*🧕🏾Labarin Jidderh🧕🏾*
*66*
"Ya kikayi shiru?"yace yana me gyara kwanciyar sa,itama murmushin tayi sannan tace"me kake so in ce?".."nace yaushe zaama Aman sister ko brother?"tayi dariya tace"ba yanzu ba"dan waro ido yayi yace"sai yaushe?"tace"nima ban sani ba,but not soon I guess"ya d'age gira daya sama yace"really?"jijjiga mishi kai tayi kawai batareda tace komai ba,bayan kimanin mintuna biyu tasoma juye juye yace"lafiya bakiyi bacci ba dama?"..ajiyar zuciya ta sauke sannan tace"taya uwa zata iya bacci batareda d'anta ba,I'm missing Aman badly"tamkar zata fashe da kuka haka ta karashe maganar,shikam wani dadi ne ke ziyartar zuciyarshi yakasa boye dariyarshi gamida farin ciki yace"Nima I'm him"tace"ba kamar ni ba,I feel like crying"waro ido yayi yace"nikuma I feel like getting out of the room idan kika fara kukan"..turo baki tayi tace"sabida baka damu dani ba ko?"yayi murmushi yace"that sounds right"can gefen gadon ta je ta duqunqune alamar tayi fushi,bai biye mata ba yajawota zuwa jikinshi,tun tana mutsu mutsu harta bari suka kwanta cikin aminci so da kaunar juna.Washegari misalin karfe goma da rabi ta farka daga bacci,tashi tayi tanufi kitchen domin dora breakfast,chips da burger ta hada tanayi tana kallon time domin 12 take da lectures. Cikin azama ta koma daki tashiga wanka,tana fitowa taga elmoudan zaune yana kallon hanyar kofar toilet din,batareda ta bata lokaci ba tace dashi "good morning antashi lafiya?"tana maganar ne tana goge jikinta mai digar da ruwa,murmushi yayi yace"Alhamdulillah you?"dariya tayi tace"same"wanda hakan yayi daidai da kiran da Inteesar ke ma Jidderh,da sauri jideerh tayi picking sabida tsabagen murna dayake video call ne tama manta towel ne kawai daure ajikinta,Kallo d'aya Inteesar tayi ma jidderh ta kawar da kai suka chigaba da fira,sosai ta nuna mata Aman wanda ke bacci peacefully with zero worries."Ina Daddy Aman?"sai alokacin jiddeeh ta tuna da towel din dake jikinta wata kunyah ce ta rufeta ,murya can kasa tace"baya nan".dan waro ido Inteesar tayi tace"ina yaje?yau Saturday fah"lumshe idanu Jidderh tayi ta bude sannan tace"kika sani ko amarya za'a mana?bana son zurfafa bincike ne"dariya Inteesar tayi tace"kinga alamomi ne shiyasa baki san zurfafa binciken?"tayi dariya tace"kila hakan ne"inteesar tayi dariya tace"Allah ya kawota lafiya ya zaunar damu lafiya"d'an waro ido Jidderh tayi tace"Anty!ni gaskiya bana son kishiya,mu biyun mun isa ai"murmushi Inteesaar tayi tace"selfish girl,I'll advice him yakara biyu ma,kinga ya rufe kofa"nan da nan hankalin Jidderh yayi masifar tashi,fara'arta ta dauke alokaci daya,cikin wata iriyar murya tace"Anty dan Allah kiyi hakuri"sosai maganar Jidderh tabaiwa Inteesar dariya,elmoudan dake gefe ma banda dariya babu abinda yakeyi,musamman ma da Jidderh ta zama tamkar wata abar tausayi alokacin.tasowa yayi yakarbe wayar batareda ta shirya bashi ba,runtse ido kawai Jidderh tayi sannan tabar dakin tana ayyana seta kwana biyu basuyi waya da Inteesar ba.tana cikin saka kaya taji ya shigo bedroom din yana dariya kasa kasa,baisan taganshi ta mirror ba hakan yasanyata kuma had'e rai,saida ya karaso daf da ita sannan yace"tunda baza ama Aman sister ko brother ba kinga se in karo biyu suyita haifa min kids tunda ke kince a'a "smirking tayi tace"whatever I don't care"waro ido yayi yace"tamkar dagaske zan baki mamaki"bata kuma cewa kala ba tachigaba da shiryawarta shikuma yafita yanata faman dariya.adining taganshi yana breakfast,kallo daya tamishi ta kawar da kanta tace"natafi school"tamkar amafarki taji yace"bazakije ba"narai narai tayi da ido tace "but why?I'm having a test today"..in an i don't care tune yace"nide nagama magana the choice is yours"ta ajiye jakar akan kujera sannan takarasa dining tazauna tasoma cin abincin duk atunaninta yin hakan ka iya sa ya sauko tunda ya haneta da zuwa school batareda breakfast ba.kadan taci ta mike tace dashi"gashi nayi breakfast din"yace"wannan kuma kanki kikai mawa"zaro ido tayi tace"ya omri I'm running late,dan Allah intafi"mikewa yayi tareda kamalshe hannayenshi akan kirjinsa yace"going without completing your compulsory tasks ko?"tayi murmushi tace"me kuma yayi saura?Nabaka breakfast fa"ya sosa sajensa yace"babu goodbye kiss and hugg""Namanta ma ashe fushi nakeyi dakai,kaida kace zaka k'ara aure"ya gyad'a kai yace "kara aure yazama dole my dear gara ma ki kwantar da hankalinki "runtse idanu kawai tayi takoma kan kujera ta zauna tana jin wani azababban kishin sa na kuma kamata,murmushi yayi ganin tayi fushi yasashi karasawa inda take,babu zato babu tsammani taji yasoma mata cakulkuli tako ina,dariya tashigayi harda ta Allah ya isa,bai barta ba saida yabari gabadaya ta birkice hawaye na zuba dankwali yayi kudu jakarta tayi arewa,ita tana gabas,bata gama rufe baki ba yayi owning lips dinta kissing her with all he got,hade fuska tayi tace"wallahi test gareni kuma time na tafiya"yace"nafada miki bazakije bafa,kidena damu na"tayi narai narai da fuska tace "haba my omri,karkayi min haka"yace"nariga da nayi ma ai"serious face dinta tayi wearing tace"Allah kuwa dagaske nake maka"yace"ni karya nake ai"shiru tayi tareda kokarin mikewa dan ya gama bata mata rai,yanzu test din data kwallafawa rai ya hanata zuwa,wasu hawayene sukayi nasarar zubowa daga idanuwanta wanda ta gaza tsaida su,ganin haka yasa elmoudan mikewa ya dagata sama ya na juyi da ita,duk da hakan namata dadi amma ta tsuke fuska tareda rufe ido,saida yagama hajijiya da ita sannan ya kwantar da ita kan kujera,tana kokarin tashi taji yace"kin manta yau bakuda school?"nan da nan ta tuna cewar ashe anyi postponing test din tasu zuwa Monday.turo baki tayi tana murmushi alokaci guda tace"shine saida ka wahalar dani kafin ka fada min?"yayi dariya yace"I like teasing you ne"dariya tayi tace"harda zancen kara aure ko?" Yayi murmushi yace"o'o banda wannan dagaske nakeyi,kiss me hayatee"kafada tabuga tace"kaje wurin su suyi maka"salati yayi yace"sabida bakya kishi na ko?"tace"naga alamar mutuwa zanyi kafin time dina" "are you crazy?"tace"crazy that has no limit inde akanka ne..."se kuma tayi shiru tana bubbuga kafafunta,with adoration yake kallonta yace"just kidding".."o'o ni babu ruwana dakai"yace"pls I'm sorry"kifa kanta tayi ma tana murmushi yayinda wani sanyin dadi ke ratsata,dagota yayi cak ya dora akan laps dinshi sannan yayi owning lips dinta kissing her passionately wanda sanadiyyar hakan yasanyasu zubewa kasa,hada ido sukayi tareda fashewa da dariya.
*2 months later*
Yau yakama Friday ranar da Inteesar zata dawo daga kaduna,harda Hajiya dasu ashnoor wanda yau ko gobe haihuwarsu,suna tafiya ne hajiya takira elmoudan nan yake fada mata cewar yakai Jidderh asibiti batada lafiya,da farin ciki hajiya tace"Allah ya sawwake"amin yace sannan suka katse kiran deep down in her heart tana jin wani dadi mara fasaltuwa yana ratsata,jikoki sun kusa cika mata gida.tabangaren su Jidderh kuwa maganin malaria aka bata suka koma gida,babu yadda elmoudan beyiba akan kada tayi girki amma sanda tayi dayake rufe kofar tayi ta ciki tagama aikinta tsabb sannan tafito,afalo taganshi ya had'e rai tamkar hadarin gabas;bata kula shi tashiga wanka tana fitowa taji horn din mota wanda babu tantama su hajiya ne,cikeda sauri tagama shiryawa tafito tarbarsu,suka mata yaya jiki tace Alhamdulillah,Inteesar ce tace"meke damunki"..tayi murmushi tace"malaria ce".."Allah ya sawwake"duk suka furta atare.ahannun elmoudan taje zata karbi Aman but ganin irin yadda yawani sha kunu yasata juyawa tagabatar musu da abinci,yace"hajiya yaya Elameen da muhd zasu bar su suyi tafiya In this condition?"tayi murmushi tace"insha Allah babu abinda ze faru,gobe zamu ai Insha Allah "gyada kai kawai yayi batareda yace komai ba,Aman ne yasoma tsala kuka,yasoma jijjigashi yaki shiru haka yasanya Inteesar karbarshi tasoma shayar dashi yayi shiru abinshi,wani kyau yaga na musamman yaga Inteesar din ta k'ara.washegari su hajiya suka juya kd bayan sha tara ta arziki datayi wa su Jidderh har ma da Mami.ganin taji karfin jikinta yasanyata zuwa tasameshi afalonshi time din yanata faman wasa da Aman,ciki ciki ya amsa sallamar tata sannan ta zauna daf dashi tace"sannu da hutawa"..yace"yawwa"saida ta dauki kimanin mintuna biyar sannan tace"Daddyn Aman pls inason zuwa gida"..yace"na hanaki zuwa gida ne?"tace"a'a "yace"toh sekin dawo"kallonshi tayi kawai ta bar falon tanajin wani iri,tana fita Inteesar tashigo suka chigaba da fira cikin wasa da dariya,abinda ya matukar baiwa Jidderh mamaki kenan,wato ita yake hade ma rai,"natafi sai anjima"kawai tace tareda sakai tafita batareda tajira amsar su ba,Inteesar ta kalli elmoudan tace"kamar akwai abinda ke damunta".."ehh haka rayuwar take dama"yace yana shilla Aman sama,kallonshi tayi tana son fahimtar wani lamari,sharewa tayi daga baya suka chigaba da hirarsu cikin aminci so da kaunar juna. Jidderh kam tana shiga mota tasoma zubda hawaye batareda driver yayi noticing ba,saurin dakatar da kanta tayi ganin fah gidansu zataje,cikin mintuna kalilan suka karasa gidan,acan ta tarar dasu Sumy wanda kawo yanzu cikinsu yayi girma.Suna cikin fira Mami tafito da wata leda wacce Jidderh bazata taba iya manta wanda yabata ita ba."Wata acikin ku ta manta da wannan kayan,kuma daga gani masu tsada ne"cewar Mami tana me bude ledar again,murmushi Jidderh tayi tace"Mami tawa ce,inata nema ban ganta ba"murmushi Mami tayi ta mika mata ledar batareda tayi noticing komai ba,har bayan isha Jidderh takai agidansu kafin ta koma gida,elmoudan yacika yayi fam tamkar kwab'in fanke,jira kawai yakeyi yaga shigowarta,ajiyar zuciya yayi dayaji horn din mota,batafi five minutes ba tashigo falon bakinta dauke da sallama,tace"Anty inteesar Mami na gaisheki tace akawo miki wannan"ta mika mata sakon da Mamin tabayar,Inteesar tace"Masha Allah bari in kirata"tana gama fadin hakan tabar falon,itama Jidderh ta shige daki tana kallon Aman dayake hannun Elmoudan.yakasa gane wani irin taurin kaine da Jidderh data kasa bashi hakuri su sasanta kansu,ganin zaya iya mutuwa idan be daidaita da ita ba yasashi samunta adakinta tana hawaye,batayi kokarin sharewa ba domin barinsu tayi su zuba son ransu,dasauri ya karasa inda take ya rungume abarshi yana goge mata hawayen,hannu tasa ta rungumeshi itama domin tana da niyyar zuwa bashi hakuri se gashi ya rigata.murya can kasa kasa yace"I'm sorry hayatee"tace"I'm sorry ya omri".cupping face dinta yayi yana circling lips dinta yace"I freaking love you hayatee"tace"I love you more"yayi murmushi yace"oya kiss me"bai gama rufe baki ba tayi owning lips dinshi kissing him with all she got.
*2 months after*
Yau yakama Saturday,elmoudan,Inteesar da Jidderh na zaune sunayin lunch,anata fira cikin wasa da dariya,time din Aman na 4months aduniya,kamarshi da babanshi takuma fitowa tamkar elmoudan yayi kaki ya ajiye.wayar Jidderh ce tafara ringing,ganin Mami yasata saurin picking inda Mami ke shaida mata cewar Sumy tahaihu jiya da dare yayinda Aneesah da Jasmine suka haihu da safe..inda Sumy tasamu baby girl Aneesah da Jasmine kuma baby boys.dadi tamkar ya kashe Jidderh haka taji,ta ajiye wayar bayan ta shaidawa Mami zuwanta yanzu yanzu.ta kalli inteesar tace"Anty su Sumy sun haihu,tasamu baby girl Aneesah da Jasmine kuma baby boys "washe haqora tayi tace"Masha Allah I can't wait to them..wata daya kenan tsakaninsu dasu baby"tace"ehh I can't wait to hold them in my arms"murmushi elmoudan yayi yace"ku shirya muje.Ranar suna yara sukaci sunayen bangaren dagin ubansu,akayi suna lafiya aka tashi lafiya sai san barka.
*2 months later*
Zuwa yanzu Jidderh ta kammala first year dinta zasu shiga part two,Aman yakuma girma sosai yaro mai masifar wayo.afalo ya tarar da Jidderh da Aman suna wasa yace"Ammin Aman zan kai mummyn Aman asibiti batajin dadi "tayi murmushi tace"Allah ya sawwake bari in dauko hijab,bayanta yabi dakallo yana jin wata kaunarta na kuma sukarsa. Acan asibiti aka tabbatar musu da Inteesar na dauke da ciki harna 3months,murna wurin Elmoudan Inteesar da Jidderh ba'a magana...dayake wannan cikin na inteesar mai masifar laulayi ne hakan yasanya Jidderh chigaba da kula da girkin gidan harma da Aman.Allah yasa cikin hutu suke Shiyasa aikin baya damunta.sosai suka saba Aman ta yadda mai karatu baya zato...dan sanda za'a yaye shima awurinta ya zauna.kawo yanzu cikin inteesar yashiga watan haihuwa yayinda babys dinsu Jasmine sunyi wayo sosai har kwatanta mikewa sukeyi,shekarar Aman d'aya cif Inteesar tahaifi santaleliyar diyarta mai kama da ita kwabo da kwabo yaso saka sunan hajiya Amma sabida yayima Inteesar halacci ya sanya sunan Hajiya Halima zasu rinqa kiranta da Suhaila.wannan karon bataje kaduna wanka ba sede hajiya ta aiko dawata dattijuwar dazata chigaba da kula da ita har suyi arba'in.Time din Jidderh tana exams din second semester part2 elmoudan yashigo bedroom dinta ya tarar tana karatu.littafin ya daga yaga phamaceutics take karantawa yace"sannu da karatu yaushe zaku gama exams din?"ta lumshe ido ta bude sannan tace"gobe Insha Allah wannan ne last paper dinmu"gyada kai yayi yace"wish you all the best hayateee"tace"thank you ya omri"yana me pecking goshinta.wayar tace tasoma k'ara hakan yasanyata mikewa tanufi inda wayar take,kallon jikinta yakeyi yana nazarin wani al amari.agajiye tadawo daga school tabaje afalonta tana hutawa,Aman yazo dagudu ya fada kanta yayinda elmoudan ya shigo hannunshi dauke da Suhaila,murmushi yayi yace"sannu da dawowa,wannan school din bata kyauta min gaskiya irin wannan gajiya haka?"tayi murmushi tace"shi karatu dama ya gaji haka.ya zauna yana fadin"kinji abin mamaki wai ashnoor takara haihuwa"baki ta bude sannan tace "are you kidding me?"tafadi haka tana me mikewa zaune,yayi dariya yace"ki zauna jira dai"dariya kawai tayi sannan ta dauki wayarta da niyyar kiran Ashnoor taga missed call din Aneesah,koda ta kira Aneesah cemata tayi Sumy tasamu miscarriage,sosai hankalinta ya tashi ta ajiye wayar ta dubi elmoudan tace"ya omri Sumy tayi miscarriage "sunyi jimami sannan sukaje sunata har asibitin.
*5months later*
Zuwa yanzu Jidderh tagama first semester dinta na part 3 sun shiga hutu.Suhaila na tafiya yayinda Aman yasoma koyon magana,Elmoudan nazaune da yaranshi afalo inteesar tace"nifa akwai abinda ke damu na"ya nisa yace"mene ne?"tace"akan Jidderh mana"yace"meya faru da jidderhn?"cikeda damuwa tasoma fadin"kawo yanzu banga alamar tana dauke da ciki ba,kaga fah sister's dinta duk haihuwa ta biyu zasuyi watan gobe amma ita har yanzu ko batan wata bata taba yiba,aurenku yanzu fah almost 3yrs,aganina koza kuje asibiti ne"murmushi yayi yace"komai lokaci ne my forever"tace"haka ne kam sannan she might think ko cin fuska ma za'a mata tunda kai de ga yaranka har biyu"yace"abinda nakeso ki fahimta kenan"tace"insha Allah itama babu komai lokacinta ne baiyi ba"karashe maganar inteesar yayi daidai da shigowar Jidderh da Aman falon bakinta dauke da sallama,tace"Anty yau mun taki sa'a,last pieces muka samu"dariya inteesar tayi tace"lallai kam,akwai wasu kaya da'aka kawo zamu duba anjima"tace"wasu iri ne?"tana me zama akasan carpet,Inteesar tace"gowns ne"Jidderh tace"yeeee aikuwa zamu zaba"banda kallon Jidderh ba abinda elmoudan keyi yana saka da warwara cikin ranshi.Bayan wata d'aya sister's din Jidderh suka haihu alokaci daya inda kowacce tasamu baby boy,murna wurin abbansu ba'a magana,gashi da Allah be azurtashi da yaya maza ba yabashi jikoki,sai a wannan lokacin Mami tasoma damuwa da rashin haihuwar Jidderh ganin ko ciki babu a sunan su Jasmine sede bata ce mata komai ba.sun koma makaranta tachigaba da karatunta cikin kwanciyar hankali domin rashin haihuwar tata bai taba damunta ba hasalima tunanin bai taba zuwan mata ba.tana karatun test sunata fira afalo taji mararta tayi mugun murdewa,runtse ido tayi tana cize lebe sabida azabar datakeji,babu wanda ya lura da halin datake ciki dubaga kallon dasukeyi.cikin wani irin yanayi tace"Anty inteesar,meke zuba ajikina?"arikice inteesar da elmoudan suka karaso wurin cikeda mamaki ganin jini nabin kafafunta.emergency aka kaita inda suka tabbatar da miscarriage tasamu,babu wanda beyi mamaki ba acikinsu,ita kam se alokacin taji zafin fitar ciki,bata damu da Mami,inteesar,sister's dinta,elmoudan,hajiya dasu Ashnoor ba ta fashe dawani matsanancin kuka gamida riqe cikinta,agigice suka kira doctor don duk azatonsu wani mugun ciwo ne ke taso mata,dr ya tabbatar da lafiya kalau take sannan hakalinsu ya kwanta,tayi kuka har me isarta domin hajiya tahana abata hakuri,gara ta amayar da bakin cikin yanzu ba se daga baya ba ta riqa tashin hankalin ta.Elmoudan kanshi ya yi wani iri gabadaya bayajin dadin yadda alamarin yafaru,hajiya ta dafa shi tace"Allah zai mayarda mafi alheri"yayi murmushi yace"ehh".gidansu aka mayar da ita Mami tachigaba da kula da ita yadda yakamata,tun kafin takoma gidanta tasoma zuwa school dubaga exams dasuka fara ta part3 second semester,bata koma ba saida ta kammala exams tsabb sede kullum se elmoudan yazo dasu Aman da Inteesar gaisheta.yau takama Friday ranar dazata koma gidanta tagama shirya komai nata elmoudan yazo ya dauketa. Amota yake ce da ita"amma fah Mami ta iya kiwo. Irin wannan kyau haka?"murmushi tayi tace"stop exaggerating"ya riqo hannunta yace"happy 4th anniversary in advance..i love you"..tayi murmushi tace"same ya omri I love you too amma fah da saura"yace"ehh ...zamu dauko Aman daga school "tace"Allah sarki babynah I missed him"yakalleta yace"bayan kullum se kun hadu dashi shine kuma harda wani missing?"tayi dariya tace"ehh mana,sannan ma zamuyi takeaway Inteesar bata jin dadi "ta dan waro ido tace"meya sameta?"yayi jim sannan yace"she's pregnant "cikeda jin dadi tace"Masha Allah. Allah ya inganta ya kawo mana baby lafiya"yace"amin ya rabbi"duk wani uncomfortable yake jin kanshi shikam dayasan kasuwar da ake siyan ciki daya siyoma Jidderh koda tsadar ze sanya yarasa komai nashi.Aman suka fara daukowa a school sannan sukayi takeaway suka karasa gida.akwance sukaga inteesar yayinda Suhaila ke gefenta ganinsu yasanyata mikewa zaune tana murmushi tace"welcome back sweetheart"sannan suka rungume juna itada Jidderh.
*5months later*
A time dinnan Jidderh ta kammala first semester exams dinta ta level four cikin inteesar nada wata shida lokacin,har yanzu Jidderh bata samu ciki ba kawo yanzu tafara shiga damuwa amna bata taba nunawa kowa ba,akullum elmoudan cikin kwantar mata da hankali yakeyi ta wata sigar domin ba fitowa fili yakeyi yana fada mata ba.lokacin da cikin inteesar yashiga watan haihuwa Jidderh ta kammala degree dinta time din shekararsu 4 da aure,su Sumy ma basu kara haihuwa ba yaran biyu biyu alokacin.walima sosai elmoudan yahada mata nagani nafada,washegari Inteesar ta haifi santalelen baby boy dinta,me kama da ita kwabo da kwabo inda yaron yaci sunan kawu mallam wato Abubakar sadiq zasu rinqa kiranshi da Abeed.elmoudan yaso mace ce yasanya sunan Hajiya amma se aka samu namiji.kawo yanzu elmoudan yagama gininshi dake Ahmed Bello way,gida ne nagani nafada wanda fasaltashi ko kamanta shi bata lokaci ne. Bayan sun koma sabon gidan ne elmoudan yasamu Jidderh nawaya inda take shaidama Mami cewar a asibitin murtala zatayi internship dinta.bayan sun kammala maganar ne ta mike ta karasa kusa dashi ta zauna tana me dora kanta bisa shoulder dinshi,murya can kasa tace"ya omri yanzu haka rayuwata zata chigaba da tafiya?"waro ido yayi yace"hayatee meya faru?"fashewa tayi da kuka tace"haka zan chigaba da rayuwa as a barren woman(juya)?"saurin dora fingers dinshi yayi akan lips dinta yace"shhh kar na karaji kinyi wannan maganar,zaki haifa mana kids I promise you Insha Allah "tayi murmushi tace"I pray so"yace"you will Insha Allah,I love you so very much hayatee" tace"same ya omri.".anan su Aman suka shigo bedroom din dagudu suna wasa.bayan wata daya
*ALLAHU SAMI'UN DU'A*,after four years without conceiving Jidderh ta tashi dawani matsanancin zazzabi,elmoudan na dakin inteesar time din hakan yasanya ta mikewa tana ganin jiri ta fita babban falo inda taga Aman na wasa dasu Suhaila,zama tayi sannan tace"Aman kiramun daddy"Da gudu yaron ya shiga bedroom din mamanshi inda suke shiryawa yace"daddy Ammi tace I should call you"da mamaki ya kalli inteesar sabida Jidderh bata tab'a aikawa akirashiba sai yau kenan akwai matsala.da sauri ya fita ganinta afalo yasashi saurin karasawa ya jawota jikinshi,saurin firgita yayi jin turirin dake tashi ajikinta,dasauri inteesar tasaka mata hijab suka nufi asibiti,test akama ta inda bayan an kammala suka tabbatar da ciki ne da ita na 2months,murna elmoudan harta hawaye,itama hawayen ne suka soma zubo mata,Mami kam zama tayi tasha kukanta tanata godiya ga Allah haka hajiya sujjada tayi domin lamarin ba karamin daga mata hankali yayiba,ahwaz da matarshi Aisha da yaransu biyu suka zo dubata har asibitin,kwana biyar tayi aka sallameta takoma gida,tamkar kwai haka elmoudan da Inteesar ke kula da ita,abin har mamaki yake bata wani sa'in kuma yasata kunyah,akwana atashi babu wuya awurin Allah ranar wata juma'a Jiddeeh ta haifi santaleliyar baby girl dinta wacce taci sunan hajiya ana kiranta da Amani💕,yarinyar tamkar Jidderh tayi kaki ta ajiye haka ta ke kama da ita sede ta dauko farin elmoudan,anyi suna nagani nafada sannan aka maida Jidderh gida domin wankan haihuwa,Amani nada shekara d'aya Jidderh ta kara haihuwar santalelen baby boy dinta mai kama da elmoudan sosai,inda yaron yaci sunan baban elmoudan din suna kiranshi da Suhail,year after takuma haihuwar diyarta mace dataci sunan Mami aka kiranta da Abeeda,bayan 2years inteesar da Jidderh suka haihu atare inda Jidderh tahaifi namiji suka sami shi sunan elmoudan ana kiranshi Affan yayinda inteesar tasamu baby girl aka saka sunan anty bebi suna kiranta da Afiya.Rayuwarsu tazama abin sha'awa dubaga yadda suka Gina dangantakar su akan gaskiya da amana da yarda da juna uwa uba soyayyah da kauna. Yau takama Saturday gabadaya sun shirya domin zuwa Ado bayero mall dake zoo road,kowanne yaro se tsalle yakeyi dan ba baya ba wurin son yawo.Shopping sosai babansu yamusu har ya kaiga Inteesar da Jidderh sun zuba musu ido domin babu damar suyi magana ya gwale su.Ta baya inteesar taji an dafa ta wazata gani inba ziyada ba,cikeda mamaki baki na rawa tace"Ziyada!"hawayene suka soma zubowa Ziyada daga idanu tace"inteesar rai kanga rai"gefen Ziyada ta kalla taga wasu cute kids zasu kai biyar tace"yaranki ne?"Ziyada tace"biyu ne nawa sauran na anty Fa'iza ne"cikeda rudani tace"wace anty Fa'iza kuma?"dariya Ziyada tayi tace"uwargidan ce,"sai a lokacin ta kula da Jidderh tace"wacece wannan?"inteesar tace"Jidderh matar elmoudan ta biyu "waro ido Ziyada tayi tace"are you kidding me?"dariya inteesar tayi tace"ga tawagar mu can na tahowa"ganin yara takwas yasanya Ziyada gasgata maganar inteesar,tayi jim tace"ki yafe min inteesar"saurin rufe bakinta inteesar tayi tace"duk da bansan lefin dana yimiki ba kokikayi min komai yawuce insha Allah,can we be friends again"dariya Ziyada tayi tace"ofcourse yes "saurin sunkuyar da kai Ziyada tayi ganin elmoudan wata kunyah ta lullubeta,dariya yayi sanda yatuna abinda suka gabata.ALHAMDULILLAH!!!
Anan ni XEEEBELLSS na kawo k'arshen wannan littafi nawa me taken *_LABARIN JIDDERH_* inda nayi kuskure ko na fad'i ba daidai ba Allah yafemin, kamar yadda kuka sani wannan labari k'irk'ira nayi (fiction) saboda haka adena kwatanta min shi da real life nayi littafin ne dan nishad'i sekuma fad’akarwar dake ciki.
I will first of all like to thank *you* for reading my novel and supporting me through out, thank you so much as we keep loving each other.GARGADI
Wannan littafi da labarin daya kunsa duk mallakar marubuciyar littafin ce.saboda haka sai a guji juya,ko sarrafa Wannan littafi ko labarin dake cikinsa batareda izini ba.TUNATARWA
Labarin dake cikin wannan littafi kagaggen labari ne don fadakarwa da nishadantar da mai karatu.Saboda haka sai a guji yin zargi ko zaton cewa anyi wannan labari ne domin musgunawa wani ko wasu. Haka sunaye da garuruwan dake ciki an saka ne kawai don kayata labarin.
GODIYA
Ga ubangijin talikai mai kowa mai komai wanda ya cancanci duk kan yabo da jinjinawa,domin baiwarsa,Ni'imominsa,da jin k'ansa a garemu mabuwayin sarki,wanda bashi da abokin tarayya,masanin zahiri da bad'ini. Tsira da amincinsa su k'ara tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W)da ahalinsa da sahabbansa da duk mabiyansa har zuwa tashin alkiyama.Amin.YAN UWA RABIN JIKI
Khadija M Yusuf(Ya ummi)
Yusuf M Yusuf (Ya abba)
Fauziya M Yusuf (Ya fauzi)
Maryam M Yusuf (Ya mariam)
Musa M Yusuf
Mohammed M Yusuf
Abubakar M Yusuf
Munirah M Yusuf
Allah ya rayamu cikin zumunci da aminci ya tabbatar mana da alkhairi,duk burikanmu na alkhairi cikin rayuwarmu,ubangiji ya cika mana su amin.TUKWICI NE GA
Anty Fatima Bello Salim(Batul mamman) amintacciya,hakika baki baida kalmar godiya agareki saidai adduar samun dacewa duniya da lahira,Allah ubangiji yajikan Maman Ruqayyah yasa aljanna ce makoma sannan yaraya rukayya da Abeed amin amin ,ba abinda zance sai Allah yabar zumunci.Anty Nafeesah Nuhu(sadnaf),Allah yabar kauna da zumunci yaraya affan da ikram.amin.nasan har yanxu fushi kikeyi to kaina bisa wuya wannan sakon ban hakuri ne.
SADAUKARWA
Wannan labarin sadaukarwa ne ga aminiyata,bestynah mai kaunar farin cikina Zaynab Mohd Gureey,words are inexplicable when it comes to you,babu kalmomin dazan iya amfani dasu wurin bayyana yadda kike awurina,know that I love you so very much,(future Mrs Saleem😘❤)KUNA RAINA
Anty ayush iliasu
Fateema ashemie
Sis inna
Mzz daddy
Sis shafa aminu
Sis najah mustapha
Mmn mummy
Maryam ipteen
Hermebreah
Shamsiyya salis
Ummu Othman
Meenerh
Maman nana
Jiddooo sulty
Zainab abdurrahman
Lady of the rose
Fateemah Zahra umar
Zinnira
Starnucee
Maman tima
Layla maman khadeejah
Zakiyyah haruna
Kubrah mmn fatee
Mrs hamisu taura
Ilham
Smile
Zainab babagana....washhhhhh my hands are aching really,wanda bega sunansa ba yayi hakuri zamu hadu agaba,I love you all my supporters Allah hada fuskokin mu a aljannah.To the wonderful groups
ZEEEBELLS NOVELS GROUP
MZZ DADDY NOVELS GROUP
YAR HUTU FANS CLUB
ZAUREN AYUSH AND HAWWA SALEH...thank you all for reading.To my wattpad readers,thank you all for reading,Sakillahu bil jannah sai mun sake haduwa cikin littafina nagaba mai suna WAYA SAN GAIBU?!.or NOORUL IMRAN(the revert muslim)
with love
Xeeebellss❤
