21

1.6K 139 2
                                    

Tun da ya iso sudan bashida wani kwanciyar
hankali kwata kwata xuciyarsa batada
sukuni.....yaja dogon tsaki bayan ya gyara
kwanciyarsa
maryam bata masa adalciba kuma bata kyautawa
rayuwarsaba
ta dora masa wani nauyi mai wuyar saukewa
wato alqawari,
taya xai auri maccen da bayaso maccen da ita
yake gani tayi sanadiyar.mutuwar matarsa
saboda ansa mata matacciyar xuciyarta ita kuma
gashi tana rayuwa da xuciyar matarsa har
maryam k tsammanin ya aureta....
wannan shine alqawari bayan rai wanda bayajin
xai iya cika burin maryam indai akan banxar
wannan likitar ne
yaja bargo yaqara shigewa cikinsa ya rumtse
idanunsa yana hawaye
yasan ya rasa maryam har abada maryam tasosa
da xuciya daya tabashi kulawa fiyeda wadda yake
bata ta sadaukar da rayuwarta saboda shi kuma
kafin ta mutu tabashi yaron da yake mutuwarso
kodan wannan yakamata ya cika burin maryam
ya sakamata da alherin data masa
ya sake girgixa kansa
nooooooo....baxai yiwu ba baxai iya xama da
matar da ya tsana fiye da komai a rayuwarsa ba
domin ita tayi sanadiyar gushe masa farin
cikinsa..
ya soma hawaye ba kakkautawa dai da lokacin
da aka bude qofar dakin
duk da bai duba mai shigowaba yasan ummansa
ce
Marhoom!!! ta kira sunansa cikin kakkausar
murya
da kyar ya iya dago idanunsa da suka rine sukayi
jajir saboda kuka ya xuba mata
how comes? da girmanka da mulkinka kaxauna
kana kuka, mecece damuwar ka bayan ta xauna a
saman gadon
tasowa yayi ya fada jikinta ya qanqameta
yace momy maryam bata kyautamin ba

me maryam tayi?
yayi shiru yana kuka
tace ni iya sanina maryam bata cutarda kaiba
illah ita data cutarda kanta saboda kai
ta boye damuwarta da ciwonta duk dan kada
hankalinka ya tashi
tayima son da batawa ko iyayen tasu kagayamin
dame maryam ta cutar dakai
yayi shiru kawai
tace in tambayeka ma
wacece dr.fulani
dam gabansa ya fadi a tsorace yake kallonta
lokaci daya tsoro ya shige sa
tace kayi shiru ka xubamin ido kagayamin me
kasani game da ita
yace bansan komai ba momy
ta tsura masa ido kafin tace maryam bata
gayama komai akanta ba
bugun gabansa ya tsanata
yace tagayamin xuciyarta aka samata
tace bayan wannan fa?
ya soma inda inda yana sosa kansa
inaji shikenan mgnr da mukayi da ita
taja gauron numfashi tana kallonsa
kafin rasuwar maryam mun taba mgnr cewa tana
son ka auri fulani, na tambayeta dalilinta akan
haka
tace fulani na daya daga cikin mutane masu
muhimmanci a rayuwarta, akwai sirrin dake
tsakaninta da fulani wanda ba wanda yasani koni
bata gayawa ba, tace fulani tayi mata taimakon
da takasa biyanta da komai sai da xuciyarta
saboda rayuwarta batada kamarta acewarta
ta nemeni da inboye wannan mgnr sai bayan
mutuwarta kuma ina mamata alfarmar ka auri
fulani kaso fulani ka kuma kula da rayuwar fulani
da xuciyarta dake jikinta
kwata kwata jikinsa a mace yake xuciyarsa sai
xafi take
yace momy wane sirrine tsakaninsu kuma duka
duka yaushe suka hadu harsukayi wannan
shaquwar
momy ta yatsina fuskarta
tace batagayamin komai akan tmbyrka ba abinda
nagayama shi naji daga maryam
yace tor momy meyasa kika yarda kika
daukarmata alqawarin xn auri fulani bayan
bansanta ba
tace saboda ina son maryam kuma tana yarona
marhoom, maryam mai kirkice banajin xata
cutarda rayuwaka da wata shiyasa na yarda da
ita na amince da alqawarinta akan xaka auri
fulani
nan da nan ya qara tsuke fuskarsa
yace bana sonta momy gsky baxan auretaba
baxan iya xama da nakassashiyaba wadda
akayiwa.musayar xuciya daga matacciya ba
tayi shiru tana kallonsa cike da.mamaki kafin
tace ba neman yardarka naxoba umarni nake
baka akan kacika burin masoyiyarka
ya tashi daga inda yake xaune
yace ni kuma so ake na cuci tawa rayuwar
saboda alqawari bayan rai, dan inason maryam
bashi xaisa na so wata macce ba
itama ta tashi tana kallonsa
tace inaji kaji abinda nace umarni nabaka ba
neman yardarkaba
maryam nada muhimmanci a rayuwata ba abinda
xata nema na kasa mata saboda son da ta
nunama da kuma kyautatawarta akaina shiyasa
baxan iya take buqatartaba baxan sami sukuniba
har sainaga kacika alqawarinta
kafin yayi mgn ta juya ta fice shima ransa a bace
yabar dakin.

LABARI NAWhere stories live. Discover now