🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M*✍🏻 *Page*

1.3K 60 0
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀



         *NA*

*HAFSAT_M*✍🏻


*Page*
      
       *41*


Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃







Tashi tsaye tayi daga zaunan da take gameda kaiwan idanunta kan agogon dake manne jikin bangon dakin, ya nuna mata har shaďaya ta zarta."cikin ranta take faďin, yanzu inbanda ďan iskan mutum yana neman hanyar raba mini aure ba, sai dare lokacin da duk yawancin mutane sun kwanta bacci, kafin zai qirani halan ya jaza min bala'i." qara sauke numfashi tayi a hankali tanaci gaba da neman tsarin Allah tsakanin ta dashi."

"Ficewa tayi daga ďakin bayan ta kashe wutan gameda rufe ķofar, ta nufi nasa ďakin, cikin ranta tana Allah Allah yasa bacci ya ďauke sa dan gudun kaga ya jero mata tambayoyin da batada amsar su a wannan lokakin."

     "Bayan tashiga cikin ďakin, ta maida ķofar ta rufe, tare da kunna hasken wayar ta, ta qarasa zuwa gadon inda yake, yana nan kwance yanda ta barsa, bai canza ba, hakan tayi tsammanin yayi bacci." A hankali ta haura kan gadon ta kwanta gameda juya masa baya kamar yanda shima ya juya mata."idanunta a rufe, bayan ta karato addu'oin bacci, ta shiga zancen zucin da yakeson zama mata wajibi akoda yaushe idan tasamu nutsuwa."

     "Inafatan dai kin sanar dashi abunda nafaďa miki,?" tamkar saukan aradu taji tambayar tasa ya doki dodon kunnenta, wanda hakan shi ya dakadar mata da zancen zucin da take, ta  buďe idanunta a hankali ta jiyo da kanta garesa tana kallon bayan sa,kafin ta soma cewa."

      "Nasanar dashi wlh batun yauba, tun sanda ya soma bibiyata na gargaďe sa da yarabu dani, ya daina qirana a waya, Amman hakan ya faskara kullum cikin qiran waya na yake bansan meye dalili ba." tamkar wacce takeson yin kuka take maganar, cikin qasa da murya taci gaba da cewa, dan Allah karka bari sheďan yayi tasiri a zuciyar ka, har kashiga zargina akan abunda ba hakaba, wlh babu komai tsakanina dashi, bansan shiba, pls karka zargeni..ya isa haka taji yafaďa cikin muryan sa batare da yabari taqarasa maganar da take ba, yaqa cewa, tambayar ki nayi, kuma kin bani amsa shikenan bana bukatar wani dogon bayani a yanzu, kiyi baccin ki kawai saida safe."

      "Hakan da taji yafaďa ne ya sanya ta runtse idanunta, Kafin ta buďe, a hankali cikin sanyin jiki ta masa zuwa jikinsa tayi dafda dashi ta zagaye shi da  hannunta tare da sakala kanta ta tsakanin wuyar." yana jin ta duk abunda take masa baice da ita qala ba, illah ma rufe idanunsa da yayi dan yin bacci."

      "Haka tana manne dashi a jikinsa ta baya, har bacci yayi awun gaba da ita, wanda shima a wannan lokakin bacci ya ďauke sa."

      "Koda asuba tayi bayan ya fita masallaci akayi sallah dashi, kafin ya dawo gida wanda itama a wannan lokakin har ta idar da nata sallan ta koma ta kwanta bayan tayi zikiri da addu'oin ta." shima komawa yayi ya kwanta, wani sabon baccin ya kuma daukar sa."

Wajan misalin karfe takwas saura ta buďe idanunta, gameda kai dubanta garesa, ganin baccin sa yake hankali kwance, yasa a hankali batare da yaji motsinta ba ta fice a ďakin zuwa nata, kai tsaye wanka tayi tare dayin brush, kafin ta fito, ta shirya cikin doguwar riga ta atumfa, wanda bazai takura mata ba, Amman ďinkin yayi ma jikinta kyau." bayan ta fesa turare ta shafa me, ta fito kai tsaye ta wuce kitchen, dan ďaura musu karin safe." kifi tarwaďa ta ďaura dafuwa haka rigijif, da soyayyan dankali, gefe kuda kuma blacktea ta ďaura da kuma shayi me madara shima daban wanda yasha kayan kamshi na shayi."

     "Wajan misalin karfe tara ta kammala dafawa, ta juye ko wannen su cikin kula, kafin takawo ta jerasu kan dining table, tana gamawa ganin har zuwa wannan lokacin bai fito ba ya sanya ta, komawa ďakinta taqara watsa ruwa a jikinta, tasake wani sabon shirin tare da qara fesa turare masu daďi ajikinta, tayi kwalliya sama sama ba sosai ba, kafin ta fice daga ďakin ta nufi nasa."

      "A hankalin ta tura ķofar ďakin ta shiga, taga baya nan." can taji motsin ruwa cikin toilet  hakan ya tabbatar mata da cewa wanka yake." kafin ya fito tashiga gyaran dakin dukda ba wani datti bane dashi."

"Fai fito ba har tagama gyaran ďakin ta zauna a bakin gadon tana jiran fitowar sa," bayan wasu mintuna kaďan, ya fito daga toilet ďin ďaure da farin towel babba, tana kallon sa ta miqe tsaye daga zaunen da take, gameda qarasowa garesa, fuskan ta cikin murmushi ta gaishesa ya amsa mata batare da yaqara fadin komai ba, yaci gaba da goge ruwan dake jikinsa."

     "Sam bataji daďin ganin irin yanda ya amsa mata gaisuwar, tamkar bayaso,  hakan ya sanya jikinta yin sanyi, cikin ranta take faďin, yanzu shikenan abunda take guduwa ya afku mata, duk yanda zatayi ta sanar masa da gaskiyan ta ba yarda da ita."

      "Cikin zuciyar ta sam babu daďi." batare da ta qara faďin masa komai ba, ta tsaya jiransa har ya kammala shiryawan sa cikin blue shadda kaftan, wanda yasha zubin farin zare." sosai yayi kyau cikin kayan."

"Fitowa sukayi daga cikin ďakin a tare zuwa dining table, yaja kujera ya zauna, itama taja wanda yake kusa dashi ta zauna bayan ta zuba masa a kan plate iya yanda zai iya ci, tare da zuba masa ido tana kallon sa yanda yake cikin abincin, cikin zuciyar ta kuwa tana haďe haďen yanda zata fahimtar dashi, dan yabar wannan fishin da yake da ta."

      "A hankali ta saukar da numfashi tare da ďaukan cup guda biyu ta tsiyaya blacktea aciki ta ajiye masa ďaya kusa dashi, itama ta soman shan ďayan." jifa jifa take satan kallon sa ta gefen idanunta, har ya kammala da cin abincin sa ya miqe baiyi magana ba, ya ďauki wayar sa dake kusa dashi ya zura cikin aljihu, kafin ya ďauki hanyar fita, wanda ganin da gaske fitan zaiyi har zuwa lokacin bace mata qala ba, ya sanya ta, tashi da sauri daga zaunen da take, bayan ta ajiye cup ďin shayin dake hannunta ta, har ya isa bakin ķofar parloun zai fita, cikin ďaga kafa ta qaraso garesa, batare da yasani ba, tasa hannayen ta duk biyu ta rungume sa ta baya, wanda hakan yayi daidai da fitowar ta daga dakinta tana murzan fuska, idanunta karaf a kansu."

      "Cikin bugun zuciya, taqara gyara tsayuwar ta gameda zuba musu idanu tana kallon su, tamkar yau ta soma ganin su, cikin ranta take faďin, wannan wani irin mutane ne, wanda duk wata hanyar da nabi dan inga sun samu tsabani a tsakanin su, abun faskara yake saikace aljanu..shiru tayi daga zancen da take, tare da kasa kunne dan jiyo abunda take faďa masa dukda tsakanin su da ita akwai ďan taku, ba lallai bane taji ba, saidai idan cikin ďagun murya suke maganar."

      "A hankali tana manne dashi cikin sanyin murya ta soma magana tace, haba mijina wannan wani irin hali kakeson jefa ni, tunjiya nakasa gane kanka, pls dear ka yarda dani wlh bazan tabà cikin amanar kaba koda kuwa a mafarki ne, kane mijina me sona uban yara na, sonka da nake yarda dakai da nayi shi ya sanya ni zamtowa matar ka a yanzu, dan Allah karka bari sheďan ya sanya ka zargina a hanlin ba hakaba, pls mijina, tana qara tusa kanta jikin bayan sa take maganar a yayinda yasa hannunsa ya riqe nata tare da juyo da ita suna kallon juna......











*HaneeSat*✍🏻📚📚📚

RAYUWAR AURENA Where stories live. Discover now