Page 22

1.9K 145 31
                                    

'☆´-'☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾'☆•
❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*🙆🏻‍♂*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠  
☆ *TANTIRANCI KO KARUWANCI*☆
*.¸¸.*♠ *.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*🙆🏼‍♀*.¸¸*❆
'☆´-'☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾'☆•🤱🏻
{Fad'i alkairi ko kayi shuru)🤫
      A true life story
*Follow me on Wattpad @rahamanalele*

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh'md Rufa'i Nalele..☆

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم
Page 22
*To yazanyi daku🙁 nayi muku 16 read more* Sannan amin haƙuri wani abu ne ya shige min gaba..

Kai bazata kirasa ba, abin daya dace shine tabi bayan su Uwani ta tsoratar da ita,
Aiko da gudu tayi d'akinta tad'auko gyalanta tabi bayansu, basuyi nisa ba, dan haka nan ta tsaidasu tana me gaya musu dan Allah zatayi magana da Uwanin na minti d'aya.. d'aya daga Cikin folisawan yace mata hakan bazai yuhuba, Dan ya sab'ama doka, tayi dai hakuri sukai ofishinsu.
Nan tahau basu hak'uri, sukace toh takira ABDUL tukunna, tace dan Allah dai suyi hak'uri.
Haka badan sunso ba suka bata Uwanin.
Bayan sun d'an matsa gefe ZAINAB d'in cemata tayi.. "Wallahi Uwani idan kikace nice nace kibama RAHMA magani saina qaryataki, na kuma ce a kulleki a gidan yari har zuwa qarshen rayuwarki  dan baqaramin qazafi kika min bah, duka zaki dinga ci ba dare ba ranah ga aiyukan gidan yarin masu matuqar wahala, dan haka sai kisan me zakice musu, kindai san nan ba qauye bane, duk abinda nagaya muku zartar da hukunci zasuyi akanki, Dan haka kikiyaye idan har kina so nasa ABDUL yace susakeki..
Hawaye ya zuboma Uwani, cikin matuƙar tsoro tace, "zan kiyaye, indai zakisa a sakeni..
Zainab najin hakan tanufi  folisawan dace musu tagode, sannan sukayi gaba da Uwanin, ita kuma ta juyo gidan nasu hankalinta ad'an kwance..

Dame gadin nasu taci karo zai gudu hannunsa d'auke da kayansa, tace, "Aha, kai kuma miye haka, ina zaka da kaya kamar wani dillali.
Yace "guduwa zanyi, ganin y'an sanda sun tafi da  Uwani, kar suzo nima su tafi dani..
ZAINAB tayi dariya tace, "Da Allah kakoma ciki, ashe inaganinka kamar wani wayayye ashe abin ba haka yake ba, Uwani ko kwana bazatayi a wajensu ba! zansa ABDUL yace su saketa, yanzu idan katafi me hakan yake nufi.
D'an uwan Lantana yaja numfashi yace, "toh bara na koma, aina d'auka zasuzo su tafi dani ne.
ZAINAB ta wuccesa tana cewa, "aa, ka kwantar da hankalinka..

ABDUL da RAHMA ko gasu a asibiti..
Doctor yace RAHMAN ta samu suman ne sakamakwan jin wani abu daya furgitata da yawa, ABDUL yace mai haka ne,
Doctorn yace.. "idan hakan taqara faruwa da ita gaskiya zuciyarta zata karb'a hakan kuma zaisa zuciyar takamu da ciwo nan take
Dan haka ABDUL ka kiyaye idan har kana san ganinta da lafiya, ayanzu dai zata iya farfad'owa akowane lokaci, amma dan Allah kasan maganganun da zaka gaya mata kwawawa dan susa hankalinta kwanciya.
Sannan mun duba maka mahaifar tata, anyi mata hoto zuwa anjima idan sakamako ya fitto zamu gaya maka komai.
ABDUL yace,  " Nagode sosai doctor, Allah ya kaimu fitowar sakamakwan lafiya..

"Ameen.. doctorn yace  da barin d'akin yana me sha'awarsa da matan nasa, d'azu ya kawo ZAINAB yanzu kuma ya kawo RAHMA, duk matan nasa kwawawa dasu, kuma duk sun dace dashi..

ABDUL d'in ko zama yayi ya zubama RAHMA ido burinsa kawai yaga tatashi...
Wayarsa tayi qara yana dubawa yaga AMEER ne, nan ya d'auka da gaya masa yana asibiti ne tare da RAHMA.
AMEER yace masa meya faru, waye ba lafiya,
ABDUL ya gaya mai komai daya faru.
AMEER ya rintse idansa yace shi baiyarda da maganar Uwani ba, gwara da folisawan suka tafi da ita acan ta gaya musu gaskiya, Allah yabama RAHMAN lafiya, dama abin dayasa yanzu ya kirasa wasu takaddu ne Dady ya turo su yanzu yana buqatar saka hannunsa, dan za'a fitarma da wani kayansa ne wanda company ta had'amai.
ABDUL yace. "saidai kakawo min takaddun nan na saka hannun, Dan bazan iya tafiya na barta ita kad'ai ba, sannan Bana san ka gayama su Dadyn komai
AMEER yace "Toh, ba damuwa gani nan zuwa..

HALIN WASU MUTANAN Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz