26-30

848 57 5
                                    

🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘

*RUHIN 'DANA*

🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘🌸☘

              RUBUTAWA
              *AYSHA ISA*
          (Mummy's friend)

_*Vote me on wattpad @ AyshaIsah.*_

_*Littafan marubuciya*_

_1. Na tsani maza_

_2. Meke faruwa?_

_3. Illar rik'o ('yar rik'o )_

SADAUKARWA GA:

*AUNTY HAUWA*
_(Ummu walid)_

            &

*RAHEENAT M. ABBAKAR*
_(fake yaya😜)_

*🇸🇦ZAMAN AMANA WRITERS*
(g̲̅i̲̅d̲̅a̲̅n̲̅ z̲̅a̲̅m̲̅a̲̅n̲̅ l̲̅a̲̅f̲̅i̲̅y̲̅a̲̅ d̲̅a̲̅ a̲̅m̲̅a̲̅n̲̅a̅,  i̲̅n̲̅s̲̅h̲̅a̲̅ A̸l̸l̸a̸h 🤜🤛). ̸ ̲

_It hurt to see those you give so much worth does not take you as take them to be. Anyway that life for you never you do things because someone rather do it for Allah sake._

_A secret been told to a single person is not longer a secret, never you share your secret with someone who cannot share his with you in returns._

_Ya Allah grant my mummy shifaa, Ya Allah make live longer for us. 😭😭😭😭 Please need your prayer for my mum speedy recovery 🙏🙏🙏._

_Tawan na hakura ya na iya dake amma fa ki sani idan na tashi ramawa no complain😄😄😄_

*BIMISMILLAHIR-RAHMAIR-RAHIM*

_*Page 26-30*_

_K'asa barin wajen yayi don wani irin tsoro da yaji ya rufe shi, gabansa kuma sai dukan uku-uku yake "kadai ace baffa ya rasu ne" kuka ya fashe dashi tamkar karamin yaro tare da zaman dirshen a eurin,  haka ya cigaba da kuka yana dana sani har barci baro ya sace shi._

_Washegari da misalin karfe 8 Bukhari ya tashi,  a gurguje ya daura alwala yayi sallar sannan ya nufi asibiti. Ya isa direct wurin su Bappa ya nufa, yana ganinshi ya saki wani murmushi don jikin alhamdulillah da sauki don Bappa ya farka daga dogon suman dayi ko kuma idanuwan shi sun koma fari kamar yanda suke da_

_"Mall. bismillah ga wuri ka zauna" Jummai tace tana mikewa daga kujeran da take zaune_

_"Yi zaman ki nan ma ya isa" yace had'e da zama gefen gadon da Bappa ke kwance._

_Murmushi Jummai tayi sannan ta koma ta zauna,  ganin irin kallon da yake wa Bappa tace "mall. wannan kallon haka"_

_"Kedai bari na kalli abina wallahi jiya kusan k'asa barci nayi,  ina ta tunani wata k'il k'arshen ganin da Bappa kenan kinga dole na kalle shi ganin ya samu sauki ko?"_

_"Hmm haka ne kam,  don nima na aza rai zai yi halinsa sai gashi Allah cikin rahmansa ya bashi lafiya._

_"Alhamdulillah, Allah ya k'areshi da lafiya_

_"Ameen" inji Jummai.  Hira suka d'an yi kafin daga bisani Bukhari ya tashi yace "Jummai ni zan tafi nima, sai na dawo"._

_"A dawo lafiya,  Allah ya tsare ya kuma bada sa'a._

_"Ameen" yace sannan ya fice daga dakin._

_Wannan kenan_

_*Bayan Sati uku*_

_Kimanin wata d'aya kenan dasu Bappa ke kwance asibiti, kamar kullum Jummai ce zaune tana gogewa  Bappa miyau dake fama zilala daga bakin shi don tunda ya farfad'o haka suke fama da wannan miyau, Bappa yace cikin maganar daya koma tamkar yara masu koyon magana "mama yauce zamu koma jida?"yana magana yana kada kai tamkar dolo._

_"Bappa nima ban sani kai ka dinga rokon Allah ya baka lafiya kaji ko?"_

_Gyad'a mata kai yayi sannan ya kwanta nanda nan barci yayi aron gaba dashi._

_Tagumi Jummai tayi tana me addu'a Allah ya bashi lafiya._

_Dr. ne ya k'ariso gun su bayan ya gama duba sauran mara lafiyan dake dakin yace "madam ya jikin patient d'ina?"_

_"Toh gadai shi nan har yanzu sai a hankali._

_"Dame-dame  ke damun shi yanzu?"_

_"Har yanzu baya iya tafi daidai,  hannun ma baya iya sauke ta hagun har yanzu,  ka miyau shima bai daina zilalan masa ba."_

_"Hmmm! ki sameni a office" Dr. yace sannan yayi tafiyarsa._

_Bai jima da tafiya Jummai ta mike ta biyanshi,  da sallama ta shiga office din,  zaune yake yana duba wasu files, "gani nan Dr" jummai ta fad'a cikin girmawa. Nuni yayi mata da kujeran dake facing dinshi "zaune",  zama tayi tana sauraron abunda zai ce mata. Gyaran murya yayi sannan yace " madam nasan zaki mamakin abinda yasa nace ki biyoni office ko?"yadan shiri don jin amsar da zata bashi_

_Kai ta gyad'a alamar eh_

_Cigaba yayi yace "dama bakomai bane illa shawaran da zan baki,  a gaskiya munyi iya bakin kokarin mu ganin yaron ban ya samu sauki amma abin ya faskara kuma alamun sun nuna wannan ciwon bana asibiti bane don haka zanyi discharging d'inku kuje ku gwada na gida maybe a dace._

_Mikewa tayi jiki a sanyaye tace "nagode doctor" sannan ta koma gurin Bappa.  Da yamma da Bukhari yazo ta sanar dashi duk inda sukayi sa da Doctor, bai wani damu ba suka dauki Bappa suka dukufa niman magani,  haka suke ta fama amma shiru babu canji,  Jummai tabi ta lalace tayi wani irin muni abin duniya duk ya bi ya isheta. Daga baya ma hakuri sukayi suka barwa Allah komai._

_*Bayan kwana biyu*_

_Jummai ce zaune da Bappa a tsakar gida ta biye masa  sunata wasa abinsu din tun dawowarsu guda duk abokan was an sa babu mai don wasa dashi kuma,  wasu kuma iyayensu ne suka hana su wasa dashi a cewarsu kar yazo ya shafawa yarensu tunda shima ba haka aka haife sa ba._

_Bukhari kuwa hanya ta bude masa don yanzu shi ke dauka nayin komai na gidan._

_Yauma kamar kullum zaune take tana wasa da Bappa Bukhari ya shigo gidan da sallama,  mikewa  jummai  tayi ta anshi ledar dake hannunsa sannan tace " sannun da zuwa mai gida."_

_"Yawwa sannu " ya fada cike  da fara'a.Baffa ne ya nufoshi yana murmushi har ya kawo daf dashi, Bukhari ya daka mashi tsawa  wanda yasa nan take jikin Bappa bappa ya fara b'ari._

_Muje zuwa_

_*Mummy's friend ce🤩*_

RUHIN 'DANAWhere stories live. Discover now