🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀 *NA* *HAFSAT_M*✍🏻 *Page*

1.4K 68 1
                                    

🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀



         *NA*

*HAFSAT_M*✍🏻


*Page*
      
       *42*


Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃






"Kayataccan murmushi kwance bisa fuskan sa, yanaci gaba da kallon ta, ya saki hannunta daga riqon da yayi mata, tare da tallafo nata fuskan, cikin qasa da murya ya soma cewa."

      "Sam bana fushi dake Maman baby, waye yace miki zan tabà iyayin fushi dake, sam, ni mijinki bazanyi fishi dake ba, domin kina ķàrķàshin kulawa tane, ki daina tunanin haka kinji Maman baby."

      "Babu shakka batayi tsammanin jin haka daga bakinsa ba matuka, a zaton ta zai ciga da canza mata, ya nuna rashin yardan sa da ita,  shiyasa take ta sake saken ta yanda zata karbì kanta idan ya tunkare ta zancen." saukar da idanunta tayi daga kan nashi kafin ta buďi baki a hankali tamkar me shagwabà tace."

     "Tunjiya rabona dakai mijina, ka shareni akan abu qalilan, kabarni na wayi gari da fargaba cikin zuciya ta, sam jikina banji daďin sa ba kaurace min da kayi sai yanzu da naga ka saurareni na samu sassauci cikin raina."

    "Amman dai yanzu kin samu nutsuwar ko Maman baby,?" ya tambaye ta yana qara tallafan fuskan ta, tace Eh Amman ai da yanzu ban tsayar dakai nayi maka magana ba da tafiyar ka zakayi ka barni cikin tunani...shiiii yace da ita bayan ya ďaura yatsan sa ďaya akan labèn bakinta, yace."

      "Ya isa haka wannan korafin komai ya wuce ai, dama gwada ki nayi ingani ko har in fita zaki bini kiyi min magana ko barina zakiyi in tafi cikin fushi,  sai gashi naga ashe matar tawa ta damu dani bazata iya bari na cikin fishi har na tsawon lokaci ba." yana murmushi yake mata maganar, cikin sigar wasa takai masa duka kan ķirjin sa, ta qara faďin."

     "To kaji ďaďi ai tunda yanzu ka gane gaskiya ni ďin meson farin cikin kane a koda yaushe."

     "Nasani kuwa Maman baby kuma na qara tabbatawa a yanzu ke ďin daban ce." yana maganar yakai duban sa kan gogon dake maqale a hannunsa yaqara cewa,  yanzu dai barni in tafi kar rana tayi sosai kinga har shaďaya ake nema, gwara in hanzarta ko,?"

     "Hakane a dawo lfy baban baby." fuska ya canza jin irin sunan da ta qira sa dashi, cikin zolaya yace, wannan sunan fa daga ina yazo,?"

      "Ramawa nayi tafaďa tana dariya, ya qara cewa, to canza min shi banaso."

     "To me kakeso in qira ka dashi bayan ka kusa zama uaban yara."

     "Yauwa anzo wajan, yace da ita yana yaqa dubanta, tace kamar ya anzo wajan me kaji,?'

      "Abban yara zakina qira na nest time kinji,?"

    "Haba dai kai kuwa Amman gaskiya ka zuzuta dayawa, kaida ko ďaya baka samu ba a halin yanzu kana ambaton dayawa." wayace miki,?" ya tambaye ta yana riqo hannunta cikin nashi ya qara cewa, nidai shi nakeso dan haka dole ayi abunda nakeso."

     "To ba matsala yanzu dai a tafi sai an dawo, tafaďa tana murmushi bayan ta cire hannunta daga riqon da yayi mata kafin ya juya ta qara cewa, pls idan badamuwa inaso in koma makaranta kaga tuni an daďe da komawa ni kuma har yanzu shiru ban koma ba."

     "Dubanta yayi da kyau cikin ido kafin yace zaki koma Amman ba yanzu ba sai bayan kin haufu, wanda wannan furicin da taji ya fito daga bakinsa ya sanya ta gwale idanu waje tamkar zasu faďo qasa, gameda dafe kirji, cikin rawan murya, zatayi magana ya dakatar da ita, yace bari sai na dawo zamuyi maganar yanzu rana tanayi."shiru tayi babu yanda ta iya haka ta rabu dashi badan ranta yaso ba, ya kai mata kiss a goshin ta gameda shafan cikin ta, kafin yayi mata bye bye ya juya ya fice haraban gidan." tana kallon sa jikinta babu kwari har ya shige motar sa me gadi ya buďe masa get ya fice."

RAYUWAR AURENA Hikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin