🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M*✍🏻

1.5K 72 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀




         *NA*

*HAFSAT_M*✍🏻




*Page*
      
       *32*

Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare

*Gareki Babbar AUNTY NA SISI gaisuwar wannan shafin da ita shafin da kanta gabaki ďayan sa takice bata kowa ba AUNTY SISI ke ďin daban kike cikin duniyar whatsapp wannan maganar tawa haqqun take kowa da kowa ya sanda wannan zancan babu kamar ki wajan mutunci a yanar gizo AUNTY SISI fatan Alkhairi gareki iya wiya ana mugun tare ba makawa*😚






Fitan ta daga gidan cikin hanzari tana fatan Allah yasa babu wanda yafarka bare yaga shigowan ta, haka taka da kafarta har zuwa bakin titi anan tasamu mai Adaidaita sahu dakyar ya ďauketa ya mayar da ita gida, saukan ta keda wiya bayan ta biyasa kuďin sa ta juya da niyar shiga cikin gidan ta hango motar Abdulmalik an buďe masa get yana fita,binsa tayi da kallo yayi tamkar bai ganta ba  yaqawa motar gudu har ya baçe mata da gani,kafin ta kaďa kai a zuciyar ta tace dani kake wasa yaron nan bakasanni ba Amman nasan mai zanyi,,shiga cikin gidan tayi tana bambami ita ďaya bata ankara ba tayi kicibus da Abba tsaye bakin shiga ķofar parlon bangaran ta, ya harďe hannayensa bisa ķirjin sa tare da jifanta da kallon tuhuma fuskan sa a haďe yace,,"

Daga ina kike da sasafen nan? bari jikinta ya soma bataso yagane fita tayi ba Amman tasan koda shi baiga ficewar ta daga gidan ba ta tabbata zuwan da Abdulmalik yayi bana banza bane dole yasanar dashi gidan sa taje, tambayar ki nake kinyi min shiru, taji muryan shi ya sinkayo ta ta ďago da kai tana kallon gefe guda ta soma kame kame tace babu inda naje kawai dai na ďan shiga gidan makociyar mun nan ne anyi mata haifuwa shine naje inyi mata barka, ni kike nema kiyiwa rainin hankali Bara'atu duk irin gargaďin da nayi miki na yanaki kar naga kin fita ashe nuna zakiyi ban isa dake ba, kin ďauka bazan san fitan ki bane ko kin ďauka bansan inda kikaje bane?ya tambaye ta yana qara duban ta yace yanzu bisabidillahi duba lokaci yayi mata nuni da a gogon hannun sa yaci gaba da cewa ko ke agareki ba babban abun kunya bane ki kwashi ķafa da safen Allah kije gidan surukar ki ko tashi a bacci ma basuyi ba kinje kina zubar da girman ki da qimarki kina mataayin uwa ahaka kuma kikeso su kalli girmanki,,"

To inaso kisan wani abu bara'atu hanzari ba gudu ba wlh kinji nayi miki rantsuwa duk lokacin da naji lbr ko nagani da idona wani abu yasaki ďiban ķafafun ki da niyar zuwa gidan surukanki  to ki tabbatar da cewa zakiga bàcin raina wanda baki taba gani ba tunda ke kin nuna ba zaman lafiyan ne sam bakyason shi,,"

Tsagaitawa yayi da maganar ransa a bàce yana mata wani irin kallo yace bani waje in wuce in yaso gobe ma kije gidan tunda ke bakisan girman kanki ba, matsawa tayi tabashi hanya ya wuce tana jinsa ya shige bangaran sa, haka tana kunkuni ta qarasa shiga parloun ta samu kujera ta zauna tare da cire hijabin jikin ta tayi jifa dashi sosai takejin bakin ciki aranta babu shakka idan tayi wasa tabiye gargaďin da yakeyi mata  nan gaba kaďan zata koma abun magana cikin mutane,,"

Tagumi tayi tana nazarin ta inda zatayi taga ta gyara gidan ďanta batare da wani yasa mata ido ba koshi yagane taba dan a iya zuwa yanzu bazata ce zata qara wani zaman haquri ba yazame mata tilas ta miqe tsaye tayi abunda batayi shi ba ada, tashi tayi daga parlon ta wuce ďakin cikkn zuciyar ta ta kulla wancan ta kulka wannan,,"

*******  ********

Bayan wasu ďan kwanaki abubuwa da dama sun faru cikin zaman auran da takeyi, wanda a kullum ya kasance idan ranar kwanan ďakinta yazo takan zagewa taga tayi girke girke iri da kala masu rai da lfy ta gyare ko ina lungu da sako na cikin gidan yayi fesfes dashi ta saka turanen wuta ko ina yakama da kamsh saidai wani abunda dake ďaure mata kai akoda yashe idan yazamana tayi girki sai takan samun matsala cikin abincin da ta dafa kullum yana cikin mata korafi kenan,,"

Daga yau yace mata gishiri yayi yawa gobe yace mata yaji har baya iya cin abincin saidai ta girka masa ko indomie cikin qanqanin lokaci  idan itama ta taba taji takan mamaki to  tayaya hakan yake kasancewa da ita a halin ba'a gidan ta soma girki ba, hakan yazamana ba qaramin tashin hankali yake sakata ba dan har tafara ganin canji daga garesa hakan na damunta matuka sosai,,"

Yauma Kamar kullum itace da girkin hakan yasata tun wuri ta shige ďakinsa ta gyare masa ko ina tare da wanke toilet ďin da idan ta lura ba'a wanke sa saidai ita ta wanke, fas tagama gyara masa taja ķofar ta fice, kai tsaye kitchen ta nufa ta ďaura tuwon shinkafa da miyar yakuwa sosai yabaďa cikin gidan da kamshi, tanayi tana gyara kitchen ďin har tasamu ta kammala cikin qanqanin lokacin ta juye komai cikin kula ta haďa plate dasu cokala,,"

Barin su tayi a kitchen ďin ta fita tare da wucewa ďakinta tayi wanka tasamu kayanta na atumfa tasaka riga da zani sosai ya karbì jikinta, tayi kwalliya sama sama ba sosai ba gameda feshe ko ina na jikinta da turare kafin ta fita taje tasa turaren wuta bayan tagama ne ta koma daķin ta ta kwanta rigingine tana kallon saman ďakin cikin zuciyar ta tunani iri iri ta faďa tayi nisa sosai kallo ďaya zakayi mata kasan cewa hankalin ta baya tattare da ita,,"

Wuraren misalin karfe biyar na yamma ta dawo daga gidan shiwari tana gama parkin ďin motar ta tafita tareda rufe motar ta zagaya ta bayan gidan dama da shirin ta tazo tayi alqawarin yauma sai ta lalata mata girkin ta saidai idan batayi ba tunda taga yanzu sun fara samun matsala tsakanin su, hakan ya sanya cikin sanďa tamkar sabuwar barauniya tana leqe ganin ķofar kitchen ďin rufe yake hakan ya tabbatar ma da cewa bata ciki fatan ta ďaya Allah yasa bata shigar da abincin kan dining ba dan a kitchen ďin ne zatafi jin daďin aiwatar da abunda tayi niya,,"

Cikin sa'a kuwa ta hango su ajiye cikin kitchen ďin ganin su ba qaramin daďi yayi mata ba tana wani irin shu'umin murmushi na mugunta ta buďe kular taga miyar yakuwa ce ďayan kuma tuwon shinkafa tana yamutsa fuska ta ďibi ruwa cikin cop biyu ta juye su cikin wannan miyar tasa cokali ta garwaya taga yazama tamkar ruwan kogi kafin ta rufe kular ta gyra inda ya bàci a hankali taja ķofar kitchen kamar yanda yake ta fita, kai tsaye bayan ta shiga parloun babu kowa sai daddaďan kamshin turaren wuta dake tashi cikin ranta take faďin shegiya bakar aljana kafin dai ki kashemu da wannan mugun hayakin naki ni zanyi gaggawar fitar dake daga gidan,,"

Tana toshe da hancinta ta shige cikin ďakin dan batajin zata iya ci gaba da shakar wannan shegen fitinannan hayakin a kullum,,"

A gajiye yadawo gida yau tilis yakejin sa dan gajiya ga wani irin bala'in yunwa dake rarike masa cikin kokon cikin sa ji yake gabaki ďaya idan ba samu yayi yacika cikin sa da abinci ba bazai iyayin komai a wannan lokakin hakan yasa yana shiga parloun ďakinta ya nufa kwance ya tarar da ita idanunta lumshe tamkar wacce take bacci, yaqarasa cikin ďakin ya tsaya akanta gameda qiran sunan ta kusan sau uku kafin tajisa a hankali ta buďe idon ta suka sauka cikin nashi da sauri ta miqe zaune tana kallon sa tace sannu da zuwa har kadawo?, yauwa yafaďa a takaice yace ina abinci yunwa nakeji, muje in zuba maka tafaďa tare da tashi suka fita, kitchen ďin ta wuce ta ďauko kulan abincin da abun ďibawa yana zaune kan dining yana zaman jiranta ta tarar dashi, tana ďan murmushi ta ajiye abincin tana faďin lailla yau ba qaramin yunwa ka kwaso ba yanda ko wanka bakayi ba zakaci abinci dan tasan al adar sace kullun idan yadawo daga aiki idan ba wanka yayi ya canza kayaba bayajin daďin zama yaci abinci hankali kwance,,"

Buďe abincin tayi zata zuba masa yana kallon ta yace bani in zuba da kaina bakya sauri kafin nan kije ki ďauko min charger phone ďina a ďaki, ba musu ta basa abun ďiba abincin tana masa dariya ta wuce dan zuwa aiken da yayi mata,,"

Bayan ya ďauki tuwom malmala ďaya tare da buďe kular miyar zai ďiba cikin jin daďi ya lumshe idanunsa ya buďe su yana qara shakar daddaďan kamshin miyar dake tashi yana shige masa cikin hanci, a iyayin da yasaka ludayin cikin miyar ya ďiba yana zubawa kan plate ďin tamkar sinkekkiyar ruwa tsala yake zubawa,,"

Atake yanayin fuskan sa ya canza wannan abun ba qaramin bashi haushi yayi ba cikin bàcin rai sosai ya shiga kwala mata qira cikin ďaga murya wanda yayi sanadiyar sinkar mata da zuciya sosai jin irin yanda ya qira sunanta ba shiri cikin tana rawan jiki ta fito daga ďakin hannun ta riqe da chargen daya aiketa, tunda ta qaraso inda yake tsayen taga yanayin sa yanda yabi ya canza ta tabbatarwa da kanta ba lfy ba dan a yanda suke zaune shi da ita bai taba mata irin wannan mugun qiran hakaba bare yayi mata irin wannan mummunar kallon da yanzu taga yake binta dashi.....




_Masoyana makaranta littafina dan Allah kudai qara min haquri nakusa *✍🏻📚📚📚

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now