23

1.4K 124 0
                                    

A sanyaye taja motar ta fice daga wurin , batayi
wata tfy mai nisa ba lokacin data iso gida
tana qoqarin hawa step abbanta ya kirata
Fulani!
ta juyo tana kallonsa batare data amsa ba
idanunta cike da kwallah
yace ina kikaje haka tun daxu
kai tsaye ta amsa da
naje neman Marhoom ne ina sonsa abba
yayi tsaye yana kallonta kasaqe
yace fulani baxaki manta wannan mutum ba baki
taba ganinsaba bakisan inda xaki gansaba
kitunafa bake kesonsaba xuciyar maryam ce
ta dan yi murmushi kafin
tace abba kaine k ganin bantaba ganinsaba
amma xuciyata tasanshi tasan komai akansa
tasan lokacinda yake shigowa nigeria da
lokacinda yake barinta
nasan irin abincin da yakeso da wanda
bayaso,ayanxu kuma bashida wani buri da ya
wuce haihuwa, tay xakace bansanshi ba abba
bayan nasan komai daya shafi rayuwarsa
abba ya boye mamakinsa bayan ya hadiye yawu
da kyar
bakomai Allah ya kyauta idan kindawo hayyacinki
duk xaki manta da wannan ya juya ya fice
ta bishi da kallo har ya bace kafin ta juya ta hau
stairs ta nufi dakinta...
washe gari da wuri ta shirya kanta cikin doguwar
riga baqa oman dankwalinta ta dora akanta kana
ta fito tashiga motarta tabar gidan
duk inda xuciyarta ta rayama bi nan take bi harta
iso gidan da xuciyarta k axalxalarta taxo taga
iyayenta bayan wadanda ta baro a gida
ga mamakinta gate din gidan qarqame yake da
qaton kwado ko ina sukaje nan take xuciyarta na
raya mata suna jidda wata qila ciwon maman
maryam ne yatashi sukaje
taja dogon tsaki ta shiga motarta ta koma gida

LABARI NAWhere stories live. Discover now