanciyar hankali tayi takara fari sosai,tana cikin wannan tunanin elmoudan yashigo yana me fadin "fitar nan bazata yiwu ba yau,maman baby batajin dadi"tayi narai narai da fuska tace"Allah sarki anty inteesar,alright babu komai bari inje inga jikin nata"tana gama fadin haka ta mike zata bar falon,saurin jawota yayi zuwa jikinshi yana murmushi,itama murmushin take masa yayinda yake circling lips dinta yace"just kidding,muje in kaiki dan nayi sauri na dawo kinga babu kowa agidan"tadan turo baki tace "meyasa anty inteesar bazataje ba?gidan ai ba bakonta bane"yace"tana son baku privacy ne shiyasa"murmushi tayi tace"wani privacy kuma?kawai dai bata ra'ayin zuwan ne"murmushi yayi yace"tanada gaskiya,bai kamata zakije gidanku for the first time ba tabiki""bawani nan kila ma kaine ka hanata"..waro ido yayi yace"auuu sharrin dazaki min kenan "dariya tayi shikuma yasoma kokarin owning lips dinta,had'e rai tayi tace"ya omri my lip gloss "yayi dariya yace"dama ai saboda ni kikayi applying koba haka ba?"tace"ni o'o sabida mamina nayi applying"ya bude baki alamar mamaki yace"ai ko zaki fasa zuwa"kafarta tasoma bubbugawa yace"inyeee wannan irin buga kafa haka?bari in zauna kichigaba da buga wa"waro ido tayi tace"sorry"yace"i don't want sorry,I want kiss"murmushi tayi tareda rufe bakinshi dawani musulmin kiss,dagowa tayi tace"muje dan Allah"yace"saiki kara min"tace"haba dan Allah"yace"Allah kuwa "murmushi tayi tace" I promise you amma se da daddare "yayi murmushi yace"better,let's go"riqe mata hannunta yayi suka fita,shine yabude mata mota tashiga yarufe sannan shima yashiga yasoma driving,suna ta faman fira har suka karasa gidansu Jidderh.. yana parking tayi saurin fita ta shiga cikin gidansu da sauri,Mami tagani atsaye sai sister's dinta zaune sunata fira,dagudu taje ta rungume Mami suka gaggaisa sannan takarasa wurin sister's dinta,suka rungume juna suna yaushe rabo,se bayan Mami da elmoudan sun gaisa sannan ya juya yakoma gida.da mamaki Mami ke kallon diyoyin nata wanda ko basu fada mata ba tasan suna cikin kwanciyar hankali,dan kowacce takara fari da kiba.jasmine ce tace"Jidderh sai kuma daurin aure ya juye zuwa ga Ahmed,nayi matukar mamaki"dariya Jidderh tayi tace"nima nayi mamaki sosai dan ban saniba sai bayan ankaini"Aneesah tace"gaskiya ahwaz yayi ma Ahmed halacci"jinjina kai Jidderh tayi batareda tace koma ba,Sumy tace"yaya inteesar?".."lafiya kalau wallahi nayi nayi muzo tare tace wai a'a "daga voice dinki ma na fahimci kun fahimci juna,congratulations na tayaki murna".."kwarai dagaske anty inteesar nada kirki,she's not wat she seems to be"nan fa hira ta b'arke kowacce na kokarin baiwa yar uwarta labari.Sai bayan magrib kowacce mijinta yazo ya dauketa zuwa gida,a wannan satin Jidderh tafara attending lectures,dole elmoudan yadauko house helps mai tayasu aiki musamman idan Jidderh bata nan ita keyin komai girki dan komai inteesar keso elmoudan zai ajiye aiki yanemo mata sannan yakoma office,rayuwarsu couldn't be better,soyayyah ce tsantsar gangariya ke wakama a familyn elmoudan saide ace Masha Allah.ayanzu cikin inteesar yakai watan haihuwa haka zalika sister's din Jidderh duk suna dauke da juna biyu,sosai Mami ke kula dasu duk da ba unguwa daya suke ba.Ranar wata lahadi Inteesar ta tashi da ciwon nakuda inda tasamu santalelen baby boy,murna wurin Elmoudan,inteesar da Jidderh ba'a magana,son duniya aka dorawa yaron inda hajiya tace amaida Inteesar kaduna tachigaba da kula da ita,sunan baban inteesar aka sama yaron wato Abdullah zasu rinqa kiranshi da Aman.ranar dazasu wuce tamkar Jidderh tayi haka Inteesar,aka barta ita kadai tana ta faman tunani,aranar elmoudan yadawo kano,cikeda mamaki take kallonshi kafin tace"ya omri meyasa baka bari sai gobe ba?"yayi murmushi yace"sabida hayatee na,bazan iya kwanciya bataredake ba"murmushi tayi tace "kamar dagaske "yace"what do you mean by that"tayi murmushi tace"babu komai"yace"jiya naje gida nagaida Mami i was surprise danaga su Sumy duk da ciki,murmushi tayi tace"ka manta nafada maka?"yace"nazata wasa ne"tace"ai gashi ka gani da idonka.yayi murmushi yace "Gaskiya kiyi ma aman sister.."tayi murmushi kawai batareda tace komai ba.kuyi hakuri tafiyar tamu tazo karshe.just 2or3pages to go..indeed every beginning has an end.
